Main menu

Pages

  🌿YADDA AKE HADA MIYAN ZOGALE 🌿


INGREDIENTS

- Tattasai

- Tumatur

- Albasa🧅

- Attaruhu

- Zogale🌿

- Gyada

- Nama

- Ganda

- Kifi

- Tafarnuwa

- Gyadan qamshi

- Manja

- Maggi

- Curry

        

           PROCEDURES

Da farko uwargida zata gyara kayan miyanta sai tayi blending dinsu, saita juye a mazubi Mai tsafta, sannan sai uwargida ta gyara zogalenta,t a wankeshi ta tsaneshi a colender, uwargida zata gyara gyadarta tasoyata sama-sama, saita murje bawon dake jikin gyadar, sai uwargida ta daka yar citta da gyadar qamshi,saita zuba wannan gyadar data gyara,siaki daka dakyau harsai kinga tayi laushi, saiki dauko tafarnuwanki ki bareta kizuba Akan wannan gyadar dakika daka, Uwargida zata cigaba da dakawa harsai kinga yafara alamun zau fitar da mai,saiki zuba mazubi mai safta,then uwargida Zaki dauko tukunyarki mai tsafta saita dorata akan wuta saiki wanke nama kizuba kibarshi yadahu, saiki zubawa busashen kifinki ruwan zafi bayannkin gyarashi,saiki wankeshi tas,dama already uwargida ta gyara da tsaftace gandarta,saki dafashi yadahu sosai, sai uwargida tasauke daga kan wuta,sannan uwargida zata dorawani tukunyan Akan wuta kizuba manja, kisoya, saiki zuba kayan miyanki,kisa yar kanwa aciki sabida gudun tsami,kibarshi yadahu sosai, saiki kawo gandanki ki zuba kibarshi yadahu sosai saiki kawo kifinki dackika jiqa ki zuba,sannan nama shine na qarshe,saiki juya dakyau harsai kinga komai yahade jikinshi, saiki kawo wannan gyadar dakika daka, ki kwabata da ruwa,saiki zuba akan wannan kayan miyan naki nakan wuta,itama kijuyata ta juyu,sabida gudun kada yayi miki kamu,sannan saiki barshi yadahu for some minutes, then saiki saka Maggi da curry,ki juya dakyau, kibarshi yasamu at least 4 to 5 minutes, then saiki dauko wannan zogalen da kika wanke tun da farko,saiki zuba,kijuya ko'ina da Ina,then kirufe tukunyan kibarshi yadahu sosai,saiki saukeShikenan uwargida miyan zogalenki is ready

       Serve hot🥣

NOTE:-zaki iya yin miyan kizuba daddawa,Amma bada yawaba, Musamman idan na busashen Zogale 🌿 zakiyi,yana dadi sosai

Comments