Main menu

Pages

 

FURUCINA NE


              NA


BATUL ADAM JATTKO



```Marubuciyar```

*DAMA TA*

*AMFANIN SOYAYYA*

         ```NOW```

*FURRUCINA NE*



*_________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*_________________________________*




*Page 1*



" Please Madam kar ki damu in sha Allah za ki shiga lfy ki fito lfy mu wannan asbitin aikinmu ba ya samun matsala kin ji? Ki kwantar da hankalinki don kwanciyar hankalinki shi zai ba wa aikinmu karfin gwiwa kin ga a yau ma mata 2 na yi wa Theater nan da sati za ki ji kamar ba ke aka yiwa ba sai de ki sa d'anki a gaba kina kallon sa ki ci kaji ki ci ragon suna".

 Dr Fanna ta k'are maganan tana mata murmushi 

Hajiya Halima ta yi murmushi cikin azaban ciwo ta ce "Dr ba wani Dan Adam da ya isa guje wa kaddararsa a jikina nake jin ba zan rayu da abin da zan haifa ba, amma don Allah Dr Fanna ina neman  alfarma a wajenki dan Allah idan Allah Ya sa ban tashi ba  ki rike min d'ana amana kar ya yi maraici yanda ni na yi kuma ina son ki auri Addulsamad mijina ni ban san asalina ba an ce wai hatsari mota muka yi da Babana shi ya yi loosing  memory wanda har yanzu bai dawo hayyacinsa ba iya sunansa kaɗai ya sani yake iya fada kullum idan na ce masa Baba ina ne gidanmu su waye danginmu ba ya magana sai de ya ce *Nasuru*  ni kuma fuskata ta b'aci aka canza min wata dan da banma san asalin fuskata ta da ba 

a gidan su Abdulsamad na samu kaina kuma shi ya zama mijina.  Ba wahalar da ban yi ba wajen neman dangina ga shi har ina shirin barin duniya ban san ni wacece ba, ban san dangina ba.  Babana bai dawo hayyacinsa ba kuma motan da muka yi accident  da shi ance  ya kone ba asamu wani bayanai a ciki ba. Ina tausaya wa abin da yake cikina don shi ma na san zai yi rayuwa cikin rashin uwa duk da yana da nagatarcen uba kamar Abdulsamad. Ki ceci rayiwan d'ana ta hanyar  auren ubansa dan idan na san a hannunki na bar shi ba ni da sauran damuwa, Dr Fanna kina da tausayi da amana duk da ban san halinki ba, amma ki min alk'awarin za ki auri Addulsamad yana da kirki haka danginsa ma suna da kirki amma hankalina ya fi kwanciya  dake" 


Juyawa ta yi ta kalli inda mijin nata yake da ganin yanda ya hade fuska ka san ba ya son maganganun da take yi. 

Murmushi ta yi ta sake damk'e hannusa ta ce " Ya Abdul na san ba ka son wannan maganganun nawa amma na rasa me ya sa nake yin su nima. Kuma  na san ka amince za ka auri Fanna ko da ina raye ne ina son ka dauki Fanna a matsayin Halima ka ga kai ma ka sha cewa muna yanayi da ita. Abdulsamad ka yafemin idan da gaske ne scanning din da akamin namiji ne abinda zan Haifa kasa masa sunan Babana *NASURUDDEEN* idan macece Halima dan Allah ka ce wa dukkan danginka su yafenin, idan Babana ya warke ka ce masa ya yafe min. Ina son sa  haka  ina son mahaifiyata idan ka ganta ka ce na rayu da son ganinta  Abdul Ina SON KA INA SON KA ,  INA SON KA AURI FANNA SHI NE FANSAR SOYYYAR DA NA MAKA YA ABDULSAMAD ka yafemin" 


Cikin rikicewar murya da tsorata da al'amuran nata ya ce

 " Halima amma mun gama duk wannan maganganun tun a gida ko? Da kin bari an fara aikin nan da yanzu an gama ma."  

Dr Fanna fita ta yi dan wani irin kuka ta ji yana shirin kwace mata da sauri wata  Nurse  ta bi bayanta  

ta ce 

"Dr idan ta k'ara wasu minutes  za a iya samun matsala fa". 

Ficewa ta yi a Theaterroom gabadaya ta yi office dinta nurse Zainab na bin bayanta. Daukan wayanta ta yi akan Table  amma ya kubce zai fadi da sauri Zainab ta tare ta ce" Dr wa za a kira miki". 

Cikin kuka ta ce "Dr Husaina ko Dr Hafsa". 


Zainab ta yi saurin danna K'iran  Dr Husaina yana fara ringing ba jimawa ta dauka tana jin an dauka ta karawa kunne Fanna. Dr Fanna cikin kuka tace "Dr ki yi saurin zuwa ceton rai Dan Allah ki hanzarta".

Daga can bangari ta ce "subbahanallah Dr Fanna ya aka yi?".

"Dr Husaina ba lokaci kawai ki kamo hanya na shiga cs amma na kasa na fito".

