Cikakken Bayanin Halacci ko Haramcin Shan Maltina Ga Musulmi.
Shahararren Malamin addini nan Sheikh Bin Usman yayi tunatarwa ko ince fadakar da musulmai wani abu da ba kowa ne ya tsaya ya lura da abin ba.
Sheikh yayi bayani ne akan Shan Maltina da kowa dai ya San cewa ba giya nace, to Ina matsalar take? Matsalar shine ita Maltina ana producing din ta ne daga kamfanin giya.
A cikin hukuncin haramcin giya kuwa tsinuwa da la'ana sun tabbata ne ba ga Mai Shanta kadai ba, A'a har da masu dakon ta da masu hidimarta da duk wani Abu da za ayi ya taimaka wajen damuwar ita giya din.
Matsalar anan ita ce, idan ka sayi maltina da kudinka don ka Sha to anan haramcin yazo, saboda ka bayar da kudinka a kamfanin giya, kaga kenan indirectly ka taimaki kamfanin tunda kudin ka za su shiga cikin kamfanin har su iya fadawa fannin da za ayi wani abu ta fannin giyar da kudin.
Amma idan baka Maltina akayi ko aka kawo maka to anan shnata halal ne domin kuwa ita a Karan kanta maltinar halal ce. Don haka ki yada wanna salon take ga musulmai don su daina jefa kudadensu zuwa ga kamfanin yin giya ta hanyar sayen Maltina.
Ga cikakken bayanin daga bakin Malam, Allah Ya sa mu gane mu Kuma kiyaye Ameen.
Comments
Post a Comment