Main menu

Pages

 MU KOMA KITCHEN 

A yau Zamu leƙa Kitchen dinmu.


Uwargida ,Amaryau ku Matso kusa..

MIYAR OGBONO DA TUWON SEMO..


Kayan Haɗin Miya

Ogbono

Cry fish

Nama

Kayan ciki.

Kifi.. or (Tarwaɗa)

Manja.

Tarugu.Tattasai..,Shambo.🌶️

Albasa..🧄

Daddawa.🥣


Ogu ko Ayayo ko Karkashi ko ɗanyar Kuɓewa duk wanda kikeso zaki iya amfani dashi, Amma mu Yanzu zamuyi amfani da Ganyan Ogu.🥬

Maggi

Gishiri..


Da farko 'Yar uwatah zaki Jajjaga kayan miyanki ki ajiye agefe,Kiwanke Namanki da kayan ciki, da kifinki, Kitafasa Bama da kayan ciki su zaki fara Sakawa 


Domin kayan ciki akwai tauri, ki zuba kayan Miyanki . da Maggi, Gishiri in kina buƙata zaki iya sakawa,Magin Shima ba da yawa Zaki Saka ba,domin Miyar bata Buƙatar jin Maggi Sosai, 


Kii zuba kayan Ƙamshi, Nutmeg,Tafar Nuwa,Citta.., Idan Naman Ya dauko dahuwa Sai ki Zuba kifin ki aciki,ki zuba Daddawa,Da Dakakkaken Cry fishi Ɗinki.. ki Rufe Tukunyarki...


Bayan kamar 10mnts.

Sai ki yanka Ogu ,ki wanke ,ki zuba ciki..


Sai ki samu Frying pan..,ko ƙaramar tunkunya..

Ki Ɗauki Ogbono naki ki dakashi,Ya Daku..

Idan kuma Dama kasuwa An niƙa maki ba ,Ba matsala..


Sai ki zuba Manja a Frying pan dinki da ɗan yawa kamar Gwangwani Ɗaya ki Ɗaura Frying pan ɗin akan wuta ,idan manajan ya Narke,Sauki sauke shi a wuta ki dauko 


Ogbono ki ki zuba acikin manjan ,ki Jujjuya har sai Ogbono Ya Narke ya Haɗe da Manjan ,sai ki Dauke shi ki buɗe tukunyar Dake Kan wuta kijuye wannan Manjan mai haɗe da Ogbono


 ki juya,sai ki rufe ki rage wuta,. After 3mints  ƙi ƙara juyashi zakiga Yayi Yauki,Sai ki rage wuta ki bar shi Yayi kar 10-15 mints sai ki sauke...

..

..

.. TUWON SEMO.

Abubuwan Buƙata


Ruwa 

Kanwa

Semo.


Ki Ɗaura Ruwanki Akan wuta ..

Idan kuna so yayi danƙo sosai zaki iya saka kanwa Kaɗan idan baya Buƙata zaki iya bari shi haka...


Saiki dauko semon ki ,kizuba a roba kisa Ruwa da Muciya kijuya sai kiyi talge..

Idan Talgen Yanuna ,saiki riƙa zuba Semon.. kina Tuƙawa har ya tuƙu.., Sai ki Rufe da murfi Ya silalu sai ki Dauko ledan ki ,ki Nannaɗeshi aciki...


Miyar ogbono 🍛🍛

Ana iya cin Tuwon shinkafa, Tuwon Masara,Tuwon Dawo, Raba ,Amala,Aɓoo Dashi..
Farar taliya da wake da miya


Girkin nan yayi dadi sosai kuma an yaba sosai. gashi ma sauri amma yayi dadi kam..


Kayan aiki;

Taliya

Wake

Kayan miya

Maggi

Mai

Curry


Yadda ake hadawa


Zakiyi gyara kayan miyanki, kisa albasa da dan dama, da yar citta da tafarnuwa, 


idan aka niko sai ki soya ai ki juye ki soyata sai kiyi mata hadi da sinadaran dandano, da Curry, idan tayi ki sauke.


Sai ki gyara wakenki ki wanke ki zuba a tukunya kisa maggi ki yanka albasa ki barshi ya dahu luguf,


 sai ki sauke Sai kisa ruwa a wuta idan ya tausa ki zuba taliya, dadan gishiri, idan ta dahu ki ki juye a basket ki daurayeta. Sai kiyi serving a plate da miya, da wake da taliya.
DAN MALELE


Dan malele ya kasance abincin marmari Yana da Dadi sosae musamman ya samu yaji me dadi


Kayan aiki;

Tsaki Kofi 3

Manja

Yaji

1/2 Ajino

Gishiri tsp 1

Albasa 1

Maggi 2

Ruwa


Yadda ake hadawa


Zaki Dora ruwan sai ki wanke tsakin ki tas ki cire dusar idan ruwan ya tafasa sai ki zuba tsakin ki kisa ajino da gishiri ki juya sai ki rufe ki barshi ya dahu, 


Idan ya fara dahuwa zakiga yana kauri sai ki bude shi sbd yayi kauri sosai idan yayi kauri sai ki sauke


Ki soya manja ki yanka albasa ki xuba Dan malelen a tray kisa Maggi da manja da yaji ki yanka albasa da duk abinda kike so sai ashaFaten tsakin masara


Wannan shine karo na farko dana dafa wannan abincin kuma ta dalilin zulaihat adamu musa da ta tura nagani shine nace bari nagwada. Munji dadinsa sosai mungode


Kayan aiki;

Tsakin masara

Albasa

Attarugu

Tumatur kwara uku

Manja

Maggi da sauran kayan dandano

Yakuwa

tafarnuwa Citta da


Yadda ake hadawa


Da farko zaki daura tukunya a wuta kisa manja idan yayi zafi ki yanka albasa ki zuba kidan soyata sannan ki jajjaga tafarnuwa da citta da attarugu kizuba akai ki jujjya kidan soya sannan ki yanka tumatur ko ki jajjaga kizuba akai sai kizu a kayan dandano dasu curry ki jujjya kibarta tadan soyu


Bayan kinsoya sai kizuba ruwa mai dan yawa sai kirufeta tatafasa sannan kiyanka yakuwanki kiwanketa kizuba akai kijujjya 


sannan kirufeta tadan tafaso sannan kidauko tsakin kizuba akai kijuyashi shikenan sai kibarta tadahu sannan ki sauke


Abunda yasa ban wanke tsakinaba sabida nayi amfani da na leda kuma bata bukatan wankewa saboda batada datti ko kadanShinkafa me kanunfari da miyar nama


Kayan aiki;

Shinkafa

Kanumfari

Mai

Maggi

Spices

Attaruhu

Albasa

gwangwani Tumatur na

Koren tattasai

Karas


Yadda ake hadawa


Da farko zaki wanke shinkafarki ki barta ta tsane, sai ki zuba Mai a pan ki soyata harsai tafara zama brown, Sai ki kawo kanunfari kamar guda 5 ki daka ki zuba dama kin tanadi ruwan zafi sai ki zuba kan shinkafar kisa maggi ki barta ta dahu


Hadin miya, Zaki yanka dayan namanki a tsattsaye, su karas duk a tsaye zaki yanka da albasa sai ki Dora Mai a wuta kisa albasar da kika yanka in tafara soyuwa


Sai ki kawo naman ki zuba kifara juyawa sai ki kawo ataruhu ki zuba da tumatir din gwangwani ki zuba ki juya sai kisa ruwa kadan kisa kayan dandano da spice ki barta kamar minti biyar sai ki duba shknn


 Sai mun hadu a darasi nagaba.Comments