"Ok gani nan ma ina  B Ward  na zo duba wani patient ɗina. 

 Ta kashe wayan  ko minta daya ba a yi ba ta fado office din da saurinta. 


Fanna ta ce "ga Zainab ku tafi sauran nursing din suna ciki. Husaina ba ta tsaya b'ata lokacin ba ta fita Zainab ta bi bayanta, Dr Fanna ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take a cikin office daga karshe ma bakin  Theaterroom din ta je inda yan'uwan Alhaji  Abdulsamad suke amma duk ta fisu fita hayyaci  shiko Alhaji Abdulsamad tunda ya tsugunna ya maida kansa k'asa bai sake d'agowa ba.

 Ba a fi mintuna 30 ba wata nursin ta bito da yaron  a hannu da sauri Aisha  ta mek'e tana k'arasowa inda take tana mek'a hannu girgiza mata kai nurse din tayi tace "Uwar yaron tun kafin a fara mata aiki ta ce idan muka ciro mu ba wa Dr Fanna." 

Duk suka bita da kallon mamaki nursing ta yi inda Dr Fanna take a tsaye kamar an dasa ta  ta mek'a mata yaron tayi Dr Fanna jiki na  rawa ta karbi yaron tana cewa 

"Ita uwar yaron fa yatake?" 

Shiru nursing din tayi tana sa hannu cikin aljihunta taciro wani takaddu 

 "tace gashi tace a baki wannan, a ba wa mijinta wannan" 

 

Fanna ba ta karbi takardun ba tace "Na ce miki ya ita uwar yaron?"

Ajiyar zuciya nursing ta yi cikin harshe turanci ta ce

"ba zan iya cemiki lafiya ba dan gaskiya tayi bleeding sosai..."


Abdulsamad Bai bari ta k'arasa ba ya meke da sauri yana cewa "what!!!" Haɗe da yi hanyan theates room din a zabure, da sauri Alhaji Abdulraham da Abdulmajid suka kama shi cikin wani irin sanyin murya ya ce

"brother ku bar ni na shiga na ga halin da Halima take ciki idan na rasa ta za ku rasa ni bro Dan Allah ku barni kar su fito da ita su ce ta mutu idan nashiga  zance kar tamin haka na san tana Sona ba za ta tafi ta bar ni ba. Dan Allah ku bar ni. Da k'er suka ja shi suka fita da shi a falon wata babbar  mace wanda da gani ita ce mahaifiyar su Alhaji Abdulsamad Hajja ta meke tana cewa 

"Ke bani jikana na gan shi shi ne jikan fari magajin gida wannan nawa ne ko duka ne an ce ka dauki na fari" .

Ba ta sa hannu ta karbi yaron a hannu Dr Fanna da ba ta san ma tanayi ba ciki wani iri gudu ta fad'a d'akin theater din  har sun gama dinkin amma suna tsaye a kanta nauran gwajin numfashi suke gyara mata amma ba alaman zai yi aiki a hankali Fanna ta karasa inda Halima take a kwance ta sa hannunta a bayan wuyanta tana laluman jijiyar bayan wuyan nata ta tsanya yatsunta biyu a daidai inda ta san za ta samu jijiyar wanda ko da mutum suma ya yi to za a samu wannan jijiyar tana harbawa idan ya daina to tabbas rai ya tafi ciki wani irin zafi ta cakumi Dr Husaina tana cewa "Why she didn't breathing?

Na ce me ya sa ba ta nunfashi?  Halima kar ki min haka me yasa za ki mutu ba tare da kin gayamin dalilin da yasa muka kamu da soyayyar juna lokaci k'ank'ani? Cikin watanni tara na san ki amma ina jin ki kamar wata ɓangare na rayuwata"

Sauran nursing din ne suka kama ta suka fita da ita tana tirjewa. 


Sosai family  3brothers suka ji rashin Halima dan yariyar kirki ce har hajja da ba wani damuwa tayi da ita ba ta ji rashi musamman ma oga  Abdulsamad ba karamin wahala a kasha ba kafin a samo kansa ya fara magana shi ma da kyar ake jin maganan nasa wanda yawanci ma idan ya ga Nasir jaririnsa yake yi. Dr Fanna kam kullum tana hanyar gidan idan za ta tafi wajen aiki sai ta biya ta gan shi, idan ta tashi sai ta biya kullum da kuka take fita tana so ta ce a ba ta yaron amma tasan bata isa ta fara ba saboda Hajja ta kasa ta tsare.


Gobe ne za a yi sadakar arba'in din Halima duk suna zaune a  babban falo akan dining table ana breakfast idon Hajja ne ya yi wani irin cikiwa da kwalla da ta d'aga kai ta kalli yaran nata Abdulmajid Abdulraham matan su zaune agefinsu sai Abdulsamad ne kawai shi kadai ba matarsa  tana tausaya masa  musamman idan ta tuna a rana daya ta haifesu sunyi karatu lokaci daya sunyi aure lokaci daya amma shi ga shi tasa matar ta  mutu, ta goge kwallan idonta ta sauke idonta akan Amina matar Abdulraham wanda ita ma ko yau ko gobe tasake kallon Aisha matar Abdulmajid ita ma da cikin wata biyar da dan kwanaki ahankali ta ce "Allah Ya raba ku lafiya shi ne fatana Allah Ya raya min NASURUDDEEN".


