Main menu

Pages

 




Kala kala juices na kayan marmari kala kala, gara kina hada abinki da kanki don sunfi na gwangwani amfani.


PINEAPPLE & YOGHURT ICE


INGREDIENTS


Abarba

yoghurt

flavour

sugar


       Yadda ake hadawa


Da farko kiyanka abarba a markada acikin blander kitace saiki juye awani abin ki zuba yoghurt akai 

Da flavour da sugar da kuma kankara ko kisa acikin fridge za, asha da sanyi.



      

   PINEAPPLE AND BANANA JUICE

Ingredients:

Pineapple

Banana

Ginger

Sugar.


         Method

Ki cire bayan abarbar ki da bakin nan ki wanke kisa a blender, ki bare citta bada yawaba ki sa a ciki ki zuba ruwa kiyi blending, inya niku sai kisa rariya ko abin tacewa ki tace tas, sai kisamu tukunyarki kijuye ki sa sugar as ur taste, ki kunna wuta kita juyawa like 5mints ki sauke zakiga yadanyi kauri kadan kamar na kwali ko gwangwani.



   kisa a fridge.Inkin tashi sha saiki samu cup dinki kixuba kamar half cup ki dauko banana dinki (itama kinsata a fridge tai sanyi)ki cire bawon ki yanyankata round shape ki xuba acikin juice dinki kisha.




AGWALUMA JUICE/AFRICAN CHERRIES JUICE


INGREDIENTS

*Agwaluma

*Mint leave

*Danyar citta

*Sugar

*Flavour

*Ice cube

   Dafarko zaki samu agwalumanki kibare bayan  kidan gutsuttsurata ki sa sugar ki gauraya kisa a fridge yayi kamsr 30 mint zakiga sugarn ya narke seki kankare gingernki kizuba su duka a blender tare da mint leave amman kadan sekiyi blending ki dandana in sugar yayi shikenan in kuma beyiba seki Kara in ya nuku seki tace kisa ice cubes naki sai kisa a fridge shikenan.



COCUMBER AND APPLE JUICE


INGREDIENTS

*cucumber

*Apple

*pick milk

*suger

*vanilla flavor

*ice block


PREPARATION


Da farko zaki samu cocumber da Apple ki yanka su kanana kanana,sai ki zuba a blender kisa kankara aciki kiyi blending.

Idan kika gama sai ki tace, sai kisa suger and vanilla extract kiyi mixing sosae. 

Idan kingama zaki iya sawa a fridge ko ki kara sa kankaran akai. 



        CUCUMBER JUICE


Ingredients 

Cucumber 

Lemon

Flavor 

Sugar 

Ginger 

Kankara



Dafarko zaki bare ginger dinki ki cire bawon ta sai ki zuba cucumber da ginger din a blender 

Sai  ki matse lemon tsamin ki a ciki ki zuba sugar da flavor da kankara sai kiyi blending nasu dukka sai ki tace ki zuba a glass cup ki kara kankara 



 COCONUT WITH DATE & MILK JUICE


INGREDIENTS

*Coconut

*Date

*Milk

*Syrup sugar{if desired}

*Ice cube

*Flavour





          PREPARATION

   Da farko ki kankare coconut dinki sannan ki yankata qanana~qanana sannan kidan jiqa date dinki yayi laushi  kisa ablender kiyi blending nasu suyi  smooth kada yayi gudaje idan yayi smooth saiki tace kisa a jug kisa syrup sugar if desired tunda date yanada z aqi saiki zuba milk dinki ta ruwa or gari kisa ice cube

Wannan hadin Yana qara ni'ima sosai sannan ga Dadi abaki shikenan our coconut with date and milk is ready 

   

Sai mun hadu daku a post na gaba don ganin me zamu zo maku dashi kuma. Ku cigaba da kasancewa da Taskar Al'ummah.



SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments