Main menu

Pages

 


WANNAN POST YANA BAYANI YADDA AKE GIRKE-GIRKE DA JUICES A SAUKAKE. DON HAKA KU BIYOMU


𝙋𝘼𝙉𝘾𝘼𝙆𝙀


𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Flour (1cup)

*Madara (1/2 cup)

*Sugar (half cup)

*Baking powder (1tspn) 

*Kwai (1)

*Butter (1tspn)

 


 

𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

     Ki hada flour da madara da sugar da baking powder saiki sa ruwa kamar rabin cup ki dama da kyau ki fasa kwai a ciki ki narkar da butter ki kawo ki hada.


Saiki daura kaskon suyan kwai mara kamu (non stick frying pan)

Ki rinqa diba aludayi kina zubawa yana gasuwa ahankali karki cika wuta

Da yayi saiki juya daya gefen


𝙉𝙤𝙩𝙚:-Zaki iya cinsa hakanan Koda narkakkiyar chocolate ko kuma da shayi koda juice mai sanyi.

     
   𝙒𝘼𝙆𝙀 𝘿𝘼 𝙄𝙉𝘿𝙊𝙈𝙄


 


𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Wake gwangwanin madara (4)

*Indomie (4)

*Maggi (8)

*Gishiri (spn1½)

*Curry (tspn)

*Man gyada (1)

*Albasa (1)

*Attarugu (4)

*Tattasa (4)

*Tumatur (2)

*Nama/Kifi 

𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

    Zamu dafa nama ya dahu muzuba masa dan gishiri da Albasa saimu sauke sannan musa mai awuta mu soya nama da kayan miya saimu zuba ruwa rabin kwanonsha .

sannan musasu maggi,curry,gishiri sannan mubar ruwan ya tafasa sannan mu dauko wake da muka dafa amma anaso yafi na wanda za'a hada da taliya dahuwa sai ajuye a tafasashshen sanwar sai akawo Indomie A6allata biyu azuba sannan ajuya ahankali sai asa yankakken Albasa sai arufe idan ya nuna Asauke.

                        
   𝘾𝙃𝙐𝘾𝙐𝙎 𝙋𝙇𝘼𝙄𝙉𝙏𝘼𝙄𝙉𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Agada

*Kwai

*Nama

*Maggi

*Gishiri

*Albasa

*Cittah

*Kayan qamshi 𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉                     

   Dafa nama da albasa,citta maggi,gishiri, idan naman ya dahu sai adakashi aturmi yadaku sosai a ajiye gefe daya feraye agadar amma dafadi sosai da kuma kauri yadda idan an lankwasa bazata karyeba sai adauko wannan dakakken naman dan kadan ahannun ki sai asashi atsakiyar plantain din sai ahade sama da qasan asoke da tsinken sakace haka za'ayi tayi har agama gaba daya kada kwai akwano ko roba zuba maggi da Gishiri sai arinqa daukan wannan agadar ana sawa cikin kwan sannan asoya amai mai zafi amma ayi ahankali gurin saka naman da kuma tsinken sakacen dan kada ya bude ko kuma agadar ta yage Hmmmmm indai namane sai angaji da cinsa

      


 


     𝘽𝘼𝙉𝘼𝙉𝘼 𝘽𝘼𝙇𝙇𝙎𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Flour

*Madara half cup

*Baking powder cokali (1)

*Yeast kwatan cokali

*Sugar dai dai kima

*Ayaba (2)

*Kwai (1) 

𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

Ki hada flour da madara, da yeast da baking powder da sugar da kwai da ayaba (a yayyanka kanana) a hada duka wuri daya. A sa ruwa a dama da kauri kamar Fanke.

Ki rufe ki bari kamar na 30mint, ki daura mai a wuta.Da man ya yi zafi sai kirika  jefawa kamar fanke in ya soyu sai ki kwashe.


𝙉𝙤𝙩𝙚:-Za'a iya sha da shayi ko kuma duk wani abin sha mai sanyi ko zafi.

        𝙁𝘼𝙍𝙁𝙀𝙎𝙊𝙉 𝘿𝘼𝙉𝙆𝘼𝙇𝙄𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Kaza

*Dankalin turawa

*Curry

*Thyme

*Carrot

*Attarugu

*Tumatur

*Gishiri

*Maggi

 𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

    Da farko yar uwata ki fere dankalinki, saikiyanka shi kanana, daga nan sai ki wanke kazanki. Ki fara tafasa kazar da attarugu da curry da garin tafarnuwa da citta da maggi da tumatur da thyme. Idan ya dan dahu, sai ki zuba yankakken dankalin turawar a ciki da green beans da kuma yankakken carrot.   kina iya yin irin wannan girki da safe don a karya.


