Main menu

Pages

 



ILLAR RABA DAKI DA MAI GIDA_


Shin yan uwa Kunsan illar raba daKi da miji? 

Toh Ku saurara Kuji:-

1- yana rage Kusanci Ko shaKuwa a tsaKanin ma'aurata.


2- yana sa ma aurata su rika jin wani iri wajen neman juna don kauda sha'awarsu ko raya sunnah mace zata ki zuwa wajen mijinta tace ai idan yana da bukatarta ya nemeta, shi Kuma miji ya hakince a dakinsa yaki zuwa wajen matarsa yana jira sai ta biyoshi, karshe sai dai su rungumi Pillow su kwana suna jin haushin juna.


3- yana sa fada yayi tsawo a tsakanin maaurata idan sun samu sabani, sai a dauki kwana ki basu shiryaba.


4- yana sa miji ya samu daman yi wa matarsa iyaka da wasu abubuwanshi ababen cikin dakinsa


5- yana sa mace ta rika jin dar-dar duk lokacin da ta shiga dakin mai gida da niyyar kwalema ko neman wani abu, musamman idan ya shigo ya tarada ita a ciki dakinsa tana dube-dube Ko neme-nemen wani abu

.

*_HIKIMAR KWANA DAKI DAYA DA MIJI:-_*

1- yana sa shakuwa da karin sabo

2- yana sa tausayi da sanin halin da Partner ke ciki a cikin awoyin bacci.(incase daya daga cikinsu zai samu nyt fever, bad dream ko Wani attacK cikin


HATTARA DAI MA'AURATA 


HIRAR DARE

mu Lura da wannan 'yar'uwa Mata, hirar dare nasa maigida ya daina fita yawo da daddare, Saboda baya samun hirar dare daga Gare ki, Kuma Galibi idan suka fita, sai sun raba dare Ana tadi a waje, lokacin da zai dawo, ke Kuma sannan Kinyi barci.


Kinga irin wannan Ina amfaninsa.


Kin dinga jawo hankalin maigidanki, ta wannan sigar, domin ya kaucewa hanyar Banza kamar zina, debo cuta, shan giya da sauransu.


A Kullum Bayan sallah Isha, idan aka ci abinci, sai a dasa hira, Har lokacin barci yayi, in ma mijinki baya so, to Yau da Kullum idan ya ga ki Na yawan damunsa da hirar.


To Zaki ga ya dawo yana so, muddin kika saba masa da wannan, ba zai dinga fita yawo ba, Amma idan kika yi saka ci ya saba da fita, to duk Randa kika so ya Bari, ba zai Bari ba.


       SANA'A GA MATA


kiyi kokarin yin Sana'a koda kuwa ba ki da jari Mai karfi, to ki yi da Dan Abinda kike da shi, Saboda zama haka ba shida dadi, gara a Dan dinga Neman abin dogara da Kai kuma idan kina nema ki dinga taimakon maigida koda ba shine, idan ya samu ya biya zai dinga jin dadi Kuma zai kara sonki, Saboda tallafa masa da kike yi.


Dan Maggi, da sauran bukata.


Mu dage mu nemi Sana'a yar'uwa zama haka ba Bamu bane, tunda wani namiji Ko yana da shi, ba zai dinga Baki  Kullum ba, kin ga Ko idan kina Sana'a Zaki tallafa ma kanki da 'ya'yan ki,Kuma Zaki rage samun matsaloli tsakanin ki da maigida.


               SHAWARA


yan'uwa Mata ga shawara a garemu Baki daya, idan muna Sana'a, tofa gaskiya mu Lura mu rage yawon zuwa kasuwanni Ko Kuma mu fita zuwa kasashen ketare sarin Kaya ! Gaskiya ire-ire wadannan basu dace damu ba, Saboda Ko muna yi tsakanin da Allah, to a duniya ba kowane zai yarda da hakan ba.


