Main menu

Pages

AMFANIN KWAN SALWA GUDA 12 DAGA BINCIKEN MASANA

 Amfanin Kwan Salwa Guda Sha biyu (12) daga binciken Masana.

A yau za mu duba irin amfanin kwai ga lafiyarmu, musamman ma kwan salwa. Binciken masana ya tabbatar da cewa kwan salwa yana kunshe da abubuwan gina jiki fiye da kwan wasu tsintsayen. Misali yana kunshe da "protein" 13%, a inda kwan kaji ke da 11% .

Amfanin kwan salwa ga lafiya yana da yawan gaske daga cikin su akwai:
1. Bunkasa Garkuwar Jiki.

ALLAH (S.W.T) ya yi hikima wajen halttar dan-adam inda ya sanya masa garkuwar jiki da ke da alhakin kare shi daga kamuwa da cututtuka, idan kuma har ya kamu din ita dai wannan garkuwa ke yakar kwayoyin cutar har dan-adam ya samu lafiya. Ashe samun garkuwa mai karfi na da kyau wajen samun koshin lafiya.Kwan salwa yayi fice a wannan fagen don kuwa yawan cinsa na kara bunkasa garkuwar dan-adam. Wani sinadari na "lysine" da ALLAH YA abarkaci kwan da shi ke taimakawa wajen karfafa garkuwarmu.
2. Ginawa Da Samar Da Lafiyayyan Jiki.

Ba sai an fada ba, kowanne kwai na kunshe da sinadaran gina jiki bare kuma shi kwan salwa. Kamar yadda aka fada tun da farko yai mu su zarra a yawan wadannan sanadirai, idan haka ne kuwa ba makawa ya fi su saurin gina jiki.Saboda sinadiran gina jiki da ya ke kunshe da su ya ke taka muhimmiyar rawa wajen yin garabawul ga dukkan jiki da ya hada da kashi. hanyoyin jini tsoka d.s. Don haka yawan cin sa kan gina jiki da sauri.
3. Kaifin Basira.

Yana da wasu sinadirai da keda alaka da bunkasa lafiyar kwakwalwa wanda hakan ke bayuwa ga samun karin kaifin basira. Yana kuma bada kariya ga kwakwalwa daga samun wani lahani.To dalibai da sauran masu kwadayin ilmi sai a dimananci cin kwan salwa don samun karin karfin basira.
4. Kara Karfi Gani.

Yana kunshe da sanadarin "vitamin A" da sauran sanadirai da ke kara lafiyar ido sannnan ya kara karfin gani ga dan-adam. Haka nan yana yiwa ido riga kafin kamuwa daga wasu cutukan idon musamman idan shekaru suka fara ja.
5. Karin Kuzari.

Yawan cin kwan salwa na kara kuzari. Ta yiwu saboda sanin haka ne yasa wasu ke hada shi a abincinsu na safe don su fita wajen harkokinsu cikin kuzari da walwala.
6. Taimakawa Masu Hawan Jini.

Binciken masana ya tabbatar da cewa yawan cin kwan salwa na taimakawa masu fama da hawan jini saboda yana kunshe da sanadarin "potassium". Bayan haka yana da wasu sanadiran da ke aikin a fagen gudanar jini a jikin dan adam.
7. Gyaran Fata.

Mun ambata tun da farko cewa shi wannan kwai yana kunshe da abubuwa masu gina jiki da suka hada da "vitamins", "minerals. d.s, wanda hakan ya sa yawan cin sa ke samar da lafiyayyar fata da ban sha'awa.Bugu da kari saboda wadannan sinadirai, yawan cin sa kan baiwa fata kariya daga kamuwa daga wasu cutukan fata har da cutar daji da ke shafar fata.
8. Lafiyar Zuciya.

Yana daidaita kwalastaral na cikin jini. ta wajen rage mai lahani ga dan-adam ya kuma kara yawan mai amfani a jiki. Yin hakan ba karamin tasiri ya ke ba ga lafiyar zuciyarmu.
9. Taimakawa Masu Ciwon Siga.

Yawan cin sa na taimakawa masu ciwon siga matuka da gaske. Kamar yadda bayani ya gabata a sama cewa yana daidaita kwalastaral na cikin jini to lalle wannan zai taimakawa mai fama da ciwon siga. Haka nan zai zama rika kafi ga wanda bai kamu da ciwon ba.
10. Inganta Lafiyar Hakori.

Saboda kasancewar sa mai kunshe da sanadarin "zinc" mai yawa ya ke kara karfin hakori ya sa shi ya kasance mai lafiya.
11. Saurin Murmurewa Daga Rashin Lafiya.

Saboda kasancewar sa ya na kunshe da tarin sinadarai masu gina jiki, ake amfani da shi ga wadanda su ke murmurewa daga wata rashin lafiya kuma ana samun tasiri sosai.
12. Karfin Kashi.

Akwai wani sinadari da ake kira "amino acid" wanda kwan salwa ya ke da shi. Wannan sinadari na da matukar amfanin wajen ginawa da kuma karfin kashi musamman ga yara.
13. Karin Jini.

Kasancewar sa yana kunshe da sanadarin "iron" ya sa shi mai taimakawa wajen karin jini a jikin dan Allah yabamu ikon amfani da wannan kwai mai Albarka.

Comments