Main menu

Pages

HUKUNCIN SHAN RUBUTU A MUSULUNCE

  




            HUKUNCIN SHAN RUBUTU


      Ba'a samu hakan daga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, haka nan sahabbansa, saidai an rawaito halaccin hakan daga wasu daga cikin sahabbai kamar Ibnu Abbas, ya zo a Zadul-ma'ad "Ibn




 Abbas ya yi umarni a rubutawa wata mace mai tsananin nakuda wasu ayoyi na Alqur'ani, don ta samu sauki" haka kuma an rawaito halaccin hakan daga wasu tabi'ai kamar Mujahid, wannan kuma shi ne maganar Imamu Ahmad.




Don haka mutum ya karanta ayoyin shi ne ya fi, domin shi ne ya tabbata a ingantattun hadisai, saidai wanda ya rubuta ya sha ba za'a aibanta shi ba, tun da yana da magabata.




Allah ne mafi sani.


Don neman Karin bayani duba: Zadul ma'ad 4\170 da Majmu'ul Fataawa 19/64

Comments