Wasu ma sai Kaga mace ita kadai Ce a wurin mijinta daga ita sai 'ya'yanta, Amma ta Kasa zama ta Lura dasu da tarbiyyansu, to ire-ire wadannan duk hanyoyi ne Na nemo matsala tsakaninki da maigida Don kuwa muddin Sha'awa ta dame shi.


To watakila yaje ya nemo a waje, ke Kuma ki Na can kina yawon Sana'a Ko Kuma ya kara aure, Kinga kenan an sha dake, to gara mu rage, Saboda Ko kin bar mai ,Mai aiki , ba zata kula dasu kamar ke ba.


KI ZAMA MAI BOYE SIRRIN KI


kiboye sirrinki ga iyayenki, iyayen mijinki, yarki, "Yan'uwanki, da sauransu, karki zama komai aka yi a gidanki, idan wani naki yazo, sai kin Fada masa, Ko Kuma ke ki zari gyale da takalmi kije ki Fada.


Wannan ba Abu ne Mai kyau ba, muguwar dabi'a Ce,Kuma kina rage ma kanki mutunci da daraja da soyayya a idon mijinki da idon jama'a Baki daya.


Kuma idan mutane suka ganeki, zasu dinga zundenki, suna miki tsegumi, Don haka ki zama Mai sirrin, musamman ma ga iyayenki, sai zaman lafiya, ya wadace Ku da mijinki da kishiyarki radam! Amma iyayenki basu manta ba, Saboda an Ce tsakanin miji da Mata sai Allah.


Komai yana bukata sirrin, Kuma maigida zai dinga gaya miki magana, ba tare da yana shakka ba, Saboda ba Zaki Fada ma wani ba, Amma idan Baki da sirri,to Bama miji ba, kowa ma zai dinga gudunki da magana, domin an San idan aka gaya miki, Zaki fallasar da maganar.



・ ABUBUWAN DA SUKE KAWO NISHADI YAYIN KASANCEWA


akwai abubuwa masu tarin yawa da suke kawo nishadi da annashuwa yadda ma'aurata zasu kasance cikin nishadi.


Ga wasu daga ciki kamar haka:-


 KAUNA DA SOYAYYA 


idan akayi aure Na soyayya, da kaunar juna, to in an kasance a tare Ana samun nishadi.


・ MA'AURATA SU DINGA SHAN KAYAN MARMARI・


musamman ga mace irin su:


・ayaba・abarba・gwanda・lemun zaki・kankana・tuffa・inibi・rake・


sai Kuma ganyayyaki irinsu:


・zogale・salak・kabeji.


sha da cin wadannan kayayyaki ga ma'aurata lokaci zuwa lokaci, jini zai samu gudana a jiki sosai, in Ko jini zai kamata, to an zo jima'i jijiyoyi zasu mike sambal suyi aiki irin yadda ya kamata, to zasu sami nishadi da gamsar da juna.


ya halatta miji da matarsa suyi duk wani Abu da zai sanya su sami gamsuwa a lokaci n da suka kasance a tare in har bai kauce ma shari'ar musulunci ba.



・MIKAR DA NONO KO GYARA NONO・


a kan sami wasu matan Bayan sun girma Ko sun tsufa, sai suce sai sun jera da jikokinsu, wajen tayar da nono kamar Na jikokinsu.


wannan ita take sanya su amfani da manyan magunguna masu karfi wajen tayar da nononsu.


wani sha zasu yi,wani shafawa zasu yi.


to ya zama wajibi Mata su yi hattara domin shan wani magani suyi hattara domin shan magani Ko Shafa wani magani domin tayar da nono yana da matukar hadari ga mace, in Kuma Har sai Anyi,to a nemi shawara Likita, kwararre a kan haka, sannan abi shawara da ya bayar domin Kada a Je Neman gira a rasa idanu.


akwai Mata masu tarin yawa da suka Tafi Neman sai sun ga sun tsaida nononsu.


sai Kuma suka hadu da


・ lalacewar nono.

