Cakwakiyar da ke Faruwa a Kannywood kan Zantukan Batancin da Rukayya Dawayya tayi akan Ummi Nuhu.
A satin da ya gabata ne dai Hadiza Aliyu Gabon, ta tattauna da tsohuwar Jaruma Ummi Nuhu, inda wannan fira ta ja hankalin mutane da yawa saboda firan ta taba zuciyar duk wani mai Imani sobada akwai tausayi sosai a ciki.
Bayyanar wannan fira kenan ta tsohuwar Jaruma Ummi Nuhu sai ga su Rukayya Dawayya da Saima Muhammad suka fito caaa kamar suna jira, maimakon su tausaya mata sai ma suka fito da wasu Zantuka marasa dadi akanta.
Wanda hakan bai dace ba ko me Ummu Nuhu tayi a baya ay a matsayinta na abokiyar aikinsu da sukai kasance a tare a Lokacin ya kamata ace sun Fadi abu Mai dadi akanta in Kuma ba zasu iya yin hakan ba to da sai su kame bakinsu su tsuke.
Ire - Iren wadanan mugayen halayen na wasu 'yan film na nuna hassada da bakin ciki da son ganin wani da cikinsu ya tozarta ne ke sa Allah ke kwashe Albarka a wannan masana'anta da ba ta da hadin Kai, da rufa ma junan su asiri abu kadan zai sami wani daga cikinsu sai su fito su toma mai asiri a bainan Nasi.
Ni a zato da tunanina sunyi hakan ne don in ma akwai Wanda ya tausaya ma Ummi har ya so ya taimaketa to wannan video da sukai a media sai ya kore tausayin a tunaninsu. Sun manta Allah Shine Mai yi.
Don haka taskar Al'ammah tana yiwa Ummu Nuhu jaje da yi mata fatan samun nasara da yayewar kunci da damuwar da take ciki, Kuma Ina rokon Allah dukkan bukatunta na alkhairi Allah Ya biya mata da dukkan musulmi baki daya.
Firan da sukai da Hadiza Gabon Allah Ya sa ya zama silar fitarta daga cikin kincin rayuwar da take. Masu hali irin na Rukayya Dawayya Kuma Allah Ya shiryesu su gane cewa su da suke cikin rufin asiri ba wayonsu bane, daga Allah ne.
Ga video maganganun da su Rukayya Dawayya sukai da Kuma martanin da mutane suka mayar masu. Sannan a wannan gabar dole nayi jinjina ga Rashida Abdullahi mai sa'a akan fadar Gaskiya da ta fito tayi. Sannan Ina fatan yan Kannywood zasu ringa koyi da ita.
Ga cikakken Video
Comments
Post a Comment