Main menu

Pages

YADDA AKE KAMUWA DA ULCER, DA YADDA AKE MAGANCE TA KWATA2
Abubuwan da ke Haddasa Cutar Ulcer da yadda za ayi maganinta idan An Kamu.


Ita dai Cutar Ulcer kamar yadda kowa ya sani ita ake cema gyambon ciki. Kuma akwai sanadin kamuwa da ita da yawa da mu bamu sani ba.
Abu na farko dai shine kamar yadda muka sani ko a cikin Qur'ani Allah da Kansa cewa yayi " qulu wa sharabu" wato Ku ci kusha. Babu inda akace kusha kuci, sai dai kuci kusha.

To hakan sai kaga mutum na jin yunwa amma sai ya dauki ruwa yasha, to Ku sani akwai sinadarin  Allah Ya halitta na acid wanda yake sauak a abincin da mukaci don ya narke.

To duk lokacin da zaka sha ruwa a 'empty stomach' wato cikin da ba abinci, to Ku sani kuna Shan ruwan nan wannan sinadarin zai sauka bisa ruwan da kuka sha alhali shi ruwa ruwane dama baya bukatar abnda zai narkar dashi. 

To da wannan sinadarin ya sauka zai ratsa ruwan ne yaje ya sauka bisa bangon hanji, nan take zai karci wajen, tun yana kadan kadan ana cigaba da wannan dabi'a sai kaga wajen ya zama katon gyambo. Sai kaji ana cewa wane yana da chronic Ulcer.

Haka zalika duk wanda yake da dabi'ar cin cingum, to Ku sani akwai sinadaran narkar da abinci dake saukowa a duk lokacin da mutum yake tauna wani abu a bakinsa. 

To kana tauna cingum kana hadiye yawun nan mai dauke da sidaran narkar da abinci kana turashi cikin ciki, yana zuwa yana narkar da abinci da yayi saura a cikinka, idan babu kuma shima sai yayi ta kartar maka ciki, har ya zama rauni. ( Shiyasa duk yadda kake cikin koshi indai ka ci cingum sai kaji cikinka kamar anyi maka sata) to wannan dalilin shine.
Wasu kuma sai su tashi da safe su ki karyawa da wuri, wannan ba kamar illa bane, an kwanta an dauki wasu awowi anyi barci da safe an tashi ciki fayau kuma ace baza a karya da wuri ba wasu har 12pm suke kaiwa badu karya ba wasu ma fin haka. To dole wannan ya janyo maka Ulcer.

Maganin Ulcer idan ka kamu da ita

Magi yawancin maganin Ulcer da yafi shahara da tasiri a cikin littafan likitanci a musulunci suka sanar shine;
A hada zuma da garin habbatus sauda da garin bawon Ruman sai a hadasu waje daya a ringa shan cokali biyu sau uku a rana.

Idan kuma Ulcer din tayi tsanani wato 'chronic' ana gane ulcer takai matakin karshe ne idan mutum yayi gyatsa sai ya ringa jin wari warin jini. To idan takai wannan matakin sai a kara da garin Kumasari a cikin wancan hadin.
Allah Ya bamu lafiya mai dorewa, marasa lafiya Allah Ya basu Lafiya Ameeen.SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments