Main menu

Pages

MAGANIN ZAZZABIN DA AKE FAMA DA SHI MAI NACI

 

MAGANIN WANNAN ZAZZABIN DA AKE FAMA DASHI 


Dan Allah ayi sharing zuwa wasu group baka San iya Kan rayukan da zaka ceta ba dalilin sharing dinka


Wannan yawan rashin lafiyan da ke fama dashi a sasan kasan Nan yayi yawa ko ina ana ta fama dashi in kaje asibiti ace malariya ace typhoid. 


Haka Nan gashi ana ta fama dashi wurare da yawa asibitoci sun cika da Marassa lafiya Wanda suka kamu Allah ya basu lafiya Allah yasa kaffara ce mu da bamu kamu ba Allah ya kare mu 


To  yau munzo da wannan taymko na yadda yadda samu waraka daga wannan mashashara da ta zama kamar annoba

Da farko za'a samu lemon tsami Guda uku

Sai suga babban cokali uku 

Sai gishiri babban cokali daya

Sai a samu ganyen bishiyar dogon yaro wato bushiyar turare

Sai a debo ganyen shi da Dan yawa haka

Sai a samu ruwa Mai Dan dama kamar Lita biyar


Sai a zuba su a tukunya a tafasa su idan ta tafasa sai a sauke shi 

A tsiyaye ruwan sai a samu kankara babba Guda daya sai a jefa a ciki sai ta narke 


Sai a fara amfani dashi Asha Kofi daya da safe bayan anci abinci Kofi daya da Rana bayan anci abinci haka kofi daya da Daddare bayan anci abinci haka za'ayi har ya kare.


Wannan Abu da muka fada hadin Shan mutum daya ne, yaro kuma a bashi Rabin Kofi kamar yadda mukayi bayani a baya


Da yardan Allah za'a samu waraka da gaggawa


Dan Allah a taymka ayi sharing dan Al'ummar Annabi su amfana duk Wanda yayi amfani dashi ya samu lafiya dalilin sharing dinka kaima kana da lada Mai yawa



Amfanin dabino a jikin mutum

_Kayan marmari su na da amfani kamar yadda mu ka fara fada maku_


– Dabino na da amfani a jikin Adam kwarai da gaske


– Kadan daga ciki akwai maganin cutar sikila, kansa da sauran su


Ka ji irin amfanin dabino a jikin mutum

Dabino na da matukar amfani


A jiya muka kawo maku irin amfanin kayen marmari kamar su abarba da sauran su. Ita Abarba na maganin cutar nan ta atiraitis mai damun gabbai da cancer da sanyi sannan kuma tana kara kaifin gani da kuma hakora.


Haka kuma dabino na da amfani matuka daga ciki:


1.Maganin gudawa


Dabino na maganin cutar gudawa da duk wani ciwo ko lalacewar ciki da ake fama da shi.


2.Cancer


Haka kuma dabino na maganin cutar nan ta ’Cancer’ mai kashe kwayoyin garkuwa


3.Dabino na kara lafiya


Dabino na kara lafiya inda yake karawa mutum kiba saboda wasu sinadarai da yake kunshe da su.


4.Dabino na kara karfi


A dalilin irin sindaran da ke ciki na Calcium, Sulphur, Iron da sauran su, Dabino na kara karfi har kwanjin mutum ya karu.


Shi ya sa ma dai ake son cin dabino da zaran masu azumi sun sha ruwa domin kuwa yana kara karfi. Haka kuma ake ba yaro da zarar an haife sa.



Alamu 7 da mutum zai gane jikinsa na bukatar ruwa wanda mutane basu sani ba



-70% na jikin dan adam ruwa ne, hakan yana nuna cewa jikin yana bukatar ruwa sosai don cigaba da rayuwa -Jinin jiki ma 83% dinsa ruwa ne, sannan sai kwakwalwa ma tana da 76% nata wanda shima ruwa ne 70% na jikin dan adam ruwa ne, 


hakan yana nuna cewa jikin yana bukatar ruwa sosai don cigaba da rayuwa. Haka zalika jijiyoyin jiki da kwada ma duk kusan ruwane.


