Ko kinsan tarin amfanin da Hulba ke dashi a rayuwar diya Mace, ta hanyoyi da Dama?
Yau inaso in yi wa mata ‘yan uwa karin haske akan hulba, mata dayawa na barnata kudi wajen gyaran fatarsu, Karin ni’imar su, gyaran gashinsu da kuma gyaran cikowar kirji.
To yanzu zan kawo muku yanda hulba ke gyara fatar jiki.
Gyaran Fuska
Zaki samu garin hulba ki dama da madara da zuma ya damu sosai sai ki shafa a fuskar ki, ki barshi kamar minti talatin kafin ki yi wanka, fuskar ki zata yi sheki zai kashe miki pimples ya gyara miki fuska kuma yana maida tsohuwa yarinya.
Gyaran Gashi
Wato shi gashi wani abu ne wanda ke matukar karawa mace kyau da kima shi yasa yake da kyau mu dinga gyara gashin kanmu akai akai wato kuma a duk abun gyara gashi ba kamar hulba.
Ga masu son gashin su ya yi tsawo da sheki zaki hada garin hulba coconut oil ki gauraya sosai sai ki shafa akanki ki barshi ya dade akalla kamar awa daya ko ma fiye da hakan, kuma zaki ringa yin hakan sau biyu a sati guda, sannan za kiyi na mako uku. Yana kara tsawon gashi, kuma gashin kanki zaiyi kyau da sheki, kuma yana hana karyewar gashi.
Ga masu amosani, wato dandruff, zaki hada hulba da apple cider ko ruwan khal ki shafa a kanki, da dare ki barshi har gari ya waye, ga baki daya amosani zasu mutu kuma gashin ki zai yi kyau.
Gyaran Cikowar Kirji
Babu kamar hulba yana gyara sosai kuma yasa kirjinki ya cicciko ya kara girma da kyau, wasu suna zuba garin hulba cikin abinci kullum sunaci don gyaran kirji in har abun ya zame masu jiki yana gyara sosai, kuma bayan cikar kirji ma yana warkar da cuttutuka da dama a jiki.
Haka kuma za a iya samun kindirmo mai kyau sai ku hada da hulba kuma sha yana aiki biyu ne farko gyaran kirji na biyu kuma sa ni’ima.
Ga wanda kirjin su ya kwan biyu suna iya hada garin sa da kindirmo, sannan su sami mansa suna shan spoon daya da safe daya da rana daya da yamma, bayan haka ma suna iya dafa garinsa su tace su sa tsumma su gasa kirjin su da shi sannan kuma su shafa wa kirjin man sa.
Magana ta karshe anan kuma abin fahimta, ba’aso mace mai juna biyu ta sha hulba domin yana kawo nakuda da gaggawa. Na biyu mata masu shayarwa suna iya hada garin hulban a cikin abincin su yana kara nagartaccen ruwan mama, kuma zai sa jinjiri ya kasance cikin koshin lafiya.
Comments
Post a Comment