Main menu

Pages

ABUBUWAN DAKE KAWO KURAJEN FUSKA DA YADDA ZA A MAGANCE SU

 



Abubuwan dake kawo kurajen fuska da yadda za a Magance su.

Kurajen fuska na pimples matsala ce da ta'addabi matasa Mata da Maza musamman masu kananan shekaru wadan da suka fara balaga saboda samun canji daga sinadaran hormones. 




Duk da kurajen fuska tana Kama Mata da maza, Amma Mata sunfi damuwa saboda za kaga har nikab suke sanyawa a fuskokin su saboda kar aga ta’adin da kurajen suka yi musu a fuska.




Kurajen pimples ba a fuska kadai take fita ba suna fita a wadannan wuraren:


- Kirji 

- gadon baya

- Cinya

- wuya 



Abubuwan da suke taimakawa wajen tunzura kurajen fuska:

-  Yawan cin Abu Mai maiko.

- Amfani da mayukan da Basu dace da fatar jiki ba

- Kwayoyin cuta

- Shiga rana sosai

-  Shan wasu magunguna


Abinda ya kamata ayi domin kariyar yawaitar kurajen fuska da samun waraka sune:

1- A rage amfani da abinci masu maiko diyawa.


2- Idan kuraje suka fito kada a yawaita tabawa.


3- Idan zakai dogon waya kada ka daura wayar a fuskar ka kusada kurajen.


4- A samu ruwan dumi a matsa lemon tsami a wanke fuska da shi a kalla so biyu a rana.


5- Idan kurajen a kirji ko baya kada ayi amfani da matsattsen kaya saboda samun iska.


6- Za'a iya shafa zuma bayan dan mintuna a wanke da ruwan dumi.


 Idan wadannan hanyoyin basuyi amfani ba a tuntubi ma'aikacin lafiya domin akwai magunguna da dama masu kashe kurajen pimples.

Comments