Main menu

Pages

 


YADDA ZA A WANKE QODA (KIDNEY) CIKIN SAUKI BA TARE DAYIN DIALYSIS A ASIBITI BA!

A nemi Ganyen Yalo wato (Garden Egg Leaves), Sai a Dan wanke ganyen da Ruwa me kyau Sai a yayyankashi kanana-kanana


 Sai a zuba a tukunya me kyau tare da ruwa me kyau, Sai a dora a kan wuta tsawon mintuna goma.

Sai a tace a saisaitashi kaman shayi , idan ya Dan huce Sai a shanye cikin karamin Kofi daya. 

Bayan an shanye da Dan wasu awowi in aka ji fitsari a yi a fili ta yadda za a ga kalar

Fitsarin ya chanza tare da fitar da wasu cututtuka Daga Qoda (Kidney) Zuwa mara.

Me fama da Ciwon Qoda ya jarraba Wannan bayani Inshaa Allahu zai dace da waraka da yardar Allah! Me fama da ciwon Qoda yana iya yi kullum sau Biyu a rana har ya dace,

me son ya wanke Qodarsa kuma Sai ya dinga yi sau daya a kowacce rana Na tsawon sati daya.

Yah Allah ka bamu Lafiya da zaman lafiya, 



AMFANIN GANYEN 'DA'D'DOYA🌿 WATO GANYEN RAIHAN KO KUMA A TURANCE (SCENT LEAVES)🌿 DA YADDA AKE SARRAFA SHI🍵

(1) Yana narkan da abinci 

(2) Yana tsare mutum daga kamuwa da ciwon zuciya

(3) Yana rage tasirin Ciwon suga (diabetes)

(4) Yana rage radadin ciwo 

(5) Yana kashe bacteria da germs(qwayoyin cuta)

(6) Yana rage nikotin(nicotine)

(7) Yana tasirin wajen sanyi mai kama qabobi 

(8) Yana Amafani wajen mace mai Neman haihuwa Yana wanke mahaifa(boost fertility)

(9) Yana maganin sauro(fight mosquito)

(10) Yana taimakawa wajen mura da tari 



YADDA AKE SARRAFA GANYEN DADDOYA🌿

(1) Yadda ake amfani da dodoya  wajen narkar da abinci ana hadata da lemon grass adafa ariqa sha.

(2) Yadda ake Amfani da dodoya wajen magance kamuwa da ciwon zuciya zai ariqa dafata da danyen  citta anasha kaman tea 


(3) Yadda aka amfani da dodoya wajen ciwon suga diabetes Asami ganyen garahuni sai ahadasu adafa ariqasha Kofi daya da safe kafin aci abinci Kofi daya da yamma har sati uku


(4) Yadda ake amfani da dodoya wajen rage radadin ciwo Asami garin kanunfari Rabin cokali ahada da ganyen dodoya adafa ariqa sha


(5) Yadda ake amfani da dodoya wajen riga kafi kamuwa da cutar bacteria zaa sameta sai ariqa sawa cikin abinci ana dafawa.


(6) Yadda ake amfani daita wajen rage nicotine wannan yafi amfani ga mai shan taba ko mai cin goro ' ajajjagata ko ayi blending dinta tare da citta danye guda daya da bayan angama sai azuba zuma aciki asha


(7) Yadda ake amfani da dodoya wajen sanyi mai kama gabobi zaa sami dodoya da citta danye da lemun tsami da tafarnuwa da saiwar sanya sai adafa ariqa sha


(8) Yadda ake amfani dashi wajen mace mai Neman haihuwa Yana wanke dattin mahaifa zata sami dodoya da ganyen magarya ta dafa tariqasha " kuma anaso duk abincin dazata dafa ta tabbatar da tasa ganyen dodoya a ciki.


(9) Yadda ake amfani da dodoya wajen maganin sauro idan akayi hayaqinta yana Koran sauro 


(10) Yadda ake amfani da dodoya wajen maganin mura ana samun ganyen dodoya da citta danye sai adafa ariqa zuba Zuma anasha



*WASU DAGA CIKIN ANFANIN ALBABUNAJ* 

1. Yana magance matsalar hawan jini (high blood pressure)


2. Yana magance matsalar ciwon sugar (Diabetes)


3. Yana magance matsalar ciwon zuciya (heart problem)


4. Yana magance matsalar ciwon Ulcer da ciwon ciki


5. Yana magance matsalar Tari da Mura


6. Yana magance matsalar Damuwa da Magance matsalar barci (strees)


7. Yana magance matsalar Toshewar jini acikin jijiyoyin jikin mutum


8. Idan aka tafasashi aka wanke kai ko fuska, Yana magance duk matsalolin guraje ko makero daduk matsala ta Fata


9. Yana Sanya Fata (skin) tayi laushi dakuma kashe cuttuttukan dake jikin Fata (skin diseases)


10. Yana magance laulayin hakori na Yara jirajirai.


 *Yanda ake amfani dashi*


Ana tafasashi chokalinsa guda daya acikin ruwa, sai asanya masa Zuma chokali daya Asha safe da yamma


Idan Mansa ne, Ana shan baban chokalinsa daya safe da yamma.


