Main menu

Pages KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE HANA MACE SHIGA ALJANNAH KODA KUWA TANA SALLAH:-


1) Duk Matar da take da aure tayi zina.


2) Duk Matar da ta Mallaki Mijinta ta hanyar asiri ko ta hanyar tsafi


3) Duk Matar data Hana kishiyarta ta zauna da Mijinta lafiya


4) Duk matar da ta raba mijinta da 'ya'yansa,ko ta Hanyar Asiri ko Yaudara


5) Duk matar data raba mijinta da Yan uwansa ta hanyar asiri ko yaudara


6) Duk matar da tayi asiri akan saukarwa kishiyarta jinin haila duk ranar kwananta sai haila tazo mata


7) Duk matar da tasa aka daure mahaifar kishiyarta,don kar ta haihu


8) Duk matar data dauko ciki a waje ta bawa mijinta,kuma ta tabbata ba nasa bane


9) Duk matar da tayi daurin baka ga mijinta don yayi mata kishiya.Ma'anar baka shine: Duk ranar da zai kwana a dakin kishiyarta sai ya zamanto bana miji ba.Amma idan ya dawo dakin matsafiyar sai ya dawo namiji


10) Duk matar data nemi mijinta ya saketa,alhali baya cutar da ita.Kuma ba yadda ya iya


11) Duk matar da bata godewa mijinta bisa ga irin abubuwan da yake mata na Alkhairi


12) Duk matar da take cutar da mijinta da bakinta


13) Duk matar da batayin wankan janaba, bayan ta sadu da mijinta,ko batayin wankan haila ko biki


14) Duk matar da take tona asirin mijinta a cikin kawayenta


15) Duk matar da take annamimanci


16) Duk matar da take sa kayan da yake nuna tsiraicinta,irin wanda musulunci yake fada akan irin shigar yahudawa da nasara


17) Duk matar data kara gashi akan nata


18) Duk matar da tilastawa mijinta yayi mata wani abu wanda ba zai iya yi ba


19) Duk matar data dauki dan wani ta bashi Mama (Nono) bada izinin Mijinta ba


20) Duk matar da zata cewa Mijinta tunda muke dakai meka taba yi mini.


Dukkan wadannan Laifuka guda 20, ko wani guda daya a ciki, idan Mata ta mutu tanayi bazata shiga Aljannah ba, Koda zata shiga sai an Babbaka ta. YAR UWA KI NEMI ALBARKAR AURE BA ALFAHRI A AURE BA!

بسم الله الحمن الرحيم.

Alhamdulilah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah da ya halicce mu don wata babbar manufa ta bautarsa. 


'Yan uwa mata a wannan zamanin sun canza salon yadda suke shiryawa aurensu, 

suna daukan lokaci na musamman wajen tsara yadda bikin aurensu zai kasance don alfahri da nuna isa, da kuma son a faɗa a dangi ko unguwa ko internet cewa auren su ya fi na kowa, 

a saka gwalagwalai, da riguna masu tsada da takalmi, ayi shiga ta kece raini, ayi su party, a gayyato su DJ a kama (Event centers) masu tsada, 

ayi anko masu tsada, duk a bukin da bazai huce yini ɗaya ko biyu ba, amma sam basa yin shiri akan yadda zamantakewar rayuwar aurensu zata kasance ba.


Wannan yasa zaka ga cewa aure yayi wahala kuma yayi tsada a yanxu, saboda an tsallawa, an kallafa abubuwan da ba sharaɗi ba ne acikin auren. 


'Yan'uwana mata, aure fa bashi ne ayi ɗagawa ba a hau motoci a fita parties ba da kece raini ba ko ɗaukar hotuna tare da kwalliya da canxa fata da halitta ba. 


Aure ba shi ne yin gagarumin taro ba da yin abinci kala kala ba, da rabar da kyautuka, da yin honeymoons, da rawa da kiɗa ba! 
Aure yana nufin yin gwagwarmaya, 
da sadaukarwa, da yarda a tsakanin ma'auratan, da amana a tsakanin su, da godiya, da jin kan jun, da kuma dacewar su a matsayin ma'aurata. 


