Main menu

Pages

 



Yanda Ake Miyar Ridi Musamman ga wannan watan na ramadan


Abubuwan da za a bukata

-Tattasai

-Albasa

-Attaruhu

-Ganye (Alayyahu ko Ugu)

-Nama da kifi

-Crayfish

-Manja

-Kayan kamshi

-Gishiri da maggi



Yanda za ki hada;

-Ki tafasa namanki ki tsame ki soya ki aje ruwan a gefe. Kifinki ma ki gyara ki dafa

-A zuba manja cikin tukunya ki kawo markadadden kayan miyarki wato attarugu, tattasai, albasa da kuma crayfish ki zuba a ciki ki soya sama sama



-Sai ki dauko ruwan tafashen ki zuba a ciki sannan ki zuba maggi da gishiri da kayan kamshi ki rufe ki barsa ya tafasa

-Sai ki dauko garin nikakken ridi wanda aka riga aka niko ta a injin nikan agushi ki yanka albasa ki yayyafa  ruwa  a ta murzata har sai ta kame tadan fara fitar da mai, sai a bude tukunyan ruwan miyan sai a zuba wannan ridin a cikinta



-Idan ya nuna sai ki kawo ganyen alayyahunki ko Ugu da kika wanke ki zuba ki barsa minti biyu ki sauke

-Zaa iya ci da tuwon shinkafa, sakwara ko semovita da duk wani nauin tuwo

Comments