Main menu

Pages

ABUBUWAN DA KE KAWO FITAR ISKA A GABAN MACE, DA YANDA ZA A MAGANCE MATSALAR



Abubuwan da suke Haddasa fitar iska a gaban Mace, da hanyoyin da za ta magance fitar iskan.


Budurwa ko Matar aure ko wacce tana iya fitar da wani sauti me hade da iska a gabanta musamman lokacin da kike tafiya ko kuma lokacin da ake saduwa dake kuma zakiji abun yana kama da Tusa to dai abinda yake jawota akwai rashin zama da wando (pant) ko yawo a tsakar gida ba takalmi da kuma zama a kasa yayin da mace ta haihu ko tana jinin al'ada. harda Shan abu mai sanyi yayin jinin biki ko al'ada ko kuma. kina Ware kafafunki yayin zama kodai yawan cin kifi ba tare da citta ba.

    A takaice dai wadannan sune kan gaba wajen jawo wannan matsalar.



 idan kina da wannan matsalar sai ki kiyaye abinda na fada a sama. Sannan anaso ki yawaita shan shayi mai citta idan kina da hali ki yawaita cin farfesu mai dauke da kayan yaji. sannan ki kiyaye wato ki yawaita cin citta, tafarnuwa, zuma tare da dabino suna da matukar amfani wajen sanya jikin mace yayi dumi.

 


    Dumin jikin Mace ya zama da dumi ba karamar ni'ima bace ga zamantakewar aure saboda haka ki kiyaye wanka da ruwan sanyi ko da a tsananin zafi ne ki rika dumamawa saboda ba fata ba kadai ruwan zafi yana da tasiri har ga cikin jiki. idan baki da ra'ayin jan lalle to ki rika tafasa lallen duk wata kina wanka da ruwan zai sama miki dumin jiki zaki rabu da wannan matsalar in sha Allah.



Ko ki nemi ganyen *magarya da bagaruwa,* da "ya" yan hulbah. Sai ki hadasu gu daya kina dafawa sai ki debi gishiri cikin tafin hannunki ki zuba ciki. Sai ki dinga shiga kina seatbirth da shi na tsawon 20 minutes.



 Sannan bayan kin tsane ki nemi farin muski sai ki dangwala da auduga me tsafta ki yi matsi da shi.



Akan iya amfani da ganyen *tumpapiya* Se asamu kaman guda 7 se adorashi akan garwashin wuta inyayi zafi se mace ta gasa gabanta dashi kuma ba'a bada tazara ana cire wannan anasa wannan haka har suqare. Haka har kwanaki 3 Insha Allah zata rabu dashi.

Ayi shere wasu su karu.

Comments