Jinin jiki ma 83% dinsa ruwa ne, sannan sai kwakwalwa ma tana da 76% nata wanda shima ruwa ne.


Jiki yana rage ruwa ta hanyar numfashi zufa da kuma fitsari, saboda haka yake da kyau ka ringa shan ruwa dayawa a kowace rana.


Masana ma sun bayyana cewa ana bukatar ka ringa shan kofin ruwa 6 zuwa 8 a kowace rana, amma yawancin mutane basu wuce biyu.


Maza ana bukatar susha lita 3 ta ruwa ko kofi 12, mata kuma bukatar su ringa shan lita 2.2 ko kuma kofi 9 na ruwa.


Rashin isashshen ruwa a jiki yana kawo tsanewar jiki, wanda ake ganewa ta hanyar alamun. Alamu 7 da mutum zai gane jikinsa na bukatar ruwa wanda mutane basu sani ba


1. Bakin Fitsari Shine abu na farko dake nuna maka cewa jikinka na bukatar ruwa sosai.


Fitsari na mai lfiya zaka ganshi dorowane mai haske.


Idan baka dauki shan ruwa da muhimmanci ba zai kawo maka matsala a kodar ka, saboda zata ringa fitar da mataccen jini ta nan mai dama shine yasa zakaga fitsainka yayi duhu.


2. Ragowar Fitsari Duk mutum mai lafiya yana yin fitsari a kalla sau 6 ko 7 a cikin awowi 24.


Amma idan baka sha ruwa yanda ya kamata ba jikin bazai mayar da ruwan da ya fitar ba cikin lokaci, wanda keda koda ta bushe bayan anaso koda yaushe ta kasance akwai ruwa mai dama cikinta.


3. Shakuwa Babbar alamace dake nuna tsanewar jiki, kuma yawanci, zakaga idan ka yawaita shan ruwa zai magance maka matsalar.


Idan bakasha isashshe ba zakaga kana yin kasha mai tauri, kuma idan babu isashshen ruwa a jikinka to jikin zai jawo ruwa daga jijiyonka don ya cigaba da aiki.


4. Bushewar jiki Yawanci mata suna kashe kudi wurin sayen man jiki, wanda ke sanya laushin fata. Dr. Diana Howard tace, tsanewar jiki shine ke kawo canzawar launin jiki da kaikayi.


Wani lokaci zakaga jikin ya bushe har fata na tsagewa da jini yana fita ta fatar


5. Yunwa da kuma Karin nauyin jiki Jikin dan adam inji ne mai dabara, amma kuma bazai iya banbance tsakanin yunwa da kishirwa ba.


Shiyasa akeso ka ringa kula da lafiyarka ta hanyar shan ruwa yanda ya kamata da kuma kula da kibar jikinka.


Dakaji yunwa anaso kasha ruwa kafin kaci abinci, idan ka cigaba da jin yuwar bayan minti 15 sai kaci abinci.


6. Kishi ko bushewar baki Kishirwa babbar alamace a jikin dan adam wadda ke nuna cewa jikin na bukatar ruwa. Bushewar baki alamace da akafi saurin gane cewa mutum na jin kishi, shiyasa akeso ka yawaita shan ruwa a kowace rana.


7. Ciwon kai Idan baka sha isashshen ruwa ba, jikin yana janyo ruwa daga jijiyoyinka, kamar yanda muka riga muka fada, saboda yana kokarin tara ruwan da ya kamata yayi aiki dashi.


Haka zalika yana jawo ruwa daga kwawalwa wanda hakan yakesa kwakwalwar tana rabuwa da kasha kai wanda ke sanya ciwon kai. Kuma rashin ruwa a jiki yana rage yawan jinin dake jikin mutum.


Sai mum hadu a post na gaba.

Comments