Cikin sanyin murya suka ce Amin shiko Abdulsamad bai yi magana ba sai kawai ya kai hannu kan kujeran gefinsa wanda wajen zaman Halima ne 

Hajja ta ce" kar ka damu Abdulsamad za a samu wacce za ta zauna a kai cikin kwanan nan".


Abdulmajid ya ce

"Hajja ai ansamu ma ya kamata ya cika wa matarsa alk'awarin ya auri zabin da ta masa Dr Fanna tana da kirki sosai".



Hajja ta ce" sosai na yaba da hankalinta ganin har yanzu bai samu nusuwa ba ne ya sa ban matsa masa a kan maganarta ba, kyanta a ce an haɗa daurin auren da arba'in din Halima  amma Abdulsamad don Allah a yau nake son idan Dr Fanna ta zo kamata magana  ya dace ta fada mana garinsu da inda iyayenta suke mu je neman aurenta nide iya bincikena an tabbatar min da cewa aikine ya kawota ba a nan take ba na san de ba zai wuce a ce yar maiduguri bace tunda ga zanen barebari a fuskarta kuma sunanta  ma na barebari ne za ta kasance yar maiduguri ko yobe ".


 Cikin sanyin murya Abdulsamad ya ce "Hajja da wuri haka ni fa ko maganan ban mata ba a dan ba ni lokaci".

Hajja ta ce

"Ba lokacin da zan ba ka inason ka samu wacce za ta rage maka damuwa kuma na san Dr Fanna wayayyiyar mace ce za ta yi saurin mantar da kai ko m...... "


Ba ta karashe maganar tata ba gani wani irin gumin da Amina matar Abdulraham take tsatssaɓowa, ganin yadda ta tsorata ta tsaya da maganan ya sa duk suka kalli inda take kallo da sauri Abdulraham ya ce "ya de Amina a hankali ta da fashi tare da sauka akan jujeran ta sunkuya k'asa tana ta faman yarfa hannu daidai lokacin Dr Fanna ta shigo tun kafin ta k'arasa ta san halin da ake ciki da sauri ta koma mota ta sako safan hannu tana tafe tana sanya ta har ta karaso tana duba ta ta ga ai kan d'a ne ma yake kokarin fasowa ta kalli mazan da duk sukayi wani cirko-cirko ta ce "Don Allah ku ba mu waje" ko suna ba su ma kai ga ficewa gabadaya ba suka ji kukan yaron a tare suka juyo suka yi murmushi tare da dafa kafadun juna suka fice haifuwa ya zowa Amina da sauki sosai duk da tun dare take abunta amma dayake macce ce mai dauriya da jaruta Koda Abdulraham ya gane cewa ta yi ba wani abu dama ance ana jin haka idan ciki ya tsufa cikin k'ank'ani lokacin Dr Fanna ta gyara Amina da zankadeden jaririnta.  Zo ka ga murna a wajen Hajja da yaranta, Nasir ya samu aboki ranan suna yaro ya ci sunan Baban su Abdulsamad  Muhammad  amma Hajja tace amasa al'kunya da Araf  washe garin sunan Araf Hajja ta sake bawa Abdulsamad umarni da babban murya akan yayi wa Dr Fanna magana. Bai yi musu ba bayan zuwanta sai  da ta zo fita ya tashi ya bi bayanta Sai da tashiga mota yace "Dr idan ba damuwa in shigo ina son magana dake".


Kallon sa ta yi cikin tausayinsa za ta fito ta ga ya shiga shi ma rufo kofar bangarensa ya yi ita ma ta rufo nata sai da ya ja wasu dak'iku yaja numfashi yace "kin samu daman karanta wasik'ar Halima".

ta ce"E.  Duk a kan jaddada alk'awarinta ne da kuma in rik'e mata kai da Nasir da mahaifinta amana".


Yace "ni ma nawa akan hakan ne to ya kiga". 

Ta numfasa cikin sanyin murya ta ce "Gaskiya daga b'angarena akwai matsala ina tsoron yanayin mahaifiyarku gani nake kamar ba za ta yarda ka auri y'ar gidan christian ba ".

A firgice ya kalleta yace what Christin  kuma ke din dama a kanuri akwai arna". 

girgiza masa kai tayi ta ce 

"Ni ba kanuri ba ce kamar yanda mutane suke dauka bace nagaji da bawa mutane amsa  a a a ne yasa nabari a ni kanuri ce har naje nayi University  dina a garin maiduguri dan na koyi irin yaren dan ance a can suke na gaji da jayayya da mutane akwai sanda ina yar  secondary a logos wani malaminmu dan kanuri har marina yayi wai ina boye yarena tun daga ranan na bincika ina ne wannan k'abilan ta kanuri suka fi yawa zan je na iya yarensu dan tun ina yarinya na gaji da wannan tambaya da mutane suke min".


