Main menu

Pages

HANYOYIN DA ZAKI SARRAFA LEMUN TSAMI WAJEN GYARAN FUSKA.

 Hanyoyin da Zaki bi wajen sarrafa Lemon tsami wajen gyaran Fuska.

Lemon tsami na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan da jama’a suke amfani da shi wajen yin abubuwa da dama.


 Lemon tsami na da matukar muhimmanci ga dan Adam musamman ma wajen gyaran fuska, saboda haka, muka kawo muku yadda za ki yi amfani da shi domin gyaran fatar fuska. 
A gaba za mu kawo miki hanyoyin da za ki yi amfani da lemon tsami wajen gyara fatar fuska, sai dai muna so ki fahimci za ki iya amfani da hanya daya ce kawai daga cikin hanyoyin da za mu kawo miki, amma za ki iya amfani da sauran hanyoyin idan hanyar da kika dauka ta farko ba ta biya miki bukata ba.
- Lemon tsami da zuma; Ki debi rabin cokalin ruwan lemon tsami da kuma rabin cokalin zuma sai a kwaba su, daga nan ki shafa a fuskarki na tsawon minti 15, sannan ki wanke da ruwan sanyi. Idan kina da fata mai gautsi to za ki iya hadawa da man zaitun.
- Lemon tsami da nono;  Za ki hada rabin cokalin ruwan lemon tsami da rabin cokalin nono (amma an fi son kindirmo)sai ki kwaba sosai. Bayan haka, sai ki shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin ki wanke. A wannan hadin ba sai kin hada da wani mai ba, saboda nono na dauke da sinadarin mai.
- Timatir da lemon tsami da alkama; Ki matse ruwan timatir da na lemon tsami a wuri guda, sannan ki hada da nikakkiyar alkama, daga nan ki kwaba kafin ki shafa a fuska . Wannan hadin na taimaka wa masu yawan gumin fuska sosai. A shafa a fuska na tsawon minti 15 kafin a wanke.

Comments