Main menu

Pages

MAGANIN KARYEWAR GASHI, DA SASHI YAYI TSAWO, DA KUMA GYARAN KAFA DA RAGE QIBA DA TUMBI

 


           


    GYARAN GASHI 


Muddin uwargida na kokarin gyaran gashi lokaci lokaci, za ta kiyaye gashin nata daga karairayewa, zai rika laushi kuma ya kara tsawo. Domin cimma wannan, za ki tanadi ganyen magarya, ki rika wanke kan da shi, yana kara karfafa gashi ya kuma hana shi zubewa. Ga wadansu daga cikin sinadaran da za ki tanada:1. Man zogale.

2. Man kwakwa.

3. Man zaitun.

Sai ki hade su guri guda ki rika shafawa a kanki a matsayin man kitson ki, ko kuma ki tanadi:

1. Danyen kwai 

2. Sabulun salo

3. Garin shammar

A fasa kwai, amma banda kwaiduwar farin kadai zaki yi amfani da shi, sai ki zuba sabulun salo a ciki, ki matse ki zuba garin shammar ciki sai ki wanke kai da shi. Allah ya taimake mu.Ga wani hadin kuma dai duk na gyaran gashi wannan hadin na masu karamin karfi ne domin abubuwan daza ki tanada ba za su fi karfin ki ba da farko za ki tanadi ruwan Tumatur ne da sabulun salo kawai za ki matse ruwan tumatir din sai ki zuba sabulun salon aciki ki barshi ya samu tsayin minti talatin idan ya jika, sai ki shafa a kanki da dadare.Idan zaki kwanta bacci, da safe sai ki sanya ruwan dumi ki wanke tas. Insha Allah za ki ga gashinki yayi kyau sosai.

Wannan kuma man gashi ne mai sa laushin gashi da tsawo ya yi baki yana shekin haske. Wannan hadin ba zai taba barin gashin ki ya karairaye ba kuma zai rika laushi sosai. Da farko zaki tanadi:

1. Zaitun shitta

2. Man alayyadi

3. Man zaitun

4. Man kwakwa

5. Man albasa

6. Man hulba

7. Man ridi

Za ku hada hulba da lalle gu daya sai ku tafasa, saiku tace ku wanke kai da shi, sannan ku hade dukan wannan mayuka da na lissafo ku rinka shafawa akan ku zaku ga gashin ku yana kara kyau.

             Gyaran Tafin Kafa

‘Yan’uwana mata yanzu zan yi bayyani ne a kan yanda za mu kula da tafin kafanmu, ba ku ba zuwa wajen wanke kafa, kawai za ku yi amfani da wannan hadin kuma za ku ga abin mamaki. Ga ababen da za ku tanada:

1. Man shanu

2. Man kwakwa

3. Man ridi

4. Man alayyadiZaku hade wanan mayukan gu daya, idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi, da daddare idan za ki kwanta bacci sai ku shafa wannan mayukan a tafin kafarku sai ku sami leda ku daure kafar da shi ku kuma saka safa (socks) da safe ku wanke kafar da ruwan dumi ku shafa man zaitun da man ridi. Ko kuma ku nemi:

1. Man kwakwa

2. Man shanu

3. Man zaitunSai ku hade su gudaya suma kuringa shafawa da dare kuma saka leda kuna daure kafar sannan kusa safa (socks) idan gari ya waye ki fara gasa kafar kadan sannan ki wanke da ruwan dumi, ki shafa masa man zaitun.

Wannan hadin wanke kafa ne sai a tanadi:

1. Kokumba

2. Lalle

3. Man ridi

Sai ku tanadi ‘Cucumber’ ku fere bayan ku yanyanka shi kanana, a markada, amma fa kar a cika masa ruwa domin an fi son ainihin ruwan ‘Cucumber’ din sai a kwaba lallen da ruwan cucumber din, a rika amfani da shi da dare, ana cirewa a wanke da safe,

ku kuma wanke kafar da ruwan dumi sai a shafawa kafar man ridi insha Allah, indai aka rike wannan hade-haden, za a ga amfaninsa, kuma za a yi mamakin irin kyan da tafin kafar ku zai yi. Allah Ya taimakemu.
      Rage kiba da tumbi

Mata da dama ba su son kiba da tumbi, wannan kuma ba komai yake jawo shi ba sai haihuwa da wadansu matsalolin. Galibi, maza ba su cika son masu kiba ko tumbi ba. Amma akwai hanyoyin gyarawa. ‘Yan’uwa, za a iya gwada wannan hadin domin biyan bukata:

1. Garin hulba

2. Ganyen na’a-na’a

3. Garin kanamfari

4. Zuma

5. Lemon tsami

6. Farin kwalli

7. Man na’a-na’a

Za a hade wadannan ganyen guri guda, a sa mi farin kwalli dunkullale, za a saka a ciki, idan ya kai kamar minti biyar sai a cire sannan a saka zuma a cikin ruwan sai ku rika sha, shi kuma man na’a-na’a, za a rika shafawa a tumbi ne zai ragu insha Allahu.
Idan kuma ana son rage kibar ne gaba daya sai a sa lemon tsami a ruwan a rika sha. Nan ma wani hadin ne na rage kiba za ku tanadi:

1. Habbatus-sauda

2. Sukari

3. Ganyen shayi dan aune

4. Zuma

Wannan hadin zaki hade su guri guda ku tafasa su ki zuba zuma a ciki sai ku rinka sha

Comments