Main menu

Pages

ABUBUWAN DA YA KAMATA MACE TA KAURACEWA DON LAFIYAR GABANTA

 


Abubuwan da ya kamata Mata su kauracewa in har suna son kasancewa da gabansu Lafiya har tsufa.


Akwai wasu abubuwa da yawancin mata suke yiwa gabansu da yake musu illa ba tare da sun fahimci hakan ba.


Mata su kula da yin wadannan abubuwan mudin suna son su tsufa suna morar halittarsu.


 

1: Duk mace nason ganin gabanta cikin tsafta. Da kuma duk wani datti da zai janyo ma wajen samun matsala har takai ga yin wari.


Hakan yasa wasu matan suke amfani da sabulun dake sauya launin fata wajen wanke gabansu da shi. Daga bisani kuma su fesawa gabansu turare ko kuma hoda.

Duk macen datake yiwa gabanta hakan, ta sani zata rika jawowa kanta cuta a kullum.

Hakan kuma zai yiwa gabanta illa inji masana al'uran mata.
Kada ki wanke gabanki da duk wani sabulun da kikasan yanada sinadari mai karfi a jikinsa. Akwai sabulu na musamman da ake sayarwa na wanke gaba na mata.


 Idan kuma baki da halin saye, sabulai marasa sinadari masu karfi zasu iya tsaftace gaban mace ba tare da cutar da kanta ba.


Gaban mace baya bukatar a masa feshin turare ko hoda, domin wadannan abubuwan suna kunshe ne da sinadarin da zai yiwa mace illa a gabanta maimakon ya sata kamshi kamar yadda take bukata.
 Don haka ki guji fesa turare ko hoda a gabanki domin samawa gabanki kamshi.

 Maimakon hakan kina iya amfani da man zaitun domin shafawa a shatin gabanki ba a cikin gabanki ba. Domin cikin gabanki wannan ruwan shike tsaftace shi ya kuma kare duk wata cuta samun zama a ciki.
2: Jimawa Da Jikenken Pant: Wasu matan sukan jima da wandon da sukayi aiki suka yi gumi har gabansu ya jike. Ko kuma suka yi motsa jikin da suka jika gabansu.


Yana da kyau da zaran mace taji wandon dake jikinta ya jike saboda gumi, ko jikewa da ruwa, tayi maza ta cire Wandon domin zama da irin wannan kayan a jikin mace yakansa ta harbu da infection cikin sauki.
3: Yawan Shan Zaki: Mata da dama basusan zaki Yana da illa ga Al'auran su ba. Don haka ki rage yawan shan zaki.


Comments