Main menu

Pages

YADDA AKE HADA OMO FARI KO BLUE DON SANA'A A CIKIN GIDA
Yanda Ake Hada Omo fari ko blue don yin sana'a ko amfani a cikin gida.

Insha Allah zan maku bayani akan yadda ake hada Omo fari ko blue Na wanki. Misali klin zip da sauran su.

Kayan da ake bukata wajen hadawar sune kamar haka.1. Texxafon

2. Soda Ash

3. salponic acid

4. Turare

idan kika tanadi wadannan kayan saiki fara kamar haka;1. Ki juye soda ash a cikin buhu bag mai girma sosai saiki motsa ta sosai

2. Saiki juye texxafon dinki ki sa icce ki motsa sosai sosai har sai kin tabbatar ya motsu.

3. Sannan saiki matse salphonic acid a ciki ki motsa sosai da iccen.

4. Sai a dauko Turare ki juye ki motsa sosai.
Saiki motsa ki girgiza sosai sannan saiki bude buhun ki juyeshi sannan ki warwatsa shi amma ki haka a cikin daki saboda kar iska ya masa yawa. Idan akai haka sai a bashi wasu awowi zai bushe shikenan ya zama ready sai a samu abubuwan zubawa ana zubawa.
Ana hada wannan kayan a kano da Kaduna da zaria gamasu bukata zasu iya Neman inda ake sayar da kayannan ta saya. Kudin hadin kuma ya danganta daga yawan da kike sonyi. 

Comments