Main menu

Pages

KALA-KALAN GIRKE-GIRKE NA ZAMANI DON UWARGIDA DA AMARYA.

KUNUN GYADA MAI SHINKAFA

Ingredients1

1⃣Gyada

2⃣Shankafa

3⃣Tsamiya

4⃣Gasara

5⃣Sugar


    ~Yadda zakiyi~     

 Da farko zaki gyara gyadar ki,  ki soya ta sama sama saiki murje ta ki fitar da bayan saiki markada sannan ki tace


 shi saiki sami tukunya ki dora a wuta sai ta tafasa ki wanke shinkafa kamar rabin gwangwani ki zuba.


Idan ya dan fara nuna saiki zuba ruwan gyadar ya tafasa daman tsamiyarki ta juku sai ki kawo gasararki dai dai yanda idankika sa zai yi kauri ko ki dama ki zuba a cikin ruwan gyadarki


Saiki sauke kisaka sugar, asha dadi lpy



Lollipop dunkulalliyar doya Mai tsinke

Kayan aiki

doya

hanta

kwai

bushashshan bread

attarugu

albasa

tafarnuwa

gishiri

Mai

magi

Kori kadan


*Yadda ake hadawa*


Dafarko na feraye doyata, na wanke nasa gishi, saina Dora a wuta na barta ta dahu sosai


Sannan na tace na bari tadan huce saina kawo turmi na dakata Kamar zanyi yam boll, 


Amma wannan yafi laushi sosai sannan na kwashe nasa a mazibi mai kyau nakawo attarugu, albasa, Wanda na jajjaga na zuba nasa hanta ita na yayyankata kanana nasa magi, Kori, Sai na chakuda shi sosai ya hade jikinsa.


sannan na dunga curawa a hankali harna gama sannan na ajje agefe. Saina dora  mai, a wuta na fasa kwai, na dunga daukowa Ina sawa a  fulawa, sannan nasa a kwai nasa abushashshan bread. sai a sa cikin mai sai soyu.



YADDA AKEYIN TSIREN NAMA


Kayan hadi;

Tsokar nama

tarugu 

Magi

Curry

Spices

Fennel seed

Albasa

Tattasai

Koren tattasai

Tumatir

Garin yaji

Tafarnuwa domin bukata

Mai

Tsinken yin tsire Bama

 


YADDA AKE HADAWA


A sami nama me kyau gurin tsoka inda babu jijiya, sai a yayyanka shi madaidaita, a wanke shi tass a caccaka masa wuka sbd Idan anyi hadi ya ratsa ciki.


a tsane ruwan. Sannan a saka fennenl seed, a jajjaga tafarnuwa Idan ana bukata, curry, spices, garin citta, Maggie, bama, jajjagen tarugu da albasa kadan, da garin yaji shima kadan.


 Sai a jujjuya sosai har koina yaji sai a saka a fridge na tsawon awa 1 da rabi.


Sai a jika tsinken yin tsire a ruwa na mintuna 30 sannan a cire. A yayyanka albasa yankan manya, tattasai ma haka, 


tumatir da Koren tattasai duk ayi musu yankan manya, Sai a dauko tsinken a soka albasa, sannan nama, sannan Koren tattasai sannan nama sannan albasa sai tumatir, sai Jan tattasai haka za ayi tayi har a gama.


Sai a kunna abin gashi Idan ya yi zafi sai a dauko tsiran a jera sannan a yaryada mai akai sai a barshi ya gasu, a dunga juyawa akai akai sbd Kar ya kone.


Anayi ana yaryada mai har a gama. Za aji yana kamshi. Idan aka tabbatar ya gasu sai a cire a saka a kwano ko faranti. 


A ci da duminsa yafi dadi. Za a iya saka Wa a tsakiyar bread a ci. Shima akwai dadi.

             🥛🥛🥛


       BANANA PUDDING


Abubuwan hadawa



Ayaba 

Kwai 2

Lemun tsami 1

Suga

Filebo (flavour)


Yadda ake hadawa

Uwargida da farko za ki bare bawon ayabarki ki tsaga tsakiyan, ki cire bakin tsakiyan, 


sai ki yanka ki sa a blender.Sai ki fasa kwanki ki matse ruwan lemun tsaminki, sai ki kada sosai ya kadu,


 sai ki zuba shi a kan ayabarki.Ki zuba suga ki yi blending sai ki juyeshi ki sa flavor, ki juyashi sosai, 


sai ki sa a cikin oven ki sa wuta kadan dan, ya yi kamar minti biyu sai ki cire.Shike nan banana pudding na ki ya kammala.




Yadda ake hada lemun mangwaro (Mango Juice)


Abubuwan hadawa

Mangwaro 3

Sugar

Flavour

Lemon tsami 3


*Yadda ake hadawa*


Da farko za ki sami mangwaronki irin manyan nan. Sai ki wanke, ki fere, bayan kin yanka ki zuba a blanda ki markada, 


sannan ki juye a wani abu mai kyau.

Sai ki matse lemon ki a wani roba, ki tace har da mangwaron, ki zuba suganki da flavour sannan ki juya sosai, 


sai ki dandana, idan ya yi sai ki sa kankara ko kisa a frigde yayi sanyi asha dadi lafiya.




Yadda ake sarrafa dambun masara


A girke-girkenmu na gargajiya, a yau za mu koyi yadda ake sarrafa dambun masara.


Abubuwan hadawa

Tsakin Masara

Zogale

Attarugu

Albasa

Man gyada

Dakakkiyar gyada

Maggi

Kayan kanshi

Gishiri


*Yadda ake hadawa*


Da farko uwargida za ki wanke tsakin masaranki ya fita tas, sai ki tsameshi a mararaki. Idan ya tsane sai ki zuba ruwa a tukunya mai dan zurfi,anan sai ki sa marfi wanda zai rufe iya kan ruwan.


Sai ki dauko buhunki mai kyau ki zuba wannan tsakin, sannan ki sa a cikin tukunyarki, ki rufe ya turara.


Idan ya turara sai ki fito dashi ki juye a roba mai kyau, ki jajjaga attarugu ki zuba sai ki yanka albasa ki sa a ciki, ki sa maggi, da gishiri, da kayan kanshi, da gyada, da zogale, ki juyasu sosai.


Sai ki mayar cikin buhunki ki sa tukunya ya turara kamar minti ashirin, idan ya yi za ki ji yana kamshi.


Sai ki bude idan ya yi sai ki sauke, ki zubawa maigida da yara, ki sa man gyada da yaji. Na gode sosai. Sai mun sake haduwa a girki na gaba.

Comments