Dakatar da ita ya yi yana cewa " kin gane duk wannan bayanan naki bana ganesu sai kin bani labarinki ko zan tsinci wani abu ina cikin firgice Fanna jin ke ba kanuri ba ce". 


Wacece Fanna?

" sunana Fanna emeka ni y'ar  k'abila ibo ce a cikin garin Legos a anguwar pester na samu kaina sunan mahaifiya ta emeka  dalilin zuwana nan arewa bayan gama secondary naga wani da irin zanena shi ne nayi ta nace masa har na san masaukinsa ashe irin ciranin nan ya zo shi dan maiduguri ne wasa-wasa muka kulla soyayya da Sharif  ba tare da sanin momyna ba ina kokarin boye mata ne saboda ta tsani  musulmai kuma tun ban gama sanin kaina ba momy take koyamin ak'idan k'in musulumci kullum gargadinta da nasihartta akan na guji musulmai duk inda suke momy duk inda taga musulmi sai ta zage shi ta ce mana amma sai ga shi nayi saurayi musulmai a dare daya muka yanke shawaran mu gudu da Sharif zuwa  garin su maiduguri  iya takardun secondary da primary dinna kawai na dauka muka kamo hanya Sharif shi ma yaji tsoron nuna ni ga mahaifansa, dan haka ya nemi gidan haya ya sani ya kuma nema min makaranta kasancewar takadduna sunyi kyau sosai ba a sha wahaln sama min gurbin karatu a jami'ar ta maiduguri ba shekara bakwai na zama cikekkiyar likita duk da kananun shekaruna a lokacin muka shirya aure da Sharif dan yasamu rufin asiri sosai ya bude shagon kansa a Lagos shi ya gina min wannan gidan da kaga Ina ciki a anguwar sardauna crystal  muyi dashi zamu yi auren a boye har mutara yara lokacinda iyayensa ba za su iya cewa ba sa sona ba shi ne dalilinsa na nema min aiki anan zuwan mu kano dan ya tsara a nan zai ajiyeni yas ha fama sosai kafin yasama min aki anan malam aminu kano Iya  abinda nasani kenan a tarishina ban taba sanin ina mahaifina ko danginsa ba dan duk sanda nayi gigin tambayar momy emeka Ina Babana to zanci na jaki kuma za ta yi sati bata ba ni abinci ba da kudin makaranta kwata-kwata ba ta bani daman in san waye ubana ba sai de kuma ina wayo Ina gane duk yanda akayi ubana musulmine kuma dan yaren kanuri shi ne yamin wannan zanen da kuma sunan kanuri duk yanda aka yi akwai wani abu me girma da shiga tsakanin su shi ne ta tsane sa."


Abdulsamad yace "baki gayamin ya matsayin ki a adini ba ko kin karbi musulumci".


Ta yi murmushi ta ce "Ai tun a Lagos Sharif ya sa na karbi musulumci ka san duk wani tarbiyar da iyaye zasu bawa yarinya idan ba ayi sa a ba cikin second k'adan soyayya yake rushe shi muna zuwa maiduguri yasani islamiya ta matan aure".


Abdulsamad yace to yanzu ina shi  Sharif din".

ta sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu ta gode hawayen da yadade yana kwaranya a fuskan ta

tace" Sharif yayi hasarin mota alokacin da muke tsaka da shirye shiyen auren mu saura kwana biyar a hanyar sa ta dawowa daga Lagos". 

ta k'arashe maganan cikin fashewa da kuka sai da ya bari ta yi iya yinta dan shi ma kukan zucin yake na rashin matar sa sai da suka dauki tsawon lokaci cikin sanyin murya yace sorry Dr Fanna namiki alk'awarin za ki same ni fiye da Sharif a rayuwa ke din zabin Halima ce zan iya sadaukar da komai a kan zabinta musamman tunda kika nuna min kina son Nasir kin gama min komai a rayuwa ni sunana Abdulsamad kamar yanda kika gan mu, mu yan ukku ne yan'uwana Abdulmajid Abdulraham.



Asalinmu iyayena duk 'yan nan kano ne a sani yan kofar na'isa amma Hajja wato mahaifiyata tana da dangin mahaifiya a Dardum wani k'wauye a jahar zamfara iya mu ukku nan suka haifa shakara daya da  auren su Allah basu mu yara ukku maza a lokaci daya daga kanmu kuma ba ta Kara ba ni Abdulsamad, Abdulraham, Abdulmajid.


Mahaifinmu malam Haruna baza a kira shi me kudi ba sai rufin asiri dan sana ar dinkin maza kawai yakeyi ni Allah yamin nasibin tun ina shekara 9 nake bin Hamza wani abokina shagon Babansa  muna taya shi auna kayan masarufi  alokacin muna  primary ne Allah yayi wa Baban Hamza rasuwa kasancewan suna da yan uba suka raba gado daga nan kasuwa ta rushe adan kudin da nake Tarawa awajen Hajja na ce tabani na sari kayan aleyoyin na yara idan nazo daga makaranta zan dinga  kasawa a kofar gida  hakan ko akayi Allah Ya sawa abin da na fara kamar wasa albarka har kofar gidanmu  ya zama matattaran tara  yara saboda ina da fara'a da saurin sabo tun ina bazawa a barantin Hajja har Baba yasa aka bugamin yar benci ina bazawa tun a lokacin ko ina a jikin bencin na rubuta 

3brothers ajiki wanda yanzu haka shine  3brothers company a fadin duniya ni kasuwancin bai barni nayi karatu me zurfi ba amma kinga yan uwa na sunyi Abdulraham Lecturer a B. U. K.