𝙉𝙤𝙩𝙚:-Ina son janyo hankalin masu karatu cewa duk macen da take zuba man gyada a farfesu to da sauranta a girki, saboda farfesun kaza ko na kifi ko na nama da dai sauransu na dauke ne da kitsen ya wadatar.


 


𝙁𝘼𝙏𝙀𝙉 𝘿𝘼𝙉𝙆𝘼𝙇𝙄(𝙄𝙍𝙄𝙎𝙃 𝙋𝙊𝙏𝘼𝙏𝙊)𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Dankali (irish)

*Attarugu

*Albasa 

*Maggi

*Cittah

*Kifi  (ice fish)

*Alayyahu

*Curry

*Man gyada
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Da farko zaki fere dankalinki,   ki yanka daidai misali.

Sai ki wanke kifinki, ki cire dattin, ki yanka gunduwa-gunduwa, ki zuba albasa da maggi da cittah a kai, sa'annan ki dora a wuta.

Bayan haka sai ki jajjaga attarugu da albasa da cittah ki ajiye.

 Sai ki duba kifinki, idan ya tafasa ki sauke ki barshi ya dan huce, in ya huce sai ki bare shi ki ajiye.

 Anan sai ki dauko tukunya, ki zuba manki ki yanka albasa a ciki, ki barshi ya soyu kadan.

 Kisa jajageggen attarugu da kika jajjaga, sai ki zuba ruwa daidai misali, ki rufe yayi mintina ya tafasa.

 Idan yayi sai ki zuba dankalinki, ki sa maggi da gishiri kadan da kori da cittah, ki rufe ya nuna.

 In yayi sai ki zuba kifinki da alayyahu da albasa, ki juya, ki taba ki ji, idan komai yayi sai ki rufe, ki barshi yayi 5mints

Shi ke nan, ki sauke, ki zubawa mai gida da yara, ACI DADI LPY.

       CHINCHIN


INGREDIENTS

*Flour 

*Sugar

*Kwai (4)

*Mai

*Blueband (2)

*Baking powder (tspn)

*Madara if desirePREPARATION

   Da farko ki samu flourki Mai kyau dai dai yacce kikeso ki tankade ki kada kwanki ki aje a gefe ki zuba sugar,oil,madara,kwai, baking powder kadan kisa ruwa kiyita murzawa but, kada yayi tauri idan Kika Gama gamewa yayi laushi saiki ajiye ki rufe yadan taso saiki qara murzawa saiki yayyanka ki aza abun soyawa kisa Mai ki Kama soyawa idan yayi brown saiki kwashe shikenan

Note:-kada ki cika wuta sbd cika wuta yanasa waje ya soyu ciki akwai qullu aci dadi lpy .

 
     𝙊𝙍𝘼𝙉𝙂𝙀 𝙅𝙐𝙄𝘾𝙀
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Orange

*Ginger

*Syrup sugar𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Da farko kinemi mangwaronki nunanne ki yayyanka qanana~qanana ki cire kwallonsa kisa a blender kisa ginger danya idan suka markadu ki tace kisa syrup sugar kisa qanqara ko afridge axubawa kowa a cup asha dadi lpy.

          𝘼𝙋𝙋𝙇𝙀 𝙅𝙐𝙄𝘾𝙀


𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Apple

*Sugar

*Flavour if desire𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

    Da farko ki same apple dinki mai kyau mai qamshi ki yayyanka qanana~qanana ki xuba a blender ki markada yayi laushi sosai idan kina iya syrup sugar watau dafaffen sugar kisa da flavour sannan kisa qanqara koh afridge yayi sanyi shikenan asha dadi lpy.
     𝘾𝘼𝙍𝙍𝙊𝙏 𝙅𝙐𝙄𝘾𝙀𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Carrots

*Ginger

*Sugar
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Ki sami carrots dinki ki kankare idan yanada dirty ki yanka qanana kisa ablender da ginger kiyi blending idan yayi laushi ki tace kisa sugar kisa afridge yayi sanyi asha dadi lpy

𝙉𝙤𝙩𝙚:-Shi carrots damashi yana qarama mutun hasken ido kinga riba biyu dadi abaki ga qara lpyr ido da haske.

 𝙒𝘼𝙏𝙀𝙍 𝙈𝙀𝙇𝙊𝙉&𝙈𝙄𝙇𝙆 𝙅𝙐𝙄𝘾𝙀
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Water melon

*Sugar 

*Milk
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Da farko idan kika same water melon naki ki yayyanka kiyi blending nata idan tayi laushi ki tace kisa sugar da milk ta ruwa peak or three crown kisa afridge idan babu fridge kisa qanqara shikenan axuba acup asha

𝙉𝙤𝙩𝙚:-wannan hadin kuma yana qara ni'ima kinga abu biyu ga dadi abaki ga teste.

