Main menu

Pages

AMFANIN TSARKI DA RUWAN DUMI, DA YAWAITA SHAN ZUMA LOKACIN AL'ADAH
Amfanin yawaita yin Tsarki da ruwan dumi, da Kuma fa'idar Shan Zuma a duk lokacin da ake Al'adah da bayan gama ta.


Tsarki da ruwan dumi ba karamin taimakawa yake yi ba wajen gyaran (Farji )

Mata Ku kiyaye tsarki da ruwan sanyi saboda ba karamin illa yake yi ma mace ba.
Ana so mace ta dinga yin tsarki da ganyen magarya idan da so Samu ne ya zama shine permanent ruwan tsarkin ki shi ma ba karamin gyara ( farji ) yake yi ba.


       


Amfanin Shan Zuma lokacin Al'adah

Ana so mace ta ringa shan Zuma cokali daya (1) da safe daya (1) da daddare 1 wannan yana taimakawa wajen dawo miki da ni'iman ki da ya tafi yayin da kike jinin al'ada.
Ana so macen da take cikin jinin al'ada ta rinka shan zuma cokali uku (3) kullum da safe har tsawon kwanaki da zata gama al'ada.
Zaki sami man habbatussauda shima ki rinka sha kina shafawa a ( farji
Ki sani mafi yawa daga mazaje sun fi son zaman waje akan zaman cikin gida

wannan wani abune da ya samo asali daga ainihin gundarin halayyar da namiji don haka in dai ba wani aikin assha ne yake sa shi dadewa a waje ba to kiyi hakuri ki bi shi a hankali har Allah yasa ya daina.
Ki daina jin haushin mijinki saboda wannan dabi'a akan wannan dabi'a da yake da baki so matukar kina jin haushin abin kuma kina bayyanar masa da jin haushin to wannan ba zai sa ya daina ba sai dai ya kara ingiza shi ma ga alkatawa.

Comments