Abdulmajid kuma alk'ali abin da yasa zan  gaya miki dukiyar gidan mu nawa ne saboda shi sha'anin aure ba a boye-boye na san zama ya yi zama zaki gane to ina son na sheda miki yan'uwana suna da mahimmanci a wajenana  kuma sun fiye min komai a rayuwa ba na son ki dauki kanki amatsayi kin fi matansu ki dauka duk kanku ɗaya idan Allah Ya yi aurenmu da ke."


Ta ce "in Sha Allah amma ba ka karasamin ba ya akayi kayi kudi me yawa a cikin k'ananun shekarun naka Wanda har yanzu bazaka wuce shekara talatin ba amma duk  Nigeria ba wanda bai san 3.brothers ba". 


Murmushi ya yi ya ce "Akwai wani lokaci a lokacin ba zamu wuce shekaru sha bakwai ba, na raka Hamza abokina garin su innarsa kauyen  zamfara mun dan fita bayan kari guraren tarihi na ji nayi tuntube da wani abu kamar dusi haka ya dan dulloko da nakalli dutsin sai naga yana shek'i kuma shi ba fari ba shi ba ja ba na tsugunna na bara tonoshi ina mamakin yanda yake shek'i  kuma gashi da girma amma a cikin k'asa yake har Hamza da Yakubu suka zo suka karaso Hamza yace 'yade A.3full kake tonan k'asa haka".?


nace ''wllh Hamza wani dutse ne abin sha'awa kunga shi".


Yahaya dayake dan garin ne wani irin zabura yayi yace " kunsan meye wannan kuwa gol nefa ance yanzu sama da shekara 20 ba wanda ya tsinta nima a hoto nagani tabbas wannan shine kuma wllh gomnati ne za su kwace".

Na ce wllh ba zai yuwu ba ni zan tona kayana kuma naje na saida ba wani gomnati da zan bawa ni Allah Ya bawa. 


Yahaya ya ce ta yaya? Ina ka san ana sayar da shi wllh kwacewa za suyi su dan baka wani abu ai harmu ma munyi arzik'i tunda ai za a dan ba mu.

Na ce ka san Allah ba wani wanda zan bawa ya min wayo saidawa zan yi mu raba kudin  ku tayani tono shi  mun sha wahala dama da buhu a wajen mu za mu zuba goruba wanda zamuyi saraba da shi bamu ciko goruba ba muka sinto gol. Yahaya ya ce kai amma kai Abdulsamad kana da sa'a ka san yanda mutare suka hawalan neman wannan sama da shekaru amma kai ka samu nima na sheda wajen ko zai sake tsurowa".


da kyar suka dauramin a ka ban ma koma cikin gari ba suka rakoni tasha ba wani wanda ya kawo wai gol ne a buhuna haka har na samu motan kano su kuma suka koma cikin gari  na musu alk'awarin idan na saida zan raba kashi biyu na basu daya 

 ina zuwa nayiwa su baba da brother bayani Baba yace kar mu gayawa kowa kafin a san abin yi muka cusashi k'ark'ashin gadon Hajja 

amma da safe danaje shagon me alewa na  wanda nake sari nasan yana da amana kawai naji zuciya ta ta  aminta dana gaya masa ina gaya masa yace" to kar ka sake gayawa kowa a take yabarwa yaran sa jiran shago  muka shiga motarsa mukaje sabon gari  wajen wani abokinsa yana zuwa Dubai sarin gol  ya masa bayani da farko bai yarda ba sai da oga Kabiru  yayi da gaske alh sa'idu mai gol yace mu je ya gani ai ya san danyen gol da yana da hotonsa ma amma yanzu ya rasa muna zuwa gida Baba bai tafi shagon dinki ba saboda ba ya dan jin dadi brother suna makaranta dan alokacin suna level one 100 da ganin yanda Hajja da Baba suke harara na na san basu so na zo musu da mutane nide dama haka Allah ya yi ni da wutan ciki inde a gun kudi ne Alhaji sa'idu da oga Kabiru  sun gaisa da baba san nan suka masa bayanin abin da suka zo gani Baba yace" na dauko dak'er na mirgino shi dan sai a sannan naji nauyinsa nake ta mamakin meyasa jiya ban ji wannan nauyin ba abakin kofa na barshi Alh Sa'idu  ya tashi yazo ya gani wani irin ja da baya yayi yana rufe bakin sa yana salati sai da yagama mamakin sa ya zauna yana fitar dashi na temaka masa muka fitar yace malam Haruna wannan fa ba karamin abu bane anya zamu iya fitar dashi a k'asan nan kuwa?." 

