Main menu

Pages
 HANYOYI 14 DA ZAKA BI DOMIN GUJEWA AIKATA ZINA: 


Babban Maganin da zai hanaka yin Zina, shine: 

 

1. Tsayuwa abisa tafarkin Allah da Manzonsa (saww) da gaskiya. 

 

2. Cikakken jin tsoron Allah afili da boye. Tare da yin abota da mutanen kirki. 

 

3. Kulawa da yin Sallah akan lokaci, kuma acikin Jam'I. Tare da neman ilimin sanin Sallar. 

 

4. Zikirin Allah safe da yamma tare da neman tsarinsa daga Sharrin Shaitan ako yaushe. 

 

5. Tuna girman Allah da kuma Kusancinsa gareka/gareki. 

Yana tare dakai/dake alokacin da kuke aikata wannan Kaba'irar 

 


 6.Tunowa da girman azabar da Allah ya tanadar ma MAZINATA alahira. Kuma yadda bakaji kunyar sa'ba masa ba, shima ba zaiji nauyin azabtar dakai ba. (Allah shi kiyayemu). 

 


7. Tunowa shaitan da mummunan kaidinsa da yake Qullawa domin hallakar da 'Yan Adam. Tare da Qauracewa duk saurayi da kika tabbatar fasiqi ne, ko budurwar da ka tabbatar fasika ce. 

 


8. Gujewa kadaituwa da duk wata Matar da ba Muharramarka ba/ko Namijin da ba Muharraminki ba. Koda kuwa ya biya sadakinki ai ba'a daura muku aure ba, Kuma baki zama matarsa ba. Don haka har yanzu jikinki bai zama halal dinsa ba. Kada ki yarda ya ta'ba koda yatsan hannunki. 

 


9. Kaucewa kalle-kallen fina-finan batsa. Ko kuma wakoki da hotunan batsa ko litattafan soyayya. Ko duk abinda zai janyo motsawar sha'awa. 

 


10. Kaucewa abota ko Qawance da duk wani saurayi Mazinaci ko budurwa Mazinaciya. 

 

11. Ka tuna cewar Wannan da zaka yi zinar da ita: 'diyar wani ce, Qanwar wani ce, Yayar wani ce. Watarana kuma zata zama Uwar wani. 

 


To yadda kayi Zina da ita, kaima sai anyi Zina da Uwarka, ko Qanwarka, ko yayarka, ko 'yar cikinka wacce ka haifa. 

 


12. Addu'ar neman tsari daga Miyagun ayyuka, da mummunan tunani. 

 

"Allahumma inni a'uzu bika min Munkaratil Akhlaaqi wal Af'aali wal Ahwa'I." 13. Daga karshe kuma ka tuna cewa zaka iya kamuwa da wata mummunar cutar da zata zamanto ajalinka.. Kuma koda baka kamu da Cutar zahiri ba, Wallahi in dai ka aikata zina sai chutar Munafurci da Fasikanci da fajirci ta shiga zuciyarka, zuciyarka ta kekashe. 14. Tuno ranar da za'a tsayar da kai agaban Allah, a ranar taron Alqiyamah.. Ga iyayenka da Kakanninka, ga 'Ya'yanka har Jikokinka da jikokin-Jikokinka.. agabansu al'aurarka zata bada shaidar cewa Ka aikata abu kaza da ita arana kaza, awaje Kaza.. Mala'iku kuma zasu kawoshi arubuce, sannan Allah zai nuna maka hotonka (kamar bidiyo) gaka nan alokacin da kake aikatawa. Fatan Allah shi kiyayemu baki daya daga wannan mummunan aiki. Wadanda kuma shaitan ya riga ya rudesu, to Allah yasa wannan rubutun ya zama dalilin tubansu, Allah yasa mu rabauta baki dayanmu ameen.SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments