Main menu

Pages

MUHIMMAN ABUBUWA GUDA 19 DA YA KAMATA MA'AURATA NAYI WA JUNANSU.

 



Hakkokin Zamantakewar Aure guda 19 da ya kamata Ma'aurata suna yiwa junansu, don dorewar zaman Lafiya da soyayya.


1. Soyayya ta gaskiya:

Dolene kayiwa matarka soyayya ta gaskiya haka kema dolene agareki, Domin sai da soyayyar gaskiya zaka iya kulawa da dukkan damuwarta, 

Itama saida soyayyar gaskiya zata iya biyayya ga mijinta.



2• Tsare Amana.

Wajibi ne Mace ta tsare amanar mijinta, tundaga jikinta da dukiyarsa dama duk wani sirrinta da nasa ta kula dasu.

Haka kaima wajibine ka tsare mata amanar dukkan gaɓɓanka kada ka nemi mata a waje, banda kallan mata a waje, banda kula mata inba wata larura mai ƙarfi ba.

Kakuma tsare mata sirrinta da duk wani abu daya shafeta.




3• Tausayawa juna.

Wajibine miji yarinƙa tausayawa matarsa, saboda ita mace mai rauni ce, ga ayyukan gida ga girki da sauransu.

Haka kema wajibine ki rinƙa tausayawa mijinki kada ki rinƙa ɗora masa nauye-nauye kizama mai haƙuri da iya abinda ALLAH ya azurtaku dashi.




4• Shige da fice.

Baya halatta mace ta rinƙa fita ba tareda iznin mijinta ba, koda leƙe ta window ko ta ƙofar gida haramun ne ga mace.

Haka kaikuma ka kiyaye dawowa akan lokaci saboda duk mace tanaso mijinta yadawo gida akan lokaci.




5• Kada tayi azumin Nafila saida izninsa, ssboda zai iya zuwa da buƙatarsa alhali kuma tana cikin azumi, to anan ana iya samun matsala, kodai a karya azumin kokuma shi yashiga takura.




6• Duk lokacin da mijinki yazo da buƙatarsa wajibi ne ki amsa masa, haka kaima wajibi ne idan tazo maka da buƙatarta ka amsa mata, domin ita sha'awa wata larurace mai ƙarfi, saidai idan matar tana cikin halin haila.




6• Wajibi ne mace ta saurari mjinta idan yana magana da ita, kadata rinƙa ja'injadashi da gardama.

Haka shima idan tana magana anaso ya nutsu ya saurareta yakuma yi mata magana cikin sanyin murya.




7• Kada mace ta rinƙa raina abinda mijinta yabata, haka kuma kada shima ya rinƙa raina kyautatawar da take masa.




8• Mace ta rinƙa ado da kwalli wa mijinta ta rinƙa ɗaukar kanta itafa amaryace a kullum tana zuba ado.

kaima ka rinƙa yi mata ado kana ƙamshi ka rinka zama kuma kuna hira acikin adon kace nayi wannan ne saboda ke, ku yawaitawa junanku yin hakan, kai ka rinƙa ɗaukar kanka a matsayin ango haka itama.




9• Mace ta rinƙa gaggawar bawa mijinta haƙuri a duk lokacin data yi masa laifi, shima kada yayi girman kai ya amsa mata,

Haka kuma idan yayi mata laifi shima ya rinƙa bata haƙuri hakan yana kawo soyayya mai ƙarfi da kuma zuri'ah mai kyau.




10• Mace ta zama mai kyakkyawan hali ga mijinta, kaima kazama mai kyawawan hali ga matarka.



11• Miji ya maida matarsa abokiyarsa, itama ta rinƙa abota da mijinta su rinƙa hirar soyayya akoda yaushe.



12• Miji ya rinƙa goyo matarsa idan itama zata iya ta rinƙa goya mijinta lokaci-lokaci.



13• A lokacin kwanciyar aure a rinƙa gabatar da wasanni wa juna, a ƙalla ayi wasa da juna kamar na 1hour, yadda sha'awar kowa zata motsa sosai, kuma dukkan jiki ya amsa.



14• Ka rinƙa yi mata murmushi a duk lokaci data kalleka, haka kema ki rinƙa masa murmushi a duk lokcin daya kalleki.



15• A duk lokacin da akai kwanciyar aure a rinƙa nunawa juna farin ciki da nuna jin daɗin juna, a kuma rinƙa kwanciya a jikin juna, kowa ya rinƙa nuna damuwarsa idan ɗaya baya jikinsa a yayin bacci.



16• Ki rinƙa yiwa mijinki addu'a a duk lokacin da kikai sallah, kina masa fatan alkhairi, 

kaima ka rinƙa yiwa matarka addu'a kana yi mata fatan Alkhairi aduk lokacin da kayi sallah.



17• Idan ka fita aiki ko kasuwa ka rinƙa kiranta kana jin muryarta kana kuma yi mata godiya da yadda take haƙurin zama a gida kana yaba mata.

Kema ki rinƙa kiransa kina gaisheshi kina masa fatan alkhairi, kina kwantar masa da hankali.



18• Idan mijinki yadawo ki tareshi da murna da farin ciki, ki kuma karɓi abinda ke hannunsa.

kaima kashigo kana mai murmushi da farin ciki kuma katari matarka kana mai nuna mata farin ciki.



19• Sannan miji ya rinƙa neman shawara a gurin matarsa, itama ta rinƙa shawara da mijinta akan wasu keɓantattun lamura.

Comments