Baba yace "to yaza ayi kenan".?

shiru alh sa'idu yayi can yace "shikenan bari na kira wani balarabe abokin kasuwancina a Dubai yabamu shawaran yanda za ayi atake yafito da wayarsa ya kira shi yace shima abokin nashi yace to bari yakira wani uban gidansa me company  k'era gol yana kiransa bayan ya kashe wayan  ba jimawa aka kira wayan Abdallah ne daga Dubai yace sun gama magana da uban gidansa gobe zasubi jirgin India sabo anan ne kadai yake da register  na bita da danyen gol ta India idan yashigo na Nigeria zai iyacewa da abinsa yashigo bawanda zai tuhumeshi hakan ko akayi bayan kwana biyu sai gashi 

shi ma da yagani  tsora yayi da girman gol din musamman ma da fari ya fi yawa atake yayi mana bayani ai wannan dukiyar zai sayi campanyn  sama gaba daya bashi da kudin da zai iya sayan sa amma idan mun yarda tunda yana da company sarrafawa  sai asarrafa in yaso  sai mu ba shi ladan sa mu saida kayan mu ladan da zamu ba shi ma ya isa ya K'ara k'arfin jari shima  kasancewar da turanci yake maganan sai da yagama nayiwa Baba bayani yace ba damuwa Allah ya sa me albarka ne 

bayan su Abdallah sun koma masaukin su a dare Baba yamin nasiha sosai ashe wasiya yake min bayan mun gama cin abinci ya ce 


"Abdulsamad ina son magana dakai  Abdulsamad duk da kai da yan uwan ka  rana daya aka haifeku amma karigasu zuwa duniya dan kai anan gida aka haifeka su kuma ya gagara muka je asbiti shiyasa nake cewa kaine BABBAN GIDA kuma alama ne da Allah ya nuna kai ne jagoran su 

 to ina son kayi hakuri da yan uwan ka kamakar yanda na sanka kar ka canza wannan daukaka da Allah yake shirin yi maka na mallakan dukiya kar yasa ka dauki kan ka daban dasu ka rike zumunci ku kamar yanda kasaba tun kana yaro ka sadaukar da naka karatun kake nemaka  kawo musu sun shiga  karatun kai kuma gashi baka shiga ba 

karike zumunci kar abin duniya ya rudaka ka canza daga Abdulsamad dina me sadaukar da farin cikin sa akan na yan uwan sa Allah yasa albarka cikin rayuwar ku."


nace" Amin  Baba in sha Allah zaka sameni fiye da yanda kafada."

Baba yace" nasani Abdulsamad ba kai nake jiba sherin macce nake tsoro matar da zaka aura ni a son samu nama ka auri Halima itace zatafi dacewa da rayuwan ka" .

 na juya na kalli Halima da take wanke wanke a kusa damu wanda alokacin bazata wuce shekara 10 ko 9 ba 

nace "Baba Halima kuma." 

yace"eh ita ina tusayawa yarinyar bata da kowa sai mu kaga Baban ta har yanzu bai dawo hankalin sa ba kai nake son ka auri y'ar nan kariketa amana na yarda dakai Halima tarbiyar muce nasan zata dace da kai ".

cikin kunya nace amma Baba kaman  tayi min yarinta nifa nan da shekara 3 zanyi aure kaga lokacin nacika shekara 20 kenan".

Murmushi yayi yace"kabari nan da shekaru ukku kagani idan zata ma yarintan amma na nemi alfarman karin shikara 2 kaga ta isa aure a wannan lokaci". 

nima murmushi nayi nace "to Baba na gode".


A washegari muka kama hanyan Dubai nida Abdallah da ogan sa Albaty da kuma alh sa'idu mun isa  lafiya ba jimawa aka fara aikin sarrafa gold  wanda ya yi matukar ba da mamaki dan farin diamond  din da yafita ciki me daraja ne wanda a lokacin anci shekaru ba a samu irinsa ba kuma kinsan turawa da larabawa da shi suka amfani ana bugawa a jarida ba jimawa yan sari daga k'asashe da dama suka fara rububin companyn dinmun samu riba fiye da zaton mu, wanda yanzu tun muna hade da Albaity yanzu mun raba kuma Allah da ikon sa nawa company shine akan gaba bayan company na babba  na bubai  ina da reshe a

 America  ina da reshe a Englan ina da reshe a saudia a an Nigeria ne nake jin tsoron budewa amma ni na aikin gina babban companyn k'era mota mashin da yawanci kayan da akeyin sa da k'arfe 

Dr Fanna nayi mamakin yanda dukiya ta yake ta hayayyafa agareni kinji yanda akayi nayi yaro yayi kudi kinji  tarishi na kenan a tak'aice".


Murmushi ta yi ta ce" saura abu biyu ne ban sani ba yanda aka yi Halima ta zo gidan ku da mutuwar Baba".


