Main menu

Pages

YANDA ZAKI RAGE MUGUWAR QIBA DA TUMBI DA ZOGALE DA GAMJI

 Yanda zaki rage muguwar Qiba da Tumbi da Ganyen Zogale da Gamji cikin sauki ki koma Yar dai dai

A wani ɓangare kuma, idan mace na da buƙatar rage ƙiba, to abu mafi sauƙi da ya kamata ta yi a taƙaice shi ne kamar haka:


Abu na farko da za ta nema shi ne zogale, bayan an gyara an wanke shi, sai a markaɗa, sannan a tace ruwan, kana a riƙa sha safe da kuma dare, ma’ana kullum sau biyu a rana.

Sai dai kar a manta binciken ya bayyana cewa, akwai yiwuwar sanya gudawa, saboda an hau turbar rage ƙiba ne.


Muddin aka yi amfani da wannan dabara kamar yadda aka bayyana, to mace za ta rage ƙiba sosai da sosai.

Sannan kuma ga wacce take da tumbi, sannan ta ke son rage shi, to sai ta sami sassaƙen Gamji ta haɗa da ‘yar jar kanwa, sannan a tafasa a riƙa sha, in Allah Ya yarda za a neme shi a rasa Insha Allah.

Comments