 
𝙅𝙐𝙄𝘾𝙀 𝘿𝙄𝙉 𝘾𝙊𝘾𝙐𝙈𝘽𝙀𝙍 𝘿𝘼 𝙇𝙀𝙈𝙊𝙉 𝙏𝙎𝘼𝙈𝙄𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Cocumber

*Lemon tsami

*Sugar

*Flavour
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

    Da farko ki yayyanka cocumberki da lemon tsami ki cire kwallayen ciki kiyi blending ki tace kisa sugar da flavour asa qanqara ko afridge asha dadi lpy.

     𝘿𝘼𝙈𝘽𝙐𝙉 𝙆𝙒𝘼𝙄

𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Kwai

*Nama

*Attarugu

*Albasa

*Maggi

*Gishiri

*Curry

*Man~gyada
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Da farko sai asami nama ayanka shi awanke sannan adafa da albasa idan ya dahu sai akir6a aturmi

akwashe sannan ajajjaga attarugu,albasa akwashe ahada da naman azuba gishiri,maggi,curry

Asami kwai danye afasa azuba akan nama4 sai adora kaskon suya akan wuta azuba man~gyda ajuye haddden naman aciki ayita juyawa saiya soyu anaci da tea ko haka nan.

    
       𝙎𝙃𝙊𝙍𝙏 𝘽𝙍𝙀𝘼𝘿
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Flour

*Sugar

*Butter

*Madara

*Baking powder


 


𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Zaki saka sugar da butter a bowel kiyi mixing dinsu harsai sugar ta narke

Saikisa madarar gari,baking powder,flour ki gauraya saiya hade jikinsa

Kwa6in yadanyi tauri kadan sai kisashi afridge yayi kamar 30mints

Inkika ciroshi saiki yankashi sannan kisamu fork kiyi bulunan dashi saikisa a oven ki gasa tsawon 10~15mints

Saiki ciro shikenan angama

   

                     𝙁𝘼𝙉𝙆𝙀
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Flour

*Sugar

*Yeast

*Mai

 𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

Da farko uwargida za ki tankade fulawarki a roba mai kyau mai murfi.

Sai ki zuba yeast da sugar da ruwa ki kwaba ya kwabu sosai(ya yi ruwa-ruwa in da zai rika kamun hanu) sai ki rufe  a wuri mai dumi.

Ya sami kamar awa 1or 2 , idan ya yi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mai ya yi zafi.

Anan sai ki rinka deban kullin da ludayi kina sawa a cikin mai kina soyawa ya yi jan suya. Ana iya ci da shayi ko wani lemu

    

𝘿𝘼𝙁𝘼𝙁𝙁𝙄𝙔𝘼𝙍 𝘿𝙊𝙔𝘼 𝘿𝘼 𝙈𝙄𝙔𝘼𝙍 𝙆𝙒𝘼𝙄


𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Doya (gwargwadon bukata)

*Kwai (4)

*Albasa (2)

*Maggi (4)

*Attarugu (3)

*Curry

*Man girki

*Tafarnuwa (2)

*Gishiri

𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

    Da farko zaki fere doyarki ki wanke ki sa atukunya da dan gishiri

Idan yayi sai ki sauke ki zuba a kwanonki

Ki fasa kwanki ki jajjaga attarugu ki yanka albasarki

Ki sa kaskonki a wuta kisa mai ya danyi zafi sai ki zuba kwai kisa attarugu, da albasa, da maggi, da tafarnuwa, da kori,

Sai ki dinga juyawa kadan-kadan kar kisa wuta sosai

Idaan yayi sai ki sauke ki kawo doyarki ki zuba

𝙉𝙤𝙩𝙚:-Ana yin wannan cima da safe. ACI DADI LPY 

   
𝘼𝙇𝘼𝙇𝙀 𝙈𝘼𝙄 𝙃𝘼𝙉𝙏𝘼 𝘿𝘼 𝙆𝙒𝘼𝙄
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Wake

*Kwai

*Hanta

*Attarugu

*Albasa Mai lawashi

*Man~gyada

*Maggi

*Curry if desire
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Da farko ki wanke wakenki ki gurje kwalfarsa idan ya wanku tasss saikisa Attarugu da albasa akai markade idan aka markado saikisa maggi,curry,mai,lawashi, dama Chan kin dafa hantarki da kwai kin yayynka qanana saiki zubasu acikin qullun ki buga idan yana needing na water kiqara ki quqqulla aleda ki Dora tukunyarki da ruwa bada yawaba kisa alalenki kibata 30~35mnts zakiji qamshi yacikaki idan Kika ta6a kikaji tayi shikenan alale Mai hanta da kwai ta kammalu aci dadi lpy

𝙉𝙤𝙩𝙚:-za'a iyacin wannan da miyar attarugu ko ahakan Kuma kada acika wuta wurin dafuwar azubawa kowa a plate

        

    𝙒𝘼𝙄𝙉𝘼𝙍 𝙃𝘼𝙉𝙏𝘼
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Hanta

*Kwai

*Attarugu

*Maggi

*Albasa

*Tumatur

*Gishiri

*Curry

*Man~quli
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Da farko saiki sami hantarki ki yankata qanana~qanana ki wanke kidafa da albasa

idan ta dahu saiki dauko kayan miyarki gaba daya kijajjagasu sannan ki kawo hantarnan ki daka ki hada da kayan miya kizuba maggi,gishri,curry

ki tafasa danyan kwai ki hada kijuya4 ki rinqa diba kina soyawa kamar yadda ake soya wainar kwai sai ince aci dadi lpy.