Sai da yayi shiru na yan second yace " Dr tun zuwana na daga Dubai na farko ban samu Baba ba sai tarin wasiyoyinsa duk wannan dukiyar Baba bai san dashi ba, ita  kuma Halima ai inaji ta gaya miki da bakinta hatsari mota sukayi da babatan wanda yayi loosing memory akwai wani Alh Musa a tsohon anguwarmu kofar na'isa a gabansa suka yi hatsarin mutum ne me tausayi komai da shi akayi na ceton ransu Alh Musa  ya kashe kudi sosai akan Halima dan  saida aka canza mata fuska alokacin baza ta wuce shekara 2 a duniya ba shiko Babanta aka ce zai warke ahankali dalilin dawowar Halima gidanmu mutuwar Alh musa ne wanda wasu mutane da ba a san su waye bane suka dirka gidan sa suka kashe shi shida matarsa  bayan sadakan bakwai yan'uwansa suka zo suka koro Baban Halima da Halima da alokaci bata wuce shekara 5 ba waje suka ja gidan suka rufe shi Baban a nan kofar gidan ya zauna ita kuma Halima dama tana shigowa wajen Hajja da yake Hajja bata da ya macce tana son y'ay'a mata shiyasa ta jata sosai ajiki ta tasa ba tana shigowa shine da aka korosu  ta shigo  gidanmu tana cewa Hajja ai wasu mutane sun rufe musu gida Hajja tana jin haka ta san yan uwan Alhaji Musa ne shiga d'akin Baba ta yi ta gaya masa Baba ya je ya sanar da Mai anguwa aka zo daukan Halima da Babanta  Hajja ta ce ita zata rike Halima har sanda tunanin babanta zai dawo haka ko aka yi  Mai anguwa yawuce da Babanta ita kuma Halima ta zama yar Hajja". 


Dr Fanna tace "Allah sarki Allah ya jikan Halima ya raya Nasir yanzu ina shi Baban nata".? 


Abdulmajid yace"yana nan acikin gidanmu dama da zamu taso Hajja tace mutaso dashi yana part din sa damasu kula dashi".

Dr Fanna kallon agogon hannuta tayi tace "to Alhaji zan wuce sai da yamma a kula min da yarona kar ganin sabon yaro adena yayin nawa dan naga Hajja sai doki take" 

Murmushi yayi yace"keko ba dole tayi doki ba saifa yanzu aka mana k'anne Allah ya sa Aishan Abdulmajid mata haifi namiji kin ga 

3 brothers ya samu kenan, 

sai ke kuma idan kika tashi kifara da macce sai ku sake Haifa mana mata masu kai daya  to ya zaki aureni?

 zaki zauna da yan uwa na zuciya daya?


Murmushi Dr Fanna yayi tace "wacce macce 3 brother's zai yiwa tayin aure taki Koda na wuni daya ne amma kasa a ranka wllh ba kudin ka nake soba wasiya Halima ne da kuma son ka da yamin shigan ba zata dan tun rasa Sharif ban yi zaton zan samu wanda zan so kamar shi ba sai gashi harma fiye dashi Allah yasa kai kamin ko da rabin s....... 

Sai kuma tayi shiru tana mai da kanta daya gefen a hankali yatashi yafita a motan yana murmushi ya kama murfin motan zuciyar Dr Fanna sai bugawa yake adduar  nasara take ta karantowa ta ji kamar daga sama


 yace "zuciyar ABDUL tun yana yaro yake son auren yar barebari mai irin zanen ki me irin sanyin halinki me irin sanyin muryan ki amma nabi zabin Baba na auri Halima sai gashi a karo na biyu Allah Ya bani fiye da zabina gaskiya na san dalilin biyayya da umarni iyaye ne ya sa Allah yamin wannan babban kyautan amma ba wai dan na cancanta ba tun kallon farko dana miki naji kece matar mafarkina FATIMA ZAHRA kisa aranki Abdulsamad naki ne".


 Yana gama fadan hakan ya mata murmushin sa me tsada tare da kashe mata ido daya ya rufo kofan ya juya cikin takunsa na ingarma ya fara tafiya kasa rufe baki tayi wai ita Fanna emeka 3 brother's yake gayawa wannan kalaman anya ba mafarki take ba mutumin da saide taga sunansa ajikin gidajen Mai ko kwalin taliya ko muhun sugar omo shikafa dade  sauran su 3brother's dafe kirjinta tayi yanda yake bugawa kawai jira take taji ta farka daga baccin  da takeyi 


shi ma Abdulsamad yana shiga yayiwa Hajja da yan uwan sa bayanin wacece Fanna da farko Hajja ta nuna kamar bata gamsu da d'anta ya auri tubebbiya ba amma da taga yanayinsa ta gane yana sonta kuma ta tuna da asalin saurayin Fanna din Sharif  yanda yayi soyayya na shekaru da ita kuma suka shiya shirin aure batare da sanin iyayen saba shine ta tsorata kar shima Abdul yayi tunanin haka tunda yana da daman da zai ajiye mata dari gashi ba mazauni bane tsoron haka yasa ta amince ayi auren amma har ga Allah ba dan taso ba. 