Aure ba shi ne sai an kashe kudi ba, an yi annuzbaranci, an saɓawa Allah ta hanyar nuna tsiraici ba, 


anyanzu rawa a gaban camera, an chakuɗu maza da mata guri ɗaya ba, anyi kwalliya ta canxa halitta da fidda kama, kaga mace ɓaka ta koma fara, kaga mara hanci ta ƙara hanci. Kai yanzu babu irin fasadin da Mata basa aikatawa a wuraren shagulgulan bukin su. 

  

Ta ya ya aure zai yi albarka? Ta ya ya kuke tunanin ku samu jituwa? da hadin kai?  da tausayin juna? da soyayya ta gaskiya? da aminci? da kwanciyar hankali? ta ya ya kuke tunanin ku haifi yaran da za su yi muku biyayya? Bayan kun gama rushe albarkan auren da saɓon Allah?! 


Bayan kun gina rayuwar aurenku akan ƙarya da yaudara? Bayan kun biyewa ruɗin sheɗan?! Wanda yanzu har gani kuke yi idan har ba'ayi wannan lalacin ba to aure bai yi ba! 


Allah baya taɓa sa albarka acikin abinda aka saɓa masa! Shiyasa za ku ga kun yi auren soyayya, amma sai bayan yan kwanaki kadan ki ga mjjinki ya canxa miki, kune faɗa, rigima, tashin hankali har akai ga yin saki. Sai daga baya azo ana neman gyara da sulhu, wanda shi Allah ba ya gyara aikin maɓarnaci! A taqaice da shawarce, ku sauqaqa acikin aurenku, ku yi adalci, ku nemi albarkar Allah, albarkar Allah kuma ita ce kiyaye dokokinsa da bin abin da ya ce! Saɓa masa kuwa wallahi sai an biya bashin abin da aka yi. 


Domin Allah baya taɓa gyarawa mutane, har sai su sun canza sun gyara da kan su. 
Aure abu ne mai faɗi kwarai da gaske, 


wanda lokaci da yawan rubutu ba zai bani damar ambato su ba, amma dai yana da zurfin gaske da buƙatar daukar dawainiyar juna da sauke nauyin da ke kan juna, na yiwa juna nasiha da aikata alkhairi da barin mummuna, wannan ita ce soyayya ta gaskiya, 


kuma duk saurayin da yake kiranki ga aikata aikin alkhairi to wannan shi ne mafi dacewa da ke, ba wanda zai nuna miki duniya ba, wanda dama ita soyayya tana ginuwa ne akan wannan ta kuma qaru daga kowane bangare,  wannan shine abin da muka koya daga Iyayen mu.Wallahi, babu wani daga cikin iyayenmu mata da suka yi irin wannan shirmen da haukan a bikin aurensu irin yadda muke yi yanzu, su ba'ayi party ba ko zuwa rawa da chasu ba amma wallahi bikin su yayi albarka kuma sun sami farin ciki a auren su saboda duk sun kiyaye abin da Allah ba ya so. Don haka 'yan uwa mata, ku zama kamar iyayen mu na baya, ku shirya kanku a matsayin mace wacce ibada ce zai kai ta dakin aureta, kuma ku roki Allah akan Aure mai albarka ba don wani buri na son burgewa ko soyayya ta ƙarya da kuke yanzu ba da koyi da arna ba.Allah ya baku mazaje nagari masu tunatar da ku gaskiya, ya yi albarka a duk auren da babu party da shedanci irin na wannan zamanin. Tabbas Allah baya taimakon azzalumai
"ZINA TA GAGARI WANI SAURAYI

 

Wata rana Wani Saurayi Yaje wurin wata Budurwa da niyar Fasikanci sai yaje ya Gaya mata sai taki Amince wa Sai ya tafi Sai Bayan ya qara Dawo wa sai Yace mata ta Amince Da Abunda yake buqata tace bazata Amince Ba yace mata ya Bata duka 


Dukiyarsa Tace Bata So Amma Tana So yayi Abu guda Idan Har yayi wallahi Zata Amince Sai yace mata Ta fadi Komi nene Zaiyi Tace Masa Tana so ya Tsaida Salla kar ya sake yayi wasa da ita Har Tsawon Kwana 40 to 


Idan Har yai Haka Wallahi Zata Amince yace To Shikenan Zai Kwatanta Sai ya tafi da yaji Anyi Kiran Salla kafin liman ya Shigo shi har ya Rigashi Shi Kullum Haka Yai Tayi Aka kai kwana 10 aka kai 20 aka kai 30 Ana cika 


