Main menu

Pages

AMFANIN LALLEN GARGAJIYA GA DAN ADAM


 


AMFANIN LALLE DA MAGUNGUNAN DA YAKE YI.


Lalle wanda muka sani a kasarmu ta Hausa wata bishiya ce da mata suka fi yawan amfani da ganyenta musamman dan yin kwalliya a lokutan bukukuwan aure. A nan ba ina nufin lallen da ake yin zanen jiki na siffa ba, ina nufin lallen da muka sani na gargajiya da aka daina yin sa musamman a wannan lokacin.Ita dai bishiyar lalle tana da ganye launin kore da hure da kuma sayyu, wadanda dukkanin su ana amfani da su a sarrafa a yi magani da shi. Ganin yanda wasu sun dauki lalle tamkar kayan ado na mata kawai wadanda ko su a yanzu sun daina yin lallen nan na gargajiya da na ke magana a kai, inda suka rungumi amfani da wannan da ake siyarwa a shaguna wanda wannan lallen hade-hade ne kawai na wasu sinadaran da har illatarwa suke yi. Kusan abin da suke kallon maccen da take yin lallen gargajiya tamkar bakauyiya.A yau wannan shafin ya dukufa wajen farfado da asalin maganin da muke da shi tun a zamanin da wanda aka dauki lokaci mai tsawo ana cin moriyarsu, amma sai gashi a yanzu an fara mantawa da su, shi ya sa wasu cututtukan zamani suka gagari magani.-Na farko dai darajar mace mai yin lalle ba ta daya da wacce ba ta yi ko farin jinin su da tagomashin su ba zai zamo daya ba.-Lalle kariya ce daga aljannu dalili a nan shi ne, akwai miyagun aljanun da suka tsani ganyen lalle.-Lalle na karya sihiri a jikin mace, dan haka sai a nemi ciyawar aniya makomiya a dake tare da ganyen lalle a ringa shafawa.-Lalle kariya ce daga cututtuka masu dama musamman na fata.


Comments