Main menu

Pages

AMFANIN LALLE DA RUWAN LALLEN WAJEN GYARAN JIKI DA GASHI

 



Amfanin Lalle da Kuma ruwansa shi lallen wajen gyaran jiki da gashi.


Jama’a da dama sun san cewa lalle abin ado ne ga mace. Bayan haka ruwan lallen ma na da matukar amfani ga fata. Ana shuka lalle ne a wuraren da ke  da zafi. Yanayin zafin wuri ke nuna kyan launin lalle. Don haka a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da lalle a fata.



  • Domin samun sulbin fuska, a jika lalle na tsawon awa biyu sannan a kwaba shi da ruwansa sai a diga man zaitun da kwanduwar kwai sannan a shafa a fuska na tsawon minti talatin sannan a wanke da ruwa. Ana son shafa irin wannan hadi kamar sau daya a mako.


  • A jika lalle da ruwa sannan a zuba man zaitun da man kwakwa a rika wanke gashin kai da shi domin hana gashi tsinkewa da kuma sanya gashi laushi,



  • Domin magance amosanin kai; a kwaba lalle da ruwan lemun tsami kadan sannan a shafa a fatar kai a bar shi na tsawon minti goma zuwa sha biyar kafin a wanke da sabulun wanke gashi.



  • Ruwan lalle shi ne babban abin da ke taya lalle kamawa a fatar hannu. Ana gane lalle mai kyau ne ta ganin irin launin ruwan da ke jikin lalle.


  • Shi kansa lalle abin ado ne ga mata idan aka sanya shi a tafin kafa ko a hannu.


  • Ana wanka da ruwan lalle bayan ya tsumu domin kara launi ga amaryar gobe. Za a iya jika ruwan da lalle mai dan dama ya tsumu bayan amaryar gobe ta gama wanka za ta iya watsa wannan ruwan a wankan karshe domin sanya fata laushi da launi mai kyau.


Comments