Main menu

Pages


JAN HANKALI AKAN SALLAR ASUBAH SALLAH ITACE MAFI ALKHAIRI FIYE DA BACCI. MU RAGE BACCCI DON MU RIBAN TA DA GOBEN MU


1. Bacci amsawr kiran Zuciyane.

Sallah kuwa amsawa kiran Ubangiji ne.


2. Shi Bacci mutuwane.

Sallah kuwa Rayuwace.


3. Shi Bacci hutune na Gangar jiki.

Sallah kuwa hutune na Ruhi.


4. Shi Bacci da Mumini da Kafiri duk suna yinsa.

Sallah kuwa Mumini ne kadai yake yinta.


Masu tashi lokacin hudowar Alfijir sun rabauta, Fuskarsu kuma ta haskaka Goshinsu kuma shima yayi haske da kyalli,


 Lokacinsu kuma yayi Albarka. Idan kana cikinsu to kagodewa Allah (s.w.t.) daya fifita ka, idan kuma baka cikinsu to Karoqi Allah (s.w.t) Ya sakaka acikinsu.


Menene yafi Alfijir kyau?

Farillarsa (Sallar Asuba) zata sakaka acikin kulawar Ubangiji da kariyarsa, 


Sunnarsa: (Raka'atainil Fajr) itace tafi Duniya da abinda yake cikinta.


Sallarsa (kamar yadda Malaman tafsiri suka fassara wannan aya ta 78 Suratul - Isra'i وقرآن الفجر ana nufin Sallar Asubahi).


Ita Sallar Asubahi Mala'iku masu duty safe da masu duty dare duka suna halartota. (Domin alokacin suke handing over na duty su acikin wannan Duniya tamu).


Ya kai Dan'uwa/Yar uwa Mai girma kasani cewa : Duk wanda yarayu akan wani aiki to akansa zai mutu, wanda kuma yamutu akan wani aiki to akansa za'a tashe shi.


Idan ka karanta wannan Saqo kuma kayi aiki dashi to kasami Ladan aikin ka idan kuma katurawa wasu suma sukayi aiki dashi to Ladanka zai nunku awurin Allah (s.w.t) In Allah yaso.


Kada kaboye Ilimi, Kabayyana shi zaka sami Kyakkyawan Sakamako.

Kuyi Murna yaku masu Sallar Asubahi acikin Lokacin ta kuma acikin Jam'i. Wallahu Aalam.



ZIKIRORIN SAFE DA YAMMA


Yin sakaci da Azkar din safe da Yamma kamar yin sakaci ne ka bar wata ƙofa da sharri ko cutarwa za su iya isowa gareka!


Ki/Ka yi Azkar din ka kuwa???


💠Ayatul kursiyyu (1).

💠Qul huwaLLahu Ahad (3×).

💠Qul a'udhu bi Rabbil falaq (3×).

💠Qul a'udhu bi Rabbin naas (3×).


💠Asbahnaa wa asbahal mulku Lillah (Idan da yamma ne kuma: Amsainaa wa amsal mulku Lillah), walhamdu Lillahi, laa ilaaha illaLLahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wahuwa alaa kulli shay'in k'adeer.


Rabbi as'aluka khaira maa fi hazal yaumi wa khaira maa ba'adahu, wa a'udhu bika min sharri ma fi hazal yaumi wa sharri maa ba'adahu (da yamma kuma: Rabbi as'aluka khaira ma fi hazihil lailah wa khairi ma ba'adahu, wa a'udhu bika min sharri ma fi hazihil lailati wa sharri ma ba'adahu), Rabbi a'udhu bika minal kasal, wa suu'il kibar, Rabbi a'udhu bika min azabin fin naari, wa azabin fil ƙabar.


💠Allahumma bika asbahna wa bika amsainaa, wa bika nahyaa, wa bika namuutu wa ilaaikan nushuur.

Idan kuma da Yamma ne:

Allahumma bika amsaina wa bika asbahnaa, wa bika nahyaa wabika namuutu wa ilaikal maseer.


💠Allahumma Anta Rabbiy laa ilaaha illa Anta, khalaƙtaniy wa ana abduka, wa ana alaa ahdika wa wa'dika mastaɗa'atu, a'udhu bika min sharri ma sana'atu, abuu'u laka bini'matika alayya, wa abuu'u bidhambiy fagfirliy fa'innahu laa yagfiruz dhunuba illa anta.


💠Allahumma inniy asbahtu (Idan kuma da yamma ne: Amsaitu) ushhiduka wa ushhidu hamalata Arshika, wa malaa'ikatika wa jamee'i khalƙika, annaka AntaLLaahu laa ilaaha illa Anta wahdaka laa shareeka laka, wa anna Muhammadan abduka wa rasuuluka.


💠Hasbiyallahu laa ilaaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa Rabbul Arshil azeem (Sau 7).


💠Allahumma inniy as'alukal afwa wal aafiyata fidduniya wal aakhirah, Allahumma inniy as'alukal afwa wal aafiyata fi deeniy wa dunyaya wa ahlee, wa maaliy, Allahummas-tur auraatiy, wa aamin rau'aatiy, Allahummah-fizniy min baini yadayya wa min khalfiy, wa an yameeniy, wa an shimaaliy, wa min fauqiy, wa a'udhu bi azmatika an ugtaala min tahtee.


