Main menu

Pages

AMFANIN HULBA GA RAYUWAR DAN ADAM

A wannan rana za mu kawo mu ku bayani dangane da amfanin Hulba ga lafiyar bil'adama. 


Hulba kamar yadda mu ka san ta, kalma ce ta larabci, da harshen turanci kuwa ana kiran ta da 'Fenugreek'. Hulba wani tsiro ne mai matukar amfani ga lafiya, kuma shekaru aru-aru da su ka shude al'umma ke amfani da ita don samun waraka daga wasu matsalolin lafiya.
Jama'a na amfani da ganye da kuma kwayar hulba wajen samar da magunguna tun a shekarun da su ka gabata. Hulba ta shahara a kasashe da dama a duniya, sai dai anfi samun ta a wasu daga kasashen Larabawa musamman kasar Misra, sannan ana samun hulba a kasar Sin da kuma Indiya.
A kasar Indiya su na kiran ta da, 'Methi' a yaren Hindu, a yaren Telugu na Indiyan kuwa su na kiran ta da 'Menthulu'. Wani bincike da wata kafar yada bayanai ta yanar gizo ta wallafa, ya nuna cewa, Hulba ta shahara a kasar Indiya saboda amfaninta ga lafiya, ta yadda za ka iya kiran ta gidan kowa da akwai.
A al'adance, mutanen kasar Indiya na amfani da kwayar hulba a matsayin wani mahaɗin samar da magunguna, baya ga amfani da su ke da hulba don samar da wasu hade-hade na inganta lafiyar jiki, da kuma yadda su ke amfani da hulba don kula da lafiyar gashi.
Sai dai, binciken zamani na kwanan nan da masana su ka gudanar a kan hulba ya nuna cewa, za ta iya samar da magunguna da hade-haden inganta lafiya daga hulba, fiye da yadda jama'a su ka sani a baya. Daga cikin amfanin hulba ga lafiya da masanan su ka gano, har da taimaka wa ma su ciwon siga, ciwon ido, gyaran gashi da fata. Hakanan, ana amfani da hulba kan matsalar basir, matsalolin ciki da sauran su.
Yanzu ga bayani daki-daki kan amfanin hulba ga lafiyarmu:


1. Hulba na hana Bushewar fata; Bincike ya tabbatar da cewa, yin amfani da hulba na hana bushewar fata. Saboda haka duk mai fama da wannan matsala ta bushewar fata zai iya amfani da hulba don maganin wannan matsala.
Yadda za a yi shine ya samu garin hulba, ya kwaba ta da ruwa, amma kwaben ya yi kauri, sai ya shafa a fuskarsa, ya bar shi tsawon rabin sa'a, daga bisani ya wanke.SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments