Main menu

Pages

HANYOYIN KARA LAFIYA DA GINA JIKI

 



HANYOYIN KARA LAFIYA DA GINA JIKI:


Lafiyar jiki abu ne da kowa ke bukata domin kuwa masana kiwon lafiya sun yi kididdiga akan cewa, da yawa daga cikin cututtukan dake kama jikin dan Adam su na bayuwa ne dangane da irin cimarsa.



Idan mutum ya kauracewa da yawa daga cikin nau'ukan abinci da ake sarrafasu a kamfanunnka, kama daga kifin gongoni zuwa lemuka na gongoni, to tabbas zai tsarkeke lafiyar jikinsa daga sunadaran calories.



Wannan sinadaran na calories su na da tasiri kwarai da gaske wajen karya garkuwar jikin dan Adam, domin kuwa su na jefa sassa daban-daban na jikin dan Adam cikin hadarin kamuwa da cututtuka.


Ga jerin hanyoyi 6 da za su kara habaka lafiya da gina jikin dan Adam



1. Yawaitar amfani da kayan hatsi irinsu; gero, dawa, acca, masara, uwa uba alkama, domin kuwa su na kara karfafa karfin jikin dan Adam da kuma bayar da kariyar cututtuka irinsu, ciwon zuciya, ciwon sukari da kuma ciwon daji.



2. Amfani da 'Ya'yan itatuwa da ganyayyaki:


3. Rage amfani da gishiri da kuma sarrafaffen sukari.



4. Ana bukatar mutum ya yawaita shan ruwa domin masana kiwon lafiya sun bayyana cewa ruwa ba ya taba yin yawa a jikin dan Adam saboda irin bukatuwar jiki ga ruwa.



5. Kauracewa barasa da sinadarin Caffeine, wannan sunadarin ana samun shi a cikin lemo na Coca Cola da kuma Naskofi



6. Rage amfani da nama da kwai na kajin gidan gona, domin kuwa sinadaran gina jikinsu ba daya yake da kajin hausa ba. Saboda haka ga mai bukatar sunadarin Protein a jikinsa, akwai irinsu gyada, gujjiya da kuma wake da suke kunshe da wannan sinadarai.


Comments