Main menu

Pages

WANNAN SHINE DALILIN DA YASA SUKE HASSADA GA MINISTA PANTAMI
 DALILAN DA YASA SUKE HASSADA DA MINISTA PANTAMI KENAN
√ Shine Dan Afrika na farko da ya taba zama shugaban tsangayar koyon rubutun musulunci a Jami'ar Madina a shekarar 2014.√ A cikin kasa ga shekaru uku ya nuna irin bajintar sa inda ya samu kyaututtukan girmamawa guda dari da goma (110) a ciki da wajen Nijeriya.√ Haka kuma ya samu kyautar mutum mai kwazon daukaka ko samar da cigaban harkar sadarwa ta zamani wato ICT Promoter a turance a shekarar 2017 a Birnin London.Sunan wannan bawan Allah shine: Sheikh Dakta Isah Ali ibrahim Pantami


Ya samu Digiri da shaidar karatu kamar haka: > Digirin farko wato Bsc akan hakar Na'ura mai kwakwalwa (Bsc Computer) a Jami'ar ATBU dake garin Bauchi > Yayi Digiri na biyu wato Msc a turance a fannin ilimin Na'ura mai Kwakwalwa a Jami'ar ta ATBU (Msc Computer)> Ya samu takardar shaidar MBA Technology a Jami'ar ATBU dake Bauchi> Ya samu Digirin Digirgir wato Ph'D Oil and Gas Computing a kasar England> Ya samu Digiri a fannin samar da sauye-sauye a fannin yanar gizo wato Digital Transformation a Jami'ar Harvard > Ya samu shaidar strategic innovation a MIT, dake kasar Amurka (USA) > Ya samu takardar shaidar Management a Jami'ar Cambridge, dake USA


> Ya koyar a Jami'ar ATBU dake Bauchi


> Ya zama babban Darakta na hukumar NITDA a Nijeriya> Ya zama Ministan sadarwa da kuma tsare-tsaren tattalin arziki na zamani wato Communication and Digital Economy a Turance> Babban mahaddacin Qur'ani ne 


> Babban mai wa'azi da fassarar alkur'ani ne


Muna Addu'ar Allah ya yi maka jagora akan makiyanka na fili dana boye Malam

Comments