A ranan suna jaririn Amina ya ci sunan Haruna Baban su  A'A'A Hajja zo kaga mu a gun hajja a take tace akirashi da Agrif Hajja tsohuwar  makaranciyar litatafan hausa ce dan haka tasan suna kala_kala dan har yanzu hajja karatun hausa novel takeyi har irin na online duk tasan marubuta shiyasa ko kallon  yaranta sukayi tasan me suke nufi ita take koya musu yanda zasuyi soyayya ma 


A ranan da Nasir  ya cika wata ukku a ranan aka daura auren Dr Fanna da Abdulsamad ba wani shagali akayi ba a washegarin ranan ne kuma Aisha matar Abdulmajid ta tashi da nak'usa  tasha wahala Dr Fanna tace amata cs amma Hajja da yan'uwan Aisha  suka hana wahala tayi wahala har suma Aisha takeyi sai da sukaga abin bazai yuwuba suka saka hannu aka turata d'akin theater  ansamu nasara ceto uwa da jaririta amma ansamu babbar matsala a mahaifarta wanda yariga ya fashe ba wani dama sai de a fitar dashi Allah saki Aisha kowa sai da tausaya  mata haifuwar fari a cire mahaifa kowa ya ji sai yace Allah sarki Allah yasa albarka arayuwan d'an data haifa. Ranan suna yaro ya ci sunan Muhammad Albaity ogan gidan Abdulsamad dan Hajja haka ta ce ba abin da za a saka wa albaity dashi sai de susaka masa me suna ana kiransa da Kamal


bayan warkewar Aisha gida ya koma yanda yake kowacce tana kula da nata ɗan yanda ya namata Fanna ta ajiye aiki saboda kula da d'anta da mijinta duk da yawanci bayanan yau yana can gobe yana can wani abin mamaki Nasir yana kara girma kaman  nisa da Dr Fanna yana bayyana abin yana bawa kowa tsoro dan Abdulsamad de b'aki ne ita ma marigayi Halima kak'ace sosai amma Fanna fara ce sosai irin sol din nan farin ibo din nan idon  sa hancinsa duk rin na Fanna ne kullum Hajja cewa take ikon Allah tsabar son da Fanna take yi wa Nasir ya sa har kamanninsu yana son ya zo daya in dai ba ido na ba ne wllh sak 


*Bayan shakara biyu*


Amina ta sake haifuwa wannan karon ma danta namiji sunnan Baban Hajja Habubakar sadik aka masa alkunya da AIBAN . AIBAN na da shakara biyu Amina tasake haifuwa shima namiji sunan Baban Amina   aka sa wato  Adamu ana  kiran shi Abbaty har wannan lokacin Fanna ko batan wata ba tayi ba tun abin baya damunta har ya fara damunta dan Hajja tafara k'ananun magan ganu 

tunda yaran suka fara wayo suka gane Nasir ya fita daban acikin su yana da wani irin zafin zuciya ga rashin tsoro da rashin kunya idan ba mommynsa ba 

ba wanda yake ragawa ba wanda ya isa da shi inde yana gu to sai de kome ayi yanda yake so dan shikara 6 amma tamkar dan shekaru 20 haka yake diler kowa a gidan iyayensa ma ba ya raga musu balle ma aikatan gidan hatta Hajja shayin sa take balle su Kamal da Agrif ko abu aka ba da baya wajen to ba za su dauka ba sai sun jira ya zo ya gama jan ajinsa ya d'auki nashi su d'auka 

har ga Allah Abdulsamad ba ya son halin d'an  nasa sai de ba shi da lokacin zama da shi wani halin nasa ma bai sansu ba tunda bai fiye zama a k'asan ba. Baba yabubu me gadi kam yaron tausayi yake bashi kuma bayan mommysa ba wanda yasan halin Nasir sai Hajja da yabubu me gadi. 


Yau ma kamar kullum sun taso daga islamiya duk kansu ukku kowa akan  kekensa a tare suke tuk'awa Bodyguard dinsu ne a gefensu sun sanya su a tsakiya Agrif kam wani fisari yake ji sosai tun a makaranta amma bai isa ya wuce Nasir a gaba ba dan ahankali suke tuk'awa kuma a tare ko ataku daya wani bai isa wuce wani ba har suka zo bakin get Baba Yakubu yana ganin sa yafara masa kirarin da yasa ba 

"A a barka da zuwa NASARA nasara ko gani kafi mutum NASARA me wuyar badanci Nasara goshin jirgi me wuyar karo kafe kekensa ya yi daidai inda Baba Yakubu yake Kamal ma yatsaya cak shida bodyguard din shi ko Agrif fisari ya gama matsansa dan haka da sauri ya masa kan keken alaman ya yi gaba cikin wani irin  tsawa Nasir yace 

"What Agrif".................


Ba Agrif da ya gama jika jikinsa da fitsarin b hatta bodyguard din da Baba yabubu sai da suka tsorata dan yanda yayi tsawan kaman ba yaro ba 




*To masoya mu je zuwa don ganin FURUCINA da wane salo yake tafe kar ku manta taku Batul mai baku kala ce*

Comments