    

 


    

           𝙋𝙐𝙉𝘿𝙔
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Doya

*Nama

*Kwai

*Mai

*Attarugu

*Albasa

*Curry

*Maggi

 𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

   Kisami doyarki mai kyau da gari kifereta kidafata saiki sami attarugu,albasa,nama ajajjagasu asoya sama~sama adafa kwai ayayyanka aciki bayan ansauke saiki daka doyarki ki hadasu ki kwa6a saiki dinga dunqulewa kina tsomashi acikin soyayyan mai akwai dadin ci matuqa

𝙉𝙤𝙩𝙚:-zaki iya hadashi da cocunut juice or fruits salad or chapman aci dadi lpy 

 

       𝙃𝙐𝙎𝘽𝘼𝙉𝘿 𝙂𝙄𝙁𝙏

𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Flour

*Albasa

*Niqaqqen Nama

*Butter

*Maggi

*Gishiri

*Mai 

*Baking powder

*Zare sabo mai kyau
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

     Idan kika kwa6a flourki da baking powder da butter sai kiyi kwa6in kamarna meat pie daganan saiki dora nikakken namanki da albasa ki soyashi sama~sama sannan saiki murxa flour ki yankata asquare for angle size saiki dauko wanan naman kisaka atsakiya kikamo gefe da gefe duka guri hudun saikisa zare kidaure kisa acikin oven ki gasa zakiga yayi kyau saman qullin zai bude shikenan kin gama aci dadi lpy 
      𝘾𝙄𝙉~𝘾𝙄𝙉 𝙈𝘼𝙄 𝙆𝙒𝘼𝙆𝙒𝘼
𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Kwakwa

*Flour

*Sugar

*Kwai

*Madara

*Butter

*Baking powder
𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

    Ki tankade flour ki zuba baking powder kizuba kwakwa gogaggiya(grated)kisa butter ki murza su hade saiki zuba madarar ruwa cikin sugar kijuya saiya harde saiki fasa kwai acikin flour ki dauko madara da sugar ki kwa6a kina iyasa flavour idan madara tayi dai~dai basaikinsa ruwaba idan batayiba zaki iya qara ruwa kadan Shikenan saiki mulmula ki yanka dai~dai shape dinda kikeso saiki soya Kuma kina iya murza butter da sugar saikisa kwai da madara sai baking powder saiki zuba flour da kwakwa kamar kwa6in cake ko cookies aci dadi lpy.

   

𝘼𝙇𝙆𝙐𝘽𝙐𝙎 𝙈𝘼𝙄 𝘾𝘼𝙍𝙍𝙊𝙏

𝙄𝙉𝙂𝙍𝙀𝘿𝙄𝙀𝙉𝙏𝙎

*Flour

*carrot

*Mai

*Gishiri kadan

*Yeast


𝙋𝙍𝙀𝙋𝘼𝙍𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉

 Idan zakiyi Kamar na tiya 1 saiki tankade flourki ki kawo Mai kamar gwangwani 1 kisa sai dan gishiri kadan sai yeast Shima kamar tspn 2 sai ruwa

Ana so kidan sawa yeast din ruwan gumi ki fara motsashi harya narke sannan ki juye aflourki ki kawo Mai ki juye saiki kawo dan gishirinki kisa kadan sai ruwa shima bada yawaba saiki kwa6a ki buga sosai da kauri akeson kwa6in inya bugu saiki rufe kisa arana


Bayan kamar 2hour zai tashi indai baki cika yeast ba saiki Sami wurin da Zaki xuzzubashi ki shashshafa musu Mai ki zuba dai~dai yadda kike buqata dama kin gyara carrot dinki kin Yayyanka saiki diba ki xuzzuba akan kowanne gwangwani ko kwano inkina buqatar albasa ma zaki iya yankata round haka kijera a madambacin da kike hada kamar xakiyi dambu ki rufe bayan 7~10 mnts zakiji qamshinsa na fita ko kuma ki sami tsinke Mai kyau ki tsira atsakiya inya fito silif to yayi inya dibo dan qullu Kuma saiki barshi ya qara shikenan aci dadi lpy 

   

MU KOMA KICIN

Comments