Main menu

Pages

  


  KASAITACCIYAR MACE, ITA CE MAI GYARA KANTA


TURAREN TSUGUNO

wannan hadine me kyau wanda zai gyara miki jikinki yadinga kamshi batare da ya cutar dake ba dan akwai matan da suke fesa turare a pant dinsu kai wasuma har a gaban nasu suke sawa ko a wanke da sabulu a tunaninsu  zai yi kamshi masuyin haka ba karamin cutar da kansu suke ba. Saboda chemical din dake dauke da sabulu wannan wajan baya bukatarsa a garin neman kamshi kijawowa kanki matsalan da zata ja miki infection me wuyar magani, idan kinaso yadinga kamshi ga abinda zaki wanda ze kamsasashin sosai ba tare da kin cutu ba.


1 itacen duraf

2 garin ambulans

3 ambasal

4 hawi

5 Miski

6 turaren miski

7 turaren sandal

8 gallo


Da farko ki sami garin ambur da ambasal da dakakken gallonki da dakakken miski ki zuba akan itacen turaren durof ki juya sosai ki zuba hawi da turaren miski dana sandal dana ambur  ki jikasu suyi kwana bakwai yadda zasujiku sosai bayan sunyi kwanakin seki dakko ki kara madarorin turaren ki juya sosai shikenan sai ki dinga turaren akan kujerar katako me huda to kefa shikenan kin zama sarauniya indai kina wannan hadin ina tabbatar miki ko kina period bazaki rabu da kamshi ba.


  

Comments