Main menu

Pages

HATTARA DAI 'YAN UWA MUSULMAI

 
MUYI  HATTARA 'YAN UWA MUSULMAI, MU KAME DAGA SHIGA HAKKIN WANI.

Al'amari Mafi girman bakin ciki da tashin hankali aranar Alqiyamah shine babu damar ka bama Iyayenka ko 'Ya'yanka kyautar lada koda guda daya ne. Domin awannan ranar kowa ta kansa yake yi : "Nafsee-Nafsee".


Amma kana ji kana gani za'a kwashe ladan ibadunka mafiya tsada arika rarrabawa ga wasu Jama'a wadanda anan duniya babu wani kyakkyawan shiri atsakaninka dasu. 


Wannan zai faru ne ta dalilin Gulma da habaici da zaginsu da ka rika yi anan duniya. 


Awannan ranar babu wani mutum da zai yafe maka alhakinsa dake kanka.. Koda Mahaifinka ko mahaifiyarka ko Matarka!! (SUBHANALLAH..!!!).


Zaka taho da lodin zunubai "NIKI-NIKI" akanka da doron bayanka!! Kayi gumi kasha wahala... Amma babu mai karbarka.. Babu mai rage maka nauyi..


A haka zaka zo domin wucewa ta kan siradi.. (wata gada ce asaman wutar Jahannama)... Mala'iku suna yi maka tsawa! 


Ga santsi yana kwasarka, ga kuma nauyin ya danqareka.. Ga Jahannama tana kawo maka chafka daga kasa.. Ga kuma nisan tafiyar shekaru dubu arba'in ne {40,000 yrs} INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!. 


Babu abinda yafi rubza mutane su afka cikin Jahannama fiye da abinda Harshensu ya girbo musu... 


'Dan uwa ka kiyaye harshenka.. Shine wakilin zuciyarka. Kuma shine hallakarka take jikinsa... Kar ka rika sakinsa sai akan alkhairi ko abinda zai amfaneka. 


Shi yasa Annabi (saww) yace : "YANA DAGA CIKIN KYAWUN MUSULUNCIN MUTUM, BARINSA GA ABINDA BA ZAI AMFANESHI BA".


Kuma yace "DUK WANDA YAYI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA, TO YA FA'DI ALKHAIRI KO YAYI SHURU".


Ya Allah ka shiryemu ka tsarkake mana zukatanmu domin kai ne mafi alkhairin mai tsarkaketa. السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته


*__انا مسلم___________


” بسم الله الرحمن الرحيم


BAYANI GAME DA TSAFI, BOKANCI DA MAITA*BAYANI DA HARAMCIN TSAFI*


Darasi Na 1


Tsafi (ko sihiri) ya kasu kashi daban daban. ba tare da cewar dɓle sai an bayar da ma’anar tsafi ba, zamu iya fahimtar menene tsafi a lɓkacin da muka ɗauko bayanin rabe rabensu. 


matsafa sukan yi tsafi ne saboda wassu dalilai kamar: 


1. nunabajinta. 


2. cutar da abɓkin gaba. 


3. neman samun rTba ko cin nasara akan wani batu (kamar aure) 


4. Sana’a. 


5. Neman waraka daga wata jinya 


2.1 TSAFI SABODA NUNA BAJINTA. 


2.1.1 Tsafi lokacin wasanni: 


Da yawan matsafa sukan yi tsafi ne lɓkacin wasanni sabɓda su nuna bajinta, bajintar sai ta jawo musu ɗaukaka a wurin jama’a. A wani lokaci (kamar ranar wani biki na al’ada) 


Akan tara jama’a matsafa su zo kɓwa ya nuna irin kwarewarsa ta tsafi, jama’a suyi ta kuwwa ana samun nishaɗi. Daga cikin sana’oin hausawa, akwai waɗanda 


wasanninsu ya shahara da nune nunen tsafi. Wasanni irin na wanzame, mafarauta da maƙera suna daga na gaba-gaba a jerin wasannin da ake nuna tsafe-tsafe. Mafi yawan tsafi da akeyi a lokutan wasanni yana daga cikin nau’in tsafi na rufa ido. 


2.1.2 Tsafi na rufa ido: tsafin rufa ido yana faruwa ne a lɓkacin da mutum ya zo da 


wata dabara wacce take ɓoye ainihin (haƙTƙanin) yadda abu yake, sai mutane su ga abun tsafin nasa da wata siffa da bashi da ita a zahirin gaskiya. 


Mu ɗauki misalin igiya. A zahirin gaskiya, idan aka jefar da igiya ba zata motsa ba, 


kuma siffar igiya daban take da ta maciji. Mai tsafin rufa-ido zai iya ya zo da wassu

 

dabaru (na sihiri) sai ya arɓ siffofin maciji ya dorasu akan igiya, sai mutane su dora 

ganin igiya ta zama (kumurcin) macijiya tana motsawa. 


Irin wannan tsafi (na rufa ido da igiya) shi ne kafiran lokacin Annabi Musa (A.S) suka ƙware akai. 


Da irinsa ne suke taƙama da ganin cewa za su rinjayi Mu’ujizar Annabi Musa (A.S). WATA RANA MANZON ALLAH S. A. W suna zaune da abu zarr da yamma sai rana ta kusa faduwa sai manzon ALLAH S. A. W ya tambayi abu zarr yace ya abu zarr shin kasan yadda ranan nan zata fadi sai abu zarr yace ALLAH da manzonsa su sukafi sanin inda zata fadi sai manzon ALLAH S. A. W yace


Ba faduwa takeyiba tana zuwa gaban ALLAH ne tayi sujada sai ALLAH yace an karbi sujjadarki sai ta wuce ta bullo ta gabas sai gari ya waye. To ananan ananan


wata rana zataje gaban ALLAH tayi sujjada sai

ALLAH yace an karbi sujjadar ki ammaki koma ta inda kika fito yau babu hanya. Sai ta koma ta fito ta yamma sai gari ya waye al umma zasu wayi gari rana tafito ta yamma xata fadi a gabas. To wannan rana ranace


wadda ALLAH YA rufe karbar tuba ko da kafirine yayi kalmatush shahada ALLAH bazai karba ba domin yarufe littafin kowa da kowa. to tmbyta anan


itace shin wannan wace ranace kuma yaushe ce


INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN! YA ALLAH KA bamu kyakkyawan karshe. Kuma dan ALLAH don son annabinsa duk wanda ya karanta kuma yayi Imani ya nemi gafarar ALLAH ko zamuyi kyakkyawan karshe. Astaghfirullah wana tubu ilaihi           
اللهم ارزق من نشرها الفردوسئ الاعل

Comments