Main menu

Pages

IRE - IREN ABINCI GUDA BIYAR DAKE HAIFAR DA WARIN JIKI, - BINCIKEN LIKITOCI

 



Ire - Iren abincin guda biyar da in aka yawaita cinsu suke kawo warin jiki (body odour) da yadda za a Magance shi.


Wani likitan asibitin Nasara Specialist Hospital dake Kaduna ya shawarci mutane kan irin abinci da ka iya kawo warin kashi idan aka cika cin su.




Ya kuma bayyana abincin kamar haka;

1. Yawan cin yaji, albasa da tafarnuwa na iya kawo warin kashi domin suna dauke da Sindarin da ake kira da ‘Sulfur’ wanda ke fita ta ramukan da zufa ke fita a jikin mutum wanda hakan ke kawo warin jiki da kashi.




2. Abincin marmari wato ‘Junk food’ a turance; likitan ya ce abinci kamar su alawar cakulet, gyada, biskit, da sauransu na kara kiba a jiki wanda sanadiyyar hakan kan iya kawo warin jiki da na kashi.

Likitan ya shawarci mutanen dake cin irin wannan abinci da su yawaita motsa jiki.




3. Cin abincin da basa dauke da sinadarin ‘Carbonhydrates’ na yawan sa mutun yin zufa wanda idan ba ana tsaftace jiki ba ne za ka ga ana dan wari wari.




4. Yawan cin kifi. Shima yana kawo Karni - Karnin jiki, duk ko da irin amfanin da kifin ke dashi a jikin mu.




5. Yawan cin naman sa na kawo warin jiki ko kashi saboda idan ya taru a jikin mutun ya kan hadu da ‘Bacteria wanda ke sa warin kashi.




Dr Ankama ya ce domin guje ma irin hakan za a iya cin wasu ganyayyakin da ake ci kamar su Lansuru da ‘ya’yan itatuwa kamarsu lemun zaki, lemun tsami, tufa da sauransu.




 Yanda za a Magance warin jiki (Body Odour)

Warin jiki ko body ordour wani abune da wasu mutane kanyi fama dashi har yakan zamo abun kunya ko abin damuwa, yakan farune galibi sakamakon wasu kwayoyin cuta dake hadewa da zufa (gumi) da mutun keyi.




 Akwai warin jiki nadan lokaci akwai na dindindin, Wanda ke faruwa na dan lokaci yakan farune saboda rashin wanka ko bayan anyi aikin karfi ko kuma zufa sosai Idan zufan ya hade da wasu kwayoyin cuta sai surinka bayarda wari na daban.




  Wanda ke faruwa na dindindin yakan dauki tsawon lokaci ana fama dashi domin yakan farune idan akayi sakaci da tsaftan yara tun lokacin Balaga kimanin shekaru 14 zuwa 16 ga mata, maza kuma kimanin 15 zuwa 17 Akwai wadanda ke samun warin jiki sakamakon kamuwa da wani cuta misali ciwon sugar ko ciwon daji.





  Yanda za a Magance shi, shine;

A zuba garin magarya cokali daya aruwan zafi da kafra guda daya da garin kanumfari a ruwan zafi sai atace arinka yin wanka dashi safe da yamma idan angama wankan sai ashafa turare sa'annan arinka kulawa da gashin hammata da na mara insha Allahu zai daina wallahu A'alam.

Allah Ya sa a dace Ameen.

Comments