Main menu

Pages

Malam Nata'ala Na Cikin Mawuyacin Halin da Yake Neman Agajin Mutane da Addu'arsu

 


Halin Da Malam Nata'ala Ke Ciki, da Irin Gudummuwar da Yake Nema Jama'a Suyi Masa.


Malam Mato na Mato da aka fi sani da Malam Nata'ala a cikin Shirin dadin kowa, ya tsinci kansa cikin wata jarabawar rayuwa ta rashin lafiya, inda Malamin yake bayani da irin halinsa yake ciki a yanzu na tsananin rashin lafiya.


Malam Nata'ala yace Yana fama da ciwon kansa ne inda tace duk bayan sati uku sai anyi masa allura ta N250,000, Wanda hakan ne ya sa yake neman jama'a da su takkafa masa da kudi da kuma addu'ar samun lafiya.



A cikin bayanin nasa dai yace a yanzu baya Jin dadin komai, Kuma kome yaci bayanin dadinsa a baki saboda tsananin da yake ciki. Inda yana cikin bayani ya fashe da kuka Yana Kuma neman gafarar mutane domin bai sani ba ko ya tashi ko ba ya tashi daga wannan jinya ba.


Ga cikakken bayanin ku saurara in akwai wanda yake da niyyar taimakawa to sai ya taimaka masa domin ya bayar da number wayarsa. Kuma ayi sharing mutane su gani ko za a samu wadanda zasu taimaka. Ga cikakken Video kamar haka;



You are now in the first article

Comments