Main menu

Pages

GARABASA BIYAR GA DUK WANI MUSULMI

 






GARABASA GUDA BIYAR GA DUK WANI MUMINI


1. Ko kasan cewa yayin idar da kiran Sallah karka haramtawa kanka Addu'ah, domin Addu'ah a wannan lokaci ba'a juyata.




2. Ko kasan ina ake sanya zunuban ka yayin da kake sallah?

Manzon Allah (saw) ya ce:- "Duk lokacin da bawa ya ke Sallah ana sanya dukkan zunuban sa a wuyansa da kafadun sa, duk lokacin da ya yi ruku'u ko sujada zunuban sa za su dinga fadowa kamar yadda ganye yake fadowa daga bishiya ." 




Yakai wanda kake gaggawa yayin ruku'u ko sujada, ka tsawaita sujada da ruku'u domin zunuban ka su ragu kada ka bari wannan garabasa ta wuce ka.




3. Ko kasan wata salihar mace ta

rasu, duk lokacin da 'yan uwanta suka ziyarci kabarin ta sai suji kamshi yana tashi, sai suka tambayi mijinta sai ya ce ta kasance tana karanta Suratul Mulk kowane dare kafin tayi bacci.




4. Ko kasan karanta Ayatul Kursiyyu bayan kowace sallah zaka wayi gari tsakanin ka da Aljannah mutuwace kadai?




5. Ko kasan idan ka idar da sallah kar kayi gaggawar tashi, domin mala'iku suna roka maka gafara.


👆Ya Allah ka sanya wannan tunatarwa ta zama SADAKATUL JARIYA a gareni da Iyayena da duk wanda ya taimaka wajan yadawa,


Amin.




Comments