Main menu

Pages

ABUBUWAN DA KE HADDASAWA MATA YIN TUMBI

 


Abubuwan da suke haddasa wa Mata yin Tumbi, da Abubuwan da zasu Kiyaye ci ko Sha don Maganceshi.


Akwai yanayin abinci da ruwan sha, haka zalika akwai yanayin mu'amala na yau da kullum dake saka mata su zama masu tumbi wannan zahiri ne domin binciken masana tuntuni ya tabatar da hakan wanda ko a darusan baya mun kawo makamantansu amma ayanzu zamuyi karin bayani dangane da wannan matsalar wanda kuma shawarwari ne ga Mace idan tabi insha Allahu ba ita ba zama me tumbi,


kafin ki kwanta barci kada kici kowanne irin abinci ana son sa'o,i biyu bayan cin abinci sannan ayi bacci, musamman abu me dumi anaso abawa jiki dama wannan abincin ya narke aciki kafin bacci, atakaice yawan cin abinci kafin bacci yana sakawa mace ta zama me tumbi,


Cin abu me sanyi bayan tashi daga barci, anaso mace kafin taci komai tasha abu me dumi, ba'aso asha abu me sanyi kamar lemo dayake da gas sosai ajikinsa abari sai bayan an dumama ciki da abu me dumi,


Yawan zama waje daya, anaso mace ta zama me yawan motsa jiki musamman matan aure anaso lokacin saduwa da miji mace ta zama me yawan motsa jikinta saboda anan jikinta yana mikewa yayi daidai, amma mace ta kwanta komai miji zaiyi yana saka jikin mace ya sake da wuri tarinka yin tumbi,


Yawan cin Abu me maiko musamman mata masu yawan zama waje daya yana kawo musu basir me kumbura ciki mace ta zama me tumbi kuma wanda bashida laushi, ga yawan tusa,


Domin rabuwa da tumbi kuma akwai wanda ake dafa lemon tsami bayan an yanyankashi sai atace ruwan asaka zuma anasha sau biyu a rana kafin a kwanta barci da kuma bayan an kwanta.


Wannan kuma za'a samu danyar kurkum da danyar citta a feresu duka sai a yanyankasu a zuba aruwa shima lemon tsami ayanka guda daya sai asamu kanunfari kadan da tafarnuwa, sai a dafa wannan ruwan anaso azuba ruwan yanda zaiyi kwana uku anasha shikenan bayan ya tafasa sai atace asaka zuma anasha sau biyu arana har zuwa kwana uku. Allah Ya sa a dace.

Comments