Main menu

Pages

MAGANIN CIWON HANTA SADIDAN, DA MAGANIN MANTUWA.

 MAGANIN CIWON HANTA.


Ciwon hanta ya zama ruwan dare Inda yake kara yaduwa a tsakanin Al'ummah.


Ga wata fa'ida wanda masu fama da wannan ciwon zasu iya jarrabawa domin samun waraka daga lalurar cikin nufin Allah.


Hanya Ta Farko 1

1.Ganyen Zugale busashshe

2. Yayan Baure ko garin yayan busashshe.Yadda Za a Hada 

Sai a hade waje guda a dake su suyi laushi, mai fama da Matsalar ya rika shan karamin chokali a nono ko kuma madara ta ruwa ko kunu sau 2 a rana.Hanya Ta Biyu 2 

MAGANIN HEPATITIS A,  B & C (CIWON HANTA)


  ALAMUN CIWON HANTA

Akwai matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da typhoid akai-akai.


・ Haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki mai tsanani.


・  Yawan haraswa dakuma tashin zuciya koda ruwa kasha.


・  Ido yakanyi yellow, da rashin dandano a baki, fitsari ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi, bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa.


MAGANINTA

1. A samu garin habba cokali 10

2. Garin Sidir cokali 5

3. Garin tin cokali 5

4. Garin bawon kankana cokali 10

5. Garin Citta cokali 1

6. Garin tafarnuwa cokali 1

7. Garin Hidal cokali 5

8. Garin zogale cokali 3

9. Garin Yansun da raihan da kusdul hindi cokali 6


Sai a hadasu waje daya a samu Zuma lita biyu mai kyau sai a zuba ciki a juya ya hadu sosai sai a dinga shan cokali uku sau uku a rana.MAGANIN YAWAN MANTUWA,.DA KAIFIN KWAKWALWA.


  Domin magance yawan mantuwa,da kuma karawa kwakwalwa karfi,ga wata fa'ida sai a jarraba kuma insha Allah za a samu nasara.1. Garin ik'lil jabal (rosemary)

2. Na'a Na'a (mint leaves)

3. Girfa (cinnamon)


YADDA ZAA HADA

Za a samu kowanne magani da muka ambata garinsa, kmar chokali 5 kowanne sai a hade su waje guda a rika diban chokali 1 a tafasa kamar shayi da ruwa kofi 2 asha kofi daya safe daya yamma, za a iya sa Zuma ko sukari idan za a sha.


Dukkan wanda ya jarraba wannan fa'ida zaiga banbanci insha Allah.Comments