Lokutta guda biyar da ya kamata ka kiyaye Shan ruwa a dai dai lokacin, don samun inganta Lafiyar jiki.
1. Gab da kafin kaci abinci karka sha ruwa.
2. Bayan Gama cin abinci karka sha ruwa nan take sai bayan kamar minti 15, sannan duk kasalar da zakaji karka kwanta irin wannan lokacin
3. In zakai ibadar aure gab da yi karka sha ruwa, bayan gamawa kada kasha ruwa nan da nan, sai bayan mintoci kusan 15 zuwa 20
4. Kar kuma ka auka bandaki da niyyar Wankan tsarki bayan Gama ibadar nan da nan, a'a kadan jira tukun
5. Gab da zaka shiga bandaki Wanka ko fitsari nan ma karka sha ruwa, Bayan ka fito nan ma karka sha ruwa nan da nan.
Insha Allahu in aka kiyaye wannan za'ai lafiyar jiki kwarai da gaske.
Kuma koda kana fuskantar matsalar nan ta riƙa jin bayan kagama fitsari ka miƙe wani ɗan kaɗan na fitsarin na zubowa ya ɓata maka wando, ko wasiwasi haka kurum bama fitsarin kai ba amma ka riƙajin kamar wani ya fito ta gabanka, ko ya zamto ka riƙa jin kamar maziyi ya fito ma alhalin inka duba zakaga bakomi.
Toh inde ka kiyaye wadancan tips din insha Allahu zaka dena walau Mace ko Namiji.
Comments
Post a Comment