Main menu

Pages

 GRILLED FISH (GASHESSHEN KIFI)


Kayan aiki

Kifi tilapia

Kayan miya

Dandano

Garin citta

Black pepper

Tafarnuwa,albasa

Mai

Dark soy sauce


Matakai

Na gyara kifina na tsaneshi na gyara kayan Miya da albasa nayi greatin dinshi nasamu mazubi nazuba nakawo citta,  tafarnuwa, dandano, mai da soy sauce nazuba acikin kayan miyan na juya suka hade Sai nadauko abin gashi na shafe kifina dashi na jera a abin gashi nasa wutar sana da kasa nasa 40min yadanganta da zafin oven dinkiInya gasu zakiji Yana kamshi na musamman nayi decorating da lattus da tumatur Kuma yayi dadi sosai
  KOSAN KIFI


KAYAN HADI

Kwai

Kifi

Albasa

Attaruhu

Fulawa

Maggi

Gishiri

Man gyada

 

YADDA ZAKIYI

Ki samu kifi (ice fish) ki wanke sai ki zuba a tukunya ki sa maggi da gishiri da albasa ki dora akan wuta,idan ya dahu sai ki sauke ki cire kayar sai ki zuba kifin da attaruhu da kuma albasa a turmi ki daka su, saiki juye a roba ki fasa kwai a ciki, ki zuba fulawa (hikimar sa fulawa dan ya hade ne) sai ki zuba gishiri da maggi ki juya, sannan ki dinga mulmulawa kina sakawa a cikin mai gyada mai zafi kina soyawa idan yayi brown sai ki kwashe.


Comments