Rana Ta 40 kawai sai Yarinyar nan tazo tace yau ne zata Cika Mashi Alqawarin Da Ta Dauka Sai Yace Subahanallai Allah ya Shiryeki 


To jamaa Cika Salla akan lokaci tana Hana Alfasha Kaman Yadda Allah yake Fada a cikin Suratul-Ankabut Aya ta (45) ("Innas-salata Tanha anil fahsha'i Wal-Munkar) zuwa Karshen Aya 


Allah yasa Mu Dace ya kuma tsare mu Daga Aikin shedan Al-barkar Annabi Muhammad (S.A.W.).ILLOLIN SABAWA MAHAIFA.....


Hakika Annabi SAW ya yi mana umarni kamar yadda Allah da kansa yayi mana umarnin akan yin biyayya da kuma kyautata mahaifa,da kuma hani akan sabawa masu da kuma cutar dasu,sabawa mahaifa da rashin kyautata masu yana cikin mafi girma zunubai da akewa yiwa Allah anan duniya. 


Annabi SAW ya baiyana mana illa da girman laifin mai sabawa Mahaifansa, ga kadan daga cikin su:-


*1-Mai Cutar da mahaifansa Tsinanne ne inji Manzon Allah SAW*. 


Daga Abu Hurairaita R.A yana cewa :-

"Annabi s.a.w yana cewa:-

*(La'antacce ne mai cutar da mahaifansa ko mai sabawa mahaifansa)*

@ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻓﻲ" ﺍﻷﻭﺳﻂ

" ‏( 8497 ‏)

@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ " ‏( 2420 ‏)


*2-Allah bawa kallon mai sabawa Mahaifansa a ranar alqiyama*. 


Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-

 " Manzon Allah s.a.w yace:

(Mutane guda ukku Allah bazai kallesu ba a ranar alqiyama:-

*Mai sabawa mahaifansa*

*Wanda baya kishin iyalinsa

...............)*.

@ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏( 2562 ‏)

 @ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ

ﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ 


*3-Mai sabwa mahaifa baya shiga aljanna*. 


Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-

 " Manzon Allah s.a.w yace:

(..............Mutane guda ukku bazasu shiga aljanna ba a gobe alqiyama:-

*Mai sabawa mahaifansa*

*Mai kwankwadar giya*

*Mai yin gorin abinda ya bada)*. 

@ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏( 2562 ‏)

@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ

ﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ " .


*4-Babu mai shiga aljanna sai wanda kasance yana biyayya ga mahaifansa kuma baya saba masu*. 


Wani mutum yazo wajan Annabi s.a.w sai yace Ya Manzon Allah s.a.w:


"Na shaida babu abin bautawa bisa hakki da gaskiya sao Allah kuma kai Manzon Allah ne, kuma nayi salloli biyar na farilla,kuma na bada zakka kuma nayi azumin watan Ramada?? Sai Annabi s.a.w ya ce:


*(Wanda ya mutum akan haka yana tare da Annabawa da Shahidai Siddiqai a ranar alqiyama matuqar bai sabawa Mahaifansa ba)*

  

Allah ka gafarta mana zunabammu kajiqan iyayemmu da gafara.ABUBUWA GUDA SHIDA DA SUKE HANA SAMUN ILMI

Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa "Akwai sabubba guda shida da suke haramtawa bawa samun ilmi, waɗannan abubuwa kuwa sune kamar haka:

1. Barin yin tambaya.

2. Rashin sauraro mai kyau.

3. Rashin yin harda.

4. Rashin yaɗa ilmin.

5. Rashin yin aiki da ilmin

6. Rashin kyakkyawan fahimta. 

مفتاح دار السعادة ١/١٧٢


Shaikh Ibnu Baaz Allah ya masa rahama yake cewa "yana wajaba a kanka (dalibin ilmi) da ka kwaɗaitu wurin yaɗa ilmi ta kowace hanya da zaka iya,


 kada ya zamanto masu yaɗa ɓarna su Fika nishadin yaɗa barnarsu, sannan ka kwaɗaitu wurin anfanar da musulmai cikin Addinin su da duniyarsu"

مجموع الفتاوى ٧/٦٧Comments