Main menu

Pages

KO KUNSAN CEWA ZUMUNTA FARILLANE BA RA'AYI BA ?
 ZUMUNCI BA RA'AYI BANE, WAJIBINE. SHIN KANA KO KINA  SADA ZUMUNTA ? GA HUJJOJI 20-GAME DA ZUMUNCI.


1-Allah taala yayi Umarni da sada zumunta.Suratul bakara 36, Suratul Isra'i 26, Suratul Rum 38,   Suratul bakara 210,  Suratul Nisa'i 2 .2- Sada zumunta yana kara tsawon rai,  Bukari 5986,  Muslum 2557.3- Sada zumunta yana kara arziki,  Bukari 5986


4- Sada zumunta yana cikin abubuwan da akayi Umarni dashi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, Bukari 7


5- Sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah,  Bukari 5983 


6- Sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah yake so. Sahihut-targib 2/667.


7- Sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, Abu Dauda 4902


8- Sada zumunta wasiyyar da Annabi saw yayi wa Al'ummarsa. Sahihut-targib 2/6699- Sada zumunta siffar muminai ce.10  Sada zumunta yana sawa a karfi aikin mutum. Sahihut-targib 2/674 11- Sada zumunta yana cikin siffofin masu hankali.12- Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya dinka sada zumunta,. Bukari da Muslum.13- Sada zumunta yana kare mutum daga laantar Allah ,  Tafsir Ibn kasir Suratul Ra'adi,25.14- Yin Sadaka ga yan uwan zumunta, yana jawo lada biyu,  na Sadaka dana zumunta. Sahihu,Sunanil Tirmiziy. 1/202 .15,  Sada zumunta yana kara soyayya tsakanin dangi da yan'uwa .16- Sada zumunta yana kara hadin kai tsakanin yan'uwa. 17- Wanda baya sada zumunta bazai shiga Aljannah ba. 18- Allah taala ya yiwa Zumunta alkawari zai sadar da wanda ya sadar da ita,  zai yankewa wanda ya yanketa. 19 , Mai sada zumunta shine wanda ko baa zo masa ba, shi zai je. 20,  Baya cikin sada zumunta sai wanda yazo maka kawai zaka je masa.YA ALLAH KASA MUYI RIKO DA ZUMUNCI AMEEEN.

Comments