・ rubewar nono.

・ cutar kansa ga nono.


wasu ta kan Kai da sai an yanke nono, to ya zama wajibi Mata a yi hattara, in kuma za'a yi to a nemi shawara Likita.


・ GYARAN GABA ( FARJI )・


akwai Mata masu tarin yawa da suka dukufa wajen gyara gabansu ta kowace hanya.


・ wasu suyi jike-Jike, sannan su maka a gabansu.


・ Wasu Mai ne Na shafawa suka samo Don shafawa a gabansu.


・ wasu Kuma wani bayani suka karanta a Littafi Ko post kawai sai su Ara su yafa.


・ wasu Kuma wani boka ne ya basu suka Kuma sai su dankara a farjinsu.

  Da sunan wai Neman mafita ne ya Kai su ga yin haka, to duk Abinda za'a yi dai a nemi masana.


・ GYARAN JIKI GA MATA・


ya zama wajibi Mata musulmi da su zama masu gyaran  jikinsu, ta yadda in mazajensu suka zo kwanciya dasu, su ji jikinsu sumul yana santsi yana sheki yana kamshi.


akwai wurare da Mata musulmi suka bude Na gyaran  jiki ga mataye.


Duk wani Abu da mace zatayi Don ta gyara jikinta yadda mijinta zai gamsu da ita, ya halatta, matukar bai sabawa musulunci ba.


Amma in bai sabawa musulunci ba.


・ KARA TSAYI KO KAURI・


a kan samu wasu mazaje da suka dukufa wurin Neman maganin kara kaurin gabansu su, Ko Kuma kara tsayin gaban su.


to, in mutum yana zaune da matarsa Ko Kuma matansa, suna gamsuwa, yana gamsuwa, to ya hakura su rayu a haka.


to Amma in ya zama matarsa Tana da zurfin farji,Ko Fadin farji, to ya halatta ya nemi maganin Karin tsayi,Ko kauri.


To Amma ya zama an bi tsari Na musulunci Ko Kuma ta hanyar Likita.


 HATTARA DAI MA'AURATA 


ya zama wajibi ga ma'aurata dasu natsu, sannan suyi tsan wajen Neman magani Don samun gamsuwa wajen kusantar juna


Saboda dalilai kamar haka:


① magani guba Ce ba'a karbar magani a hannun kowa da kowa.


② Kafin Ayi amfani da magani ya zama wajibi a San inganci magani.


③ dole ne a San kwarewar Mai bada maganin, sannan a San waje shi a matsayin bada magani.


④ umartar a hada wannan ganye, da wancan tsiro,gami da wani ( chemical ) sai kwararre Likita Mai Kayan gwaje-gwaje Na duk wata cutar.


Amma a hada wannan da wancan, Ka sha Ko Ka Shafa, to yana da matukar hadari Saboda ajuujuwan jini da ruwan jikin mutane kala-kala ne, ba iri daya bane, Don haka maimakon magani sai a hadu da Ni "yasu da kaico, in ba Ayi taka-tsan ba.


⑤ wasu marubuta sun zama Yar Mai ganye, suna nan Sunyi Rubutu birjik sun watso shi a cikin jama'a da sunaye kala-kala Na magunguna Mata da maza, Don gyara fata, Ko sanya dadin jima'i.


To ya zama wajibi ga Mata musamman in sun karanta, to su San inganci magani Kafin suyi amfani da shi Saboda magani guba Ce, musamman Wanda za'a sha Ko shafawa, Ko turare.


Wajibi ne ga duk wani Ko wata da suke son suyi rubutu a kan magunguna Na gargajiya wurin hada wannan ganye da wancan gami da wasu hade-hade to Don Allah su nemi masana a kan harka.


Mu sani musulunci ya yarda da bincike da tambaya a kan duk wani Abu da za'a yi rubutu a kansa.