والله تعالى أعلم.

Dan uwanku a Musulunci

Ahmad Muhammad Nata'ala



*AMFANIN KHAL-TUFFA (Apple cider veniger* )

1. Ana amfani da shi wajen wanke

gashi yana sa kyalli, yana qara ma jijiyoyin kai kwari yana sa gashi tsayi Yana kashe dandruff cikin kan kanin lokaci.


2. Yana narkar da tsakuwar koda.


3. Yana Maganin duk wani rauni da akaji cikin kankanin lokaci.


4. Yana maganin dattin haqora a dangwalo kadan a goge haqora da shi sai a kuskure dà ruwa.


5. Ana amfani da shi wajen goge hammata after shaving yana hana kuraje fitowa, yana sa haske.


6. Ana amfani da shi wajen rage kiba ko tumbi, ana zuba murfin kwalbar biyu a ruwa asha da sassafe da kuma sanda za'ayi Barci.


7. Shan khal tuffa na taimakawa wajen matsalan hawan jini.


8. Shan shi na taimakawa kwarai wajen rage yaduwar cutar yeast infections wadda tafi kama mata.


9. Masu fama da skin problems irinsu pimples, rashes, spot, acne etc a hada shi da man dalbejiya shafa a wajen.


10. Yana maganin matsalan rashin samun bacci Idan ana hadawa da Zuma anasha kafin bacci dakuma bayan farkawa daga bacci.


11. Yana maganin matsalolin mafitsara( bladder) kasa yin fitsarin kokuma jin zafi lokacin yinta masamman masu bladder infection.


12. Yana maganin ciwon ciki idan aka zuba murfi biyu a ruwa aka sha.


13. Yana maganin tari idan aka jajjaga Citta aka zuba ruwan khal tufah da zuma aka sha.

والله تعالى أعلم.


*_ME BUQATAN YA QARA, QIBA YANEMI KAYAN HADIN NAN, IN SHA ALLAHU ZA'A DACE_*

Assalamu alaikum warahamatullahi wabarkatuhu Macen da take neman qarin qiba ta nemi wadannan abubuwan.

.

1)- *kunun gyeda :- ki jiqa shinkafar ki ta tuwo, sannan ki soya gyeda sama sama, seki murje ta a turmi ki bakace*


 seki jiqa kamar zuwa minti goma seki tsiyaye ruwan ki saka citta da kanunfari acikin gyedar.


 Sannan ki wanke shinkafar ki itama ki saka citta, seki Kai a markada miki da ban da ban. Daga nan seki tace kowane daban, ki dora gyedar akan wuta taita dahuwa kina dan motsawa Idan ta dahu zaki ji ta dena gaafi,


 seki debi wannan kullun shinkafar ki dama ki zuba akai ki cigaba da *motsawa kamar minti biyar seki sauke, 


kisa lemun tsami yanda kike so, tunda harkar ta neman qiba ce seki sa madara da suga kisha in kika juri yi zaki qiba insha Allah.*


Sannan maimakon kisa kullun shinkafa zaki iya dama garin kunu na gero ki zuba acikin gyedar shima yanada dadi sosai, 


haka kuma zaki iya markada gyedar hade da shinkafa gaba daya, wato ba sekin raba ba*, amma na daban daban din yayi jin gyeda kuma yafi gardi.

.

2) *Ki samu waken suya ki wanke ya sha rana ki hada shi da ridi, da alkama seki kai a nuqa miki, ki tankade* ki riqa dama kunu dashi.

.

3) Ki kai a barza miki alkama seki tankade seki dora ruwa a wuta in yai zafi seki kawo wannan tsakin da kika tankade ki zuba akan wuta yaita dahuwa a hankali in kina so zaki iya saka gishiri kadan, idan ya dahu zakiga har yauqi yake kamar oats, *seki sa sugar ki sa madara.*

.

4) Yawaita cin abubuwan da suke dauke da fat, yana qara qiba, kamar su madara, milo, bournvita, ovaltine, blue band da sauran su.


*Abu na qarshe kwanciyar hankali yana sa mutum yai qiba in me jikin qibar ne. dan wata ko garinsu zata cinye bazatay qiba ba, saboda kowa da kalan halittan shi!!*


Sannan maza ma zasu iya amfani dashi ba sai lalle mata ba, *sannan wannan hadin ba iyaka jiki kadai yake qarawa ba, har niieman jikin dan adam yana qarowa da izinin ALLAH*


Comments