Main menu

Pages

ABUBUWAN DAKE HADDASA ZAFIN TAFIN HANNU KO KAFA.

 Abubuwan dake kawo matsalar Zafin tafin hannu ko na kafa.

Matsalar zafin tafin hannu ko kafa ba kasafai wannan yanayin ke zama alama ta matsala ba, akwai sauran dalilai wadanda zasu iya haifar Mana da wannan alamomin.
Bayan wannan an zakulo wasu dalilai 'yan kadan wadanda zasu iya kawo mana zafin tafin kafa ko hannaye ko duka lokaci daya.1 - Karancin sinadaran gina jiki, idan jiki baya samun wadatattun sinadaran Gina jiki wadanda jiki kanshi ke samarwa da Kuma wadanda muke Anfani dasu acikin kayan abinci Wanda muke Anfani dasu Yana Daya daga cikin alamomin dake haifar da wannan kamar sanadarin Vitamin D, Ascorbic Acid, Vitamin B2, Vitamin B12 da Sauran su.
2- Diabetes:- Matsala ko alamomin ciwon sugar Yana daga cikin abunda ke haifar da wannan ko Yana daga cikin alamomin farko farko na matsalar hauhawan Sugar jik.
3- Kidney failure:- Matsalolin Koda, Idan yacika samun wannan matsalar ya bibiyi aikin Kodar sa ta hanyar Awo da Kuma fahimtar sauran alamomin Koda a jiki, kada tinanin ya tsaya ga matsalar zafin tafin kafa ko hannu kadai. Kamar yanda mukai ta bayanin matsalolin Koda da alamomin ta a gidannan.
4- Anfani da magunguna na bature suna gaba gaba wajen haifar da wannan yanayin na zafin tafin kafa ko hannuwa.


5- Auto Immune Disease

6- Toxins

7- Infection

8- Alcoholism


Abin lura; Idan ana samun wannan yanayin ta hanyar bincike da tatsar sauran bayanai ke tabbatar da abunda ke haifar da wannan lalurar. Anfani da magani Kai tsaye bazai magance matsalar ba.

Comments