Main menu

Pages

YADDA ZA AYI HADIN NONON RAKUMI DA DABINO KWAKWA DSS




Yadda za ayi hadin Nonon Rakumi don samun Ni'ima ga Mata da Maza da magance wasu matsalolin.

Wannan hadin yana taimakawa ga mata gaya dangane da zamantakewar aure, musamman kara ni'ima da sauran su. 


(1) Zaki samu wadannan abubuwa kamar hak :

Nonon rakumi Mara hadi ko kadan. 

(2) Aya 

(3) Gero. 

(4) Kwakwa. 

(5)Zaki samo Dabino bushashshe. 




Hanyar da za a hada za a nika aya, gero, Dabino, da wannan kwakwa, amma ayar kafin anika ana bukatar asoya ta kadan, idan akayi garin wadannan Magungunan Sai a hada waje daya. 




Sai akawo wannan Nonon rakumi azuba kadan ana gaurayawa har yahade sosai ta yadda kada acika daga nan ana bukatar  busar dashi. 


Bayan yabushe za a Kara nikawa ko adaka Sai adinga shansa da madara ko aruwan shayi insha Allah wannan zai taimaka sosai wajen bada ni'ima da kuma magani. 




Dangane da maza kuma zaka iya samun no-non rakumi mai kyau, mara hadi da fitsarin sa, da kuma Zuma. Sai kahada no-non dan kadan da fitsarin kadan da Zuma ka gauraya kashanye. Ko kuma kahada da Zuma da fitsarin rakumi kadan, da no-non sa kadan sai kazuba gishiri kadan ka gauraya kasha wannan yana taimakawa sosai ga mazaje wajen bada kuzari. 



Amma idan kasamo marasa kyau to baza a samu wannan faidaba, dafatan za a kiyaye. 


Bayan haka Kamar yadda ake yawan tambaya akan matsalolin da suka shafi maza maganar karfi, da Kara kuzari, zaka iya samun garin kuka Mara hadi, kahada da Kanin fari, ko kayan yaji kanike kadinga sha da ruwa hakanan, ko ruwan shayi wannan Shima yana taimakawa sosai. 




Bayan haka masu matsala na Ciwan sikla musamman alokacin sanyi matsalar tana yawan tashi, to Kamar yadda wasu suka jarraba idan aka samu no-non rakumi, da kuma fitsarin sa wadanda basuda hadi akayi amfani dashi, Kamar marfi magani za arika sha sau uku arana, no-non Kamar Karamin kofin yara sau daya arana, bayan haka za ayi ma yaron wanka sannan a shafa masa fitsarin rakumi ayi Kamar haka na sati uku idan Allah swt. Yasa anyi bisa dace za a iya samun waraka.


Dafatan Allah taala yabamu dacewa Allahumma Ameen. 


Comments