Main menu

Pages

AMARYA TA SIYAR DA BUDURCINTA SBD KUDIN EVENT AMARYA TA RASA BUDURCINTA  WAJEN  NEMAN  KUDIN  YIN  “EVENT ” DIN  AUREN TA  

 Labarine mai ban takaici da wasu 'yanmatanmu suke jefa kansu, saboda wani kyale-kyalen Duniya, ko zugan kawaye. Don haka mata ku farka ku rike kimarku da mutuncinku.

Akwai tashin hankali kwarai a wannan labarin.


Wanda ya ruwaito  labarin ya fara ne kamar haka;


Dazu na hadu da wani abokina, muna cikin surutai sai yake bani wannan labari me ta yar da hankali.


Yace min a watan Nuwamba 2020, yaje wurin wani mai gidansa,  suna tattauna wata harkar kasuwanci, sun gama suna hira sai aka kira maigidan nasa a waya, sai ya dauka. 


Mace ce ta kirashi, sai take ce mishi “don Allah Sir, ka kara ko da dubu 20 (₦20,000) ne ya zama dubu 70 (₦70,000) ka taimaka min don Allah, na lissafa yanda ka ce min din, ba naki bane, amma wallahi bazai isheni ba.


Sai yace mata, ke, na siya ₦50,000 idan kin siyar, in fada miki lokaci da wuri, abu gashinan baja-baja a gari, saboda ma inaso in taimakeki ne yasa zan bada har ₦50,000 a abunda zan iya samu a dubu daya da dari biyar (₦1500)!


Abokina ya yi zugum bai gane mai ke faruwa ba, bayan sun gama wayan sai Maigidan nasa yake fadamishi.


Wai wannan yar banzan yarinyar, Aure zatayi, mijinta ya bata dubu 50 suje suyi walima, amma ita da kawayen ta da yan uwanta sunce sai anyi shagali “Events” koda Guda biyu ne. 


Yace bashi da hali, bazai bayar ba kuma bazai halarci duk shagalin da suka shirya ba. Da Amaryar suka matsa masa lamba sai anyi ko da event daya ne. 


Yaki amma dai a karshe da ya gaji sai yace ko dai suyi walima ko kuma suje suyi duk abinda zasuyi da wannan dubu 50 din da ya basu, amma shi ba zai kara ko sisi ba.


To saboda Amaryar suna son dole sai anyi event, shine tazo ta roki shi wannan Alhaji yayi Amfani da ita ya bata dubu 100 


(₦100,000) ta cika zata sayi wasu designer kaya, da wani special decoration, ta biya MC da DJ, tayi lissafi, tana neman cikon Dubu 100 (₦100,000)!


Shi kuma Alhaji yace abun just few minutes ba zai bayar da dubu 100 ba? Ba ta da hankali, ya koreta, 


shine ta matsa mishi da waya, har sai da ya gaji yace zai bayar da dubu 50. Shima hamsin din don Budurwa ce jagal babu abinda ya taba gitta ta! Wa’iyazu billah.


Suna cikin haka sai gashi ta kara kira, tace mishi inane zasu hadu? Kuma don Allah yazo dashi Cash, tace masa wai Don Allah idan tazo yau, tazo gobe, zai bata dubu 70 din? 


Yace A’a, tace mai, ita fa budurwace, bata taba saduwa da wani ba a rayuwarta, idan bacin kaddara da Mijinta ne zai fara saninta nan da yan kwanaki, 


Amma shi zai samu a sama amma bai daraja budurcin ta ya bata dubu 100 ba? Haba ya duba, da kudin da zai rasa, da Abinda zai rasa wanne yafi daraja?


Yace mata kudi yafi daraja, don itama zata siyar da nata abun mai karamin daraja ta karbi kudi, masu babban daraja, idan kuma nata yafi daraja, toh ta tafi ta barmasa nasa, tace to ina zasu hadu?


Ya bata (inda zasu hadu suyi zinar) hotel room da time ya kashe wayarsa.


Abokina yayi jigum ya kasa magana kawai yana sauraren abunda ke wakana tsakanin Alhaji da wannan amarya, 


nan Alhaji ya bar shi zaune ya tafi hotel abunsa (inda za ta same shi ya yayi zinar da ita). Innalillahi wainna ilaihirrajiun!


Wannan wane irin masifa ce, akan event ki rasa darajar ki? Kai jama’a, wannan wani irin rayuwa ne?


 Irin wannan kananan abubuwan da muke kau da kanmu akai muna dauka fa ba abakin komai ba, toh kunji inda suka kai yanzu.


Ya kamata dai a duba, kuma a tashi tsaye da addua, mazanmu da matanmu.LIMAMI BARAWO!

A watan Ramadan,wasu mutane suka gayyaci wani limami shan ruwa a gidansu,sabida girmama shi da suke yi,a gurin da limamin ya zauna zai ci abinci,matar gidan ta manta da kudin ta a gurin,


Bayan liman ya gama cin abinci yayi sallama ya tafi,sai ta duba,amma sai bata ga kudin ba,kuma bata da yara,kuma babu Wanda ya shigo gidan sai wannan liman din.


Sai ta fada wa mijinta,tace yaje ya sameshi,Dan ya karbo mata kudin ta.


Sai yace mata bai kamata a kunyata shi ba,ko a zubar masa da mutunci,sabida yana da kima a idon mutane.


Amma suka yanke shawarar su dena bin sa sallah,kuma su yanke duk wata alaqa dashi,haka ko suka yi.


Ana nan sai Allah ya sake kai su wani Ramadan din,sai mijin ya nuna wa matar,falalar yafiya,da kuma mantawa da komai da ya faru tsakaninsu da liman,kuma ma ya kamata su gayyato shi Dan ya zo yayi buda baki a gurinsu,Dan su sami cikakkiyar lada.


Sai matar tace ta yadda,amma da sharadin idan limamin ya gama buda baki,su nuna masa rashin kyautawar abinda yayi,sai mijin ya amince da sharadin.


Bayan sun gayyato liman,kuma ya gama buda baki zai tafi,sai matar ta yiwa liman magana,kan cewa a waccan shekara,sun ajiye kudin,kuma sun tabbatar shi ya dauka,sabida haka wannan abu ne da bai dace ba....


Sai wannan limamin ya sunkuyar da kai,da ya dago kai,sai ga idanuwansa cike da hawaye...


Yace tabbas ni na dau kudin......


Sai suka ce to shikenan ya dena kuka,


Sai yace masu ba yana kuka bane dan ya dauki kudin,yana kuka ne sabida sunyi kwana dari uku da sittin da biyar (365) basu karanta alqurani ba. 


ya ce a lokacin da ya dau ki kudin,ya saka shi ne a shafin farko na alqurani,a inda suratul fatiha take.


Sai matar ta tashi taje ta bude alqurani, sai ta ga kudin a ciki...


Sai suka fashe da kuka,sai suka durkusa a gaban liman suna neman yafiya akan abinda suka masa....


Sai yace masu:ni din me? Ai ba ni kuka yiwa laifi ba,Allah kuka yi mawa, sai Ku koma Ku nemi gafarar sa.


Mafi yawancin mu haka muke yanzun,mun kauracewa alqurani.....


Allah ya bamu ikon gyara wa.

Comments