Amma musulunci bai yarda da shaci Fadi ba Ko kirkirar Karya.

Musamman ma a bangaren ciwon lafiya.


Matukar Mata suna son suyi amfani da wani magani da suka karanta a wani litaffi, to ya zama wajibi su San ingancinsa sannan Mai wanne ajin jini ne zai sha Ko ya Shafa, Kuma maganin Na gargajiya ne Ko Na Bature gudun Kada kilu ta jawo bau, garin Neman gira a rasa idanu.


Mu sani Ko da maganin bature wani Kafin a bayar da shi sai Likita yayi umarni Ayi gwaji kamar haka.


☛ jinin mutum.

☛ fitsari


Wani ma sai an yi hotuna kala-kala sannan a tabbatar da magani gudun kuskuren.


Amma Yau wasu kawai sai suce hada kaza da kaza hade-hade ga su nan barkatai sannan ace wai a sha a ruguntsuma a ciki.


Bayan ciki yaki karba, jini ma da ruwan jiki basu karba ba, haka sauran sassan jiki, to daga nan sai jiki yabi ya hargitse, Ko farji ya fara doyi, Ko jiki ya fara fitar da wani wari, to daga nan ne za'a Ce Tafi hospital Bayan komai ya hargitse.


To, ya zama wajibi ga duk wata mace da zata yi amfani da wani magani Don samun Ni'ima ,Ko gyara jiki, to ya zama lallai ta San kwarewar likitan da abindaa ya shafe shi.


In Kuma Mai maganin gargajiya ne to ya zama Lalai a San inganci maganganu.


Ma'aurata Ayi hattara domin rayuwa ta inganta.



_MACEN DA BATA IYA HIRA BA_

Akwai irin wadannan mata da yawa da zaki ga wai idan miji ya dawo ko sannu ba za'a yi masa ba balle a dan yi masa yar'magana ta faranta rai ba sai dai kiga mace tayi kinkirin kamar jaka tana wani muzurai wai ita babu wargi, 


sai nace ke tafi can sokuwa' idan kuma kika ganta cikin kawaye tana zakwabi da gulma kamar ba itace ba, irin su mazajensu basu dadewa da su suke kara aure, idan kuma Allah bai nufa sun kara ba kullum suna titi haka nan za'a yi rayuwa cikin kunci.


Abin da ya dace kiyi da mijinki ya dawo ki mike da azma ko me kike yi kice a a sannu da zuwa

* malam

+ alhaji

+ baban wance

ki amshi kayansa ki adana, sannan ki dan kawo masa abu mai sanyi ( daidai karfinku ) kana ki zauna daga gefensa daman kinyi kwalliyarki tsaftsaf dake kina ta zuba kamshi,


 sai ki dan fara jansa da hira, daga gani ka gaji ko na hada maka ruwan wanka ne? Ko sai kaci abinci ? Yau dai fuskarka babu fara'a kayi hakuri kome ke damunka ka san ita rayuwa sai hakuri to haka zaki dinga magana cikin nutsuwa da kwantar da kai da kissa,


 duk rashin son hirarsa zai saki jiki, amma idan baki masa hira kina da shan takici a gaba don duk randa ya kara aure don ya kular dake da karfi zaki ji yana hira kuwa ya barki da ciwon zuciya kuma ko da kin tsira lokaci dariya zai dinga miki.


Wata kuma idan aka fara hirar sai kiga an kare da fada saboda shegen musunta da gulma tsiya, duk abin da miji yace sai tayi tsalle tace karya ne ba haka bane haba


yar'uwa ko ke ya'yanki ko kanwarki tace karya kike ranki zai baci, idan ma ba daidai ya fadi ba, ki nusar da shi ta hanyar hikima idan kinga ransa zai baci sai kice shi kenan nice ban fahimta ba ca nake sai kaza ne amma yanzu na gane zaki ga shi da kansa yaji kunya ko kuma yayi shiru


Comments