💠Allahumma aalimal gaibi wash-shahaadati faɗiras-Samaawati wal Ardi, Rabba kulli shay'in wa maleekahu, Ashhadu an laa ilaaha illa Anta, a'udhu bika min sharri nafsiy, wa min sharrish-Shaydani wa shirkihi, wa an aƙtarifa ala nafsiy suu'an au a jurrahu ila muslim.


💠Bismillahil-laziy la yadurru ma'as-mihi shay'un fil Ardi wala fis-Sama'i, wa huwas-Samee'ul Aleem (3×).


💠Radeetu billahi Rabban, wa bil Islaami deenan, wa bi Muhammadin sallalahu alaihi wa sallama nabiyyan (3×)


💠Yaa Hayyu Yaa Ƙayyumu bi rahmatika astagithu, aslih li sha'niy kullahu wala Takilniy ila nafsiy ɗarfata ainin.


💠Asbahnaa wa asbahal  mulku Lillahi Rabbil aalameen (Idan kuma da yamma ne: Amsainaa wa amsal mulku Lillahi Rabbil aalameen), Allahumma inniy as'aluka khaira hazal yaumi: fat'hahu, wa nasrahu, wa nuurahu wa barakatahu, wa hudaahu, wa a'udhu bika min sharri maa fiyhi wa sharri maa ba'adahu.


💠Asbahnaa alaa fid'ratil  Islam, wa alaa kalimatil ikhlaas, wa alaa deeni Nabiyyinaa Muhammad SAW, wa alaa millati Abeenaa Ibraheema haneefan musliman wa maa kaana minal mushrikeen.


💠Subhaanallahi wa bi hamdihi (Sau ɗari/100)


💠Laa ilaaha illaLLahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa alaa kulli shay'in ƙadeer (Sau goma/10  ko kuma sau ɗaya/1 yayin kasala).


💠Laa ilaaha illaLLahu,  wahdahu laa shareeka lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa alaa kulli shay'in ƙadeer (Sau ɗari/100 da safe)


💠Subhanallahi, wa bi hamdihi adada khalƙihi, wa ridaa nafsihi, wa zinata Arshihi wa midaada kalimaatihi (Sau uku da safe)


💠Allahumma inniy as'aluka ilman naafi'an, wa rizƙan ɗayyiban, wa amalan mutak'abbalan (da safe).


💠Astagfirullaha wa a tuubu ilaihi (sau ɗari/100 a rana)


💠A'udhu bi kalimaatiLLahi taammaati, min sharri maa khalaƙ (Sau uku/3 da yamma).


💠Allahumma salli wa sallim alaa nabiyyinaa Muhammad (Sau goma/10).




ALJANNAR MASU GODIYA:

"Aljannah kala kala ce, kowa yana samun tasa ne abisa daidai gwargwadon irin imaninsa da kuma aikin sa, wani baya taɓa tarewa wani jin daɗinsa acikinta"

-

"Duk wanda ya yawaita godiyar Allah da kuma maida lamuransa zuwa gareshi, to haƙiƙa Allah zai azurta shi da gidan aljannah mai ɗauke da sunan masu godiya"

-

"Manzon Allah ﷺ, yace: idan ɗan bawa na ya rasu, sai Allah ya yace da mala'ikunsa; kun karɓi rayuwar ɗan bawa na, sai suce na'am, sai Allah yace dasu kun karɓi rayuwar sanyin idaniyarsa, sai suce na'am,


 sai Allah yace dasu to me bawa na yace, sai suce ya gode maka, kuma ya koma gareka (yace: Inna'lilLahi wa inna'ilayHi Raji'un), sai Allah yace dasu, to ku ginawa bawa na gida a aljannah kuma ku sanya masa suna gidan godiya"

جامع الترمذي (١٠٢١)

قال أبو عيسى هذا حديث حسن غريب.


Mu Dabi'antu da kyawawan dabi'u, don samun nasara Duniya da Lahira


SADAKA

Sadaka dalilice ga ingancin imanin mai fitar da ita daga cikin dukiyarsa da kuma samun tarin ladarh ranar gobe kiyama.



 KUNYA

Kunya babu abunda take haifarwa sai alkhairi annabin rahama ﷺ yace idan bakajin kunya tau ka yi duk abunda kaga dama.


 HAKURI

Hakuri kuma haske ne domin yanasa mai shi ya fita dg cikin duhun dimuwa dake ciki har ga kaishi ga harshen nasara. Allah yace kayi bushara ga masu hakuri. Kuma wani abun burgewa ga hakuri Allah ne da kansa yake tare da masu hakuri. Kuma cin nasara yana tare da masu hakuri.


TSARKI

Tsarki rabin imani ne domin shine rukunin ibadarh, idan babu tsarki babu ibadarh. Idan kuma babu ibadarh babu imani.



ALQUR'ANI

ALQUR'ANI hujja ce a gareka idan kayi aiki da abunda ya hore ka dashi kuma hujja ce akanka idan ka saba masa.



 SALLAAH

Sallah annuri ce domin tanasa mai ita ya shiryu saboda ayoyi da yake karantawa da tawali'un da yake cikinta.




Comments