Yanda Ake hada Sabulun wanki, don yin sana'a ko amfani a cikin gida.
Yau insha Allah Zamu koya maku yadda ake hada sabulun wanki Don sayarwa ko amfanin gida. Abubuwan da ake bukata su ne.
- Palm kanel oil 2 liter
- Caustic soda 1/4 kg
- Soda ash 1/4 kg
- Sodium sulphate 1/2 tin
- Slicate starch 1/8kg
- Colour orange
Yadda za a hada shine.
Da farko za a samu ruwa kar ya wuce liter 2. Sai a dauko caustic soda a jika shi da ruwannan Kashi 1 cikin 2 ma'ana a jikashi da liter 1 na ruwa Sai a dauko soda ash a jika ta da Kashi 2 cikin 3 na sauran 1 liter na ruwan.
Sannan Sai a dauko saura ragowar ruwan a jika sodium sulphate dashi.
Za a motsa kowanne a bashi tsawon minti 20 sannan Sai a dauko PKO Palm kanel oil.
A juye Palm kanel oil dn a babban mazubi Sai a motsa shi asa mashi kala yar kadan colour. A motsa sosai sannan Sai a juye ruwan caustic soda a ciki a motsa.
Sannan a juye ruwan soda ash a motsa. Sai a juye na sodium sulphate a motsa. Daga Nan Sai a juye slicate starch a motsa.
Daga Nan ai ta motsa shi tsawon wasu mintoci za a ga ya hade yayi kauri sosai to daga Nan Sai a juye shi a mazubi a barshi ya kwana Sai a yanka shi a barshi ya idasa bushewa shikenan an kammala.
Note; Dole ayi amfani da Safar hannu saboda rashin sabo da chemicals, sannan Kar abar Yara a kusa saboda hatsarin chemicals.
Wannan Yana da riba sosai alhamdullah mutane da dama sun gwada Kuma alhamdullah.
Don haka ga wadda take tunanin irin sana'ar da ya kamata tayi to ta gwada wannan.
Comments
Post a Comment