Main menu

Pages

KASAITACCIYAR MACE ITA KE KULA DA NI'IMARTA

 DON SAMUN INGANTACCEN NI'IMA A JIKIN KI


1. kunun zaqin dabino; Zaki sami dabino mai kyau ki cire kwallayen ki tsabtace shi, sai ki jiqa har saiyayi taushi sossai saiki markada a blander, ki saka zuma ko shuga kadan da madarar ruwa, asa yayi sanyi sai ki sha.2. Yawan cin kwadon zogale da tumatir tare da dafaffen kwai.


3. Yawan cin dabinon da bai bushe ba tare da shan ruwa yana taimakawa sossai.


4. Ganyen idon zakara a daka shi ana hadawa da man tafarnuwa kadan da nono ko yogurt.


5. Yawan shan Lipton wanda yaji kanunfari, citta da na'ana'a (wannan bake ba har mai gida) yana kawo dumin jiki wa mace kuma ya kara ni'ima.


6.  ki samu 'yayan zogale bushesshe ki daka da dabino da cikwi ki dinga sha da nono zakiyi mamaki sossai.


7. Ki dake ayar ki tare da dabino, kanunfari kina sha da nono hmmn.....


8. Ki samu alkamanki a niqo miki ita ki soya sama sama haryayi ja idan ki ka kusan gama period naki sai ki dama kaman salala da nono kisha sau uku (domin jinin na tafia da abubuwa dayawa).


9. Cucumber ki fere ki yanka tumatir dayawa albasa kadan dafaffen kwai da garin kuli zai baki ni'ima sossai sossai mussaman kici daf magrib.


10. Zuma da garin habbatussauda mai kyau da man zaitun za ki sha table spoon biyu safe biyu yamma for 2wks.


11. Madarar ruwa gwangwani daya da kwai ki buga har sai ya daina kumfa asa zuma kadan hmmmn.....ga sauqi amma sai kawo ni'ima. 


Allah Ya sa mun amfana.Comments