Main menu

Pages

YADDA AKE HADA ROOM FRESHENER KO AIR FRESHENER A GIDA

 Yanda Ake yin Room Freshner/Air Freshner domin sana'a ko amfani dasu a cikin gida.

Assalamu alaikum zanyi bayanin yanda ake hada ROOM FRESHNER, AIR FRESHNER. Turaren daki ko office. Kayan da ake bukata sune 

1. Ticner

2. Menthanol

3. Menthol

4. Perfume

5. Kala

Yanda ake hadawa shine. Idan kayan 500 ne tom zaki nemi ruwa liter 3. Saiki hade na 2 dana 3 dana 4 a waje daya. Ma'ana ki dauko jarka saiki juye menthanol daga nan saiki zazzage menthol daga nan saiki matse turaren saiki nemi marfi ki rufe su.
 Saiki dauko no. 1 wato ticner kada ki bari ta taba maki hannu kisa hand glove koda na asibiti ne saiki juye ruwa kimanin liter 2 a ciki ki motsa kwarai zaki ga yayi fari kamar paint saiki aje sa a gefe daya. Saiki dauko colour ki zuba kadan a container sannan ki juye sauran ruwan nan liter 1 daya rage.
Daga nan saiki dauko na jarkan nan wanda kika rufe wanda turare ke ciki saiki juye sa a cikin farin ruwan nan ki motsa sannan ki rinka zuba ruwan kala din nan kadan kadan kina motsawa. Daya hade saiki juye sa a cikin robobin da kika sayo. 
Ana saida dozen na roba omoge a naira 660 sai orobo 720 kuma akwai sticker duk dozen a 120. Allah ya bada sa'a yasa ku fara a sa'a. Wadanda suke yi kuma ya kara kawo kasuwa mai albarka. Ameen

Comments

1 comment
Post a Comment
  1. Your blog took to me a completely critical spot. It is a valuable and genuine article to upgrade information. Gratitude for sharing an article like this.Black panther air freshener

    ReplyDelete

Post a Comment