Main menu

Pages

YADDA AKEYIN KOSAN DOYA DA KWAI CIKIN SAUKI
Yadda za ake hada Kosan doya

- Doya 

- Kwai

- Tarugu

- Albasa

- Maggi

- Spices

- Curry

- Man tuyaZa a dafa doya da gishiri sai tayi laushi sosai sai a dake ta sannan a zuba a roba asa Maggi, spices, tarugu, albasa da curry sai afasa Kwai, acikin ta asa Mai kadan acakuda su sosai ki daura aleda kamar yadda ake alala.
Amma daurin gefe sai adafa idan an dafa sai a sauke ya Sha iska abare aleda ya huce sai a yanka kamar awara a tsoma acikin hadin ruwan kwai sai a soya kamar yadda ake doya haka har agama shikenan.

Abin lura: Ana iya soyawa ahaka ba sai da kwai ba duk Yana yin kyau da dadi ko aci shi da miyar sauce